Gwamnan Jihar Neja, Hon. Umar Mohammed Bago ya shawarci matasan jihar da su rungumi sana’ar noma domin magance matsalar yunwa, kuma gwamnatinsa ta shirya mayar da hankali kan noma wajen samar da abinci da magance matsalolin yunwa a jihar.
Gwamnan yayi kiran ne a lokacin kaddamar ba da tallafi ga manoma dubu daya da dari biyu da hamsin da suka fito daga kananan hukumomi ashirin da biyar na jihar, bisa tallafin hukumar ACReSAL da hadin guiwar bankin duniya.
Tun da farko a bayaninsa, kodinetan ACReSAL na kasa, Abdulhamid Umar, ya ce bankin duniya ta ware dala miliyan dari bakwai da tamanin da shida domin karfafa harkar noma a arewacin kasar nan.
Ya ci gaba da cewa shirin zai rabar da kayyakin noma da suka hada da takin zamani, iri, magunguna, kananan motocin noma da manoma ke bukata, wanda ya sa aka zabo manoman da ke cikin kungiyoyin manoma domin fara kaddamar da shirin a Jihar Neja.
Shi kuwa kodinetan ACReSAL a Jihar Neja, Alhaji Usman Garba Ibeto ya ce duk da matsalar zaizayar kasa da ake fama da shi a jihar, hukumar ta yi shirin fuskantarsa kamar yadda aka yi a baya.
“Muna jawo hankalin manoma kar su yarda su sayar da kayayyakin da muka bayar, kuma za mu ci gaba da rabar da sauran kayayyaki da aka samar domin anfani manoma.”