Matasa a Lafiagi, ƙaramar hukumar Edu a Jihar Kwara, sun gudanar da zanga-zanga a yau Litinin kan yawaitar sace mutane da hare-haren ‘yan bindiga, inda suka ƙona ofishin hukumar NDLEA tare da kutsawa fadar Sarkin Lafiagi, suna faffasa tagogi da wasu sassa na ginin.
Wani mazaunin yankin ya ce mutane sun gaji da zaman tsoro da rashin kulawar gwamnati, yana mai cewa, “Ana sace mutane kowane mako, ba ma kwana da kwanciyar hankali. Gwamna, shugaban ƙaramar hukuma ko Sarki ba su ɗaukar wani mataki.”
- An Horas Da Kwararrun Ma’aikata Sama Da Dubu 500 Karkashin Hadin Gwiwar Sin Da Sassan Kasa Da Kasa A Fannin Inganta Kwarewar Ma’aikata
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Ɗan Kasuwa da Ɗan Banga A Kwara
Zanga-zangar ta biyo bayan sace mutane uku a cikin awa 12 – wani mai POS da aka fi sani da Yman da aka ɗauka da daddare, da wasu maza biyu daga ƙauyen Kokodo da aka sace da safe. Wata yarinya ta tsira da ranta bayan ta tsere zuwa daji.
Haka kuma, an sace wani fitaccen dillalin kayan noma, Alhaji Chemical, daga gidansa da misalin ƙarfe 1 na dare. Shaidu sun ce ‘yan bindigar sun shigo da babura tare da makamai suka sha gaban masu aikin sa kai sannan suka tsere da wanda suka dauka.
Jami’an tsaro sun shiga yankin domin dawo da doka da oda, amma zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wani bayani daga gwamnatin jihar Kwara ko fadar Sarki kan abin da ya faru ko kuma halin da waɗanda aka sace ke ciki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp