Babu wani dan takarar shugaban kasa da zai iya lashe zaben 2023 ba tare da goyon bayan matasa ba, in ji dan takarar jam’iyyar PDP a mazabar tarayya ta Ekiti ta Kudu 1, Henrich Akomolafe.
Ya kuma jaddada cewa matasa su ne kawai za su iya kawo sauyi a kasar nan.
Akomolafe, mai shekaru 29, ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi cewa idan ba matasa, zaben 2023 ba zai yiwu ba.
Don haka ya yi kira ga kowane dan takarar shugaban kasa da ya tafi da matasa tare da tabbatar da sahihin zabe na gaskiya.
A cewarsa, ’yan siyasa sun yi tunani da bincike sun gane cewa, a zabe mai zuwa, babu wani ubangida da zai cece su sai dai hada kai da matasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp