• English
  • Business News
Wednesday, September 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Matasa Sun Samu Horo Kan Shirin e-Naira Karkashin Bizi Mobile A Jihar Borno

by Leadership Hausa
3 years ago
in Labarai
0
Matasa Sun Samu Horo Kan Shirin e-Naira Karkashin Bizi Mobile A Jihar Borno
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A ci gaba da samar wa da Matasan Jihar Borno ayyukan yi, Gwamnatin Jihar Borno karkashin jagorancin Farfesa Babagana Zulum, da hadin gwiwar kamfanin hada-hadar kudi irin na zama ni, wato Bizi Mobile Cashless Consultant limited, da kamfanin Kama Integrated Serbices limited da kuma BRMFB, sun kara horar da Matasan Yankin Jihar Borno ta Arewa da ta Yamma kimanin 200 game da harkar ‘Agency Banking’ da kuma ba su horo na musamman a kan shirin Babban bankin kasa (CBN) na harkar e-Naira.

Taron horarwar na musamman wanda aka shirya shi na yini biyu, ya gudana ne a karamar hukumar Biu da ke Jihar Borno.

  • Kada Wata Jam’iyya Ta Kuskura Ta Karɓi Tallafin Kuɗi Daga Ƙasashen Waje – INEC
  • Shekara 62 Da Samun ‘Yancin Kai: Na Damu Da Halin Da ‘Yan Nijeriya Ke Ciki – Buhari

Taron horarwar wanda ya sami halartar wakilin Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, wanda kwamishan Matasa da samar da ayyukan yi na Jihar borno, Honarabul Sa Inna Buba ya walkita.

Sauran Manyan bakin sun hada da, Wakiliyar Shugaban karamar hukumar Biu, wanda Sakatariyar karamar hukumar Biu, Hajiya Larai Magira ta wakilta, sai kuma Mataimakiya na musamman akan samar wa da Matasa ayyukan yi na Gwamnan Borno Hajiya Aisha, da kuma Shugaban masu harkar POS na karamar hukumar Biu, Gwani Makeri, Daraktan kamfanin Bizi Mobile, Dakta Aminu Bizi, Shugaban Kama Integrated Serbices limited, Kalli Zanna Gambo, da kuma Shugaban bankin FMB Farfesa Bello Alhaji Ibrahim.

A yayin da yake nasa jawabin a madadin Gwamnatin Jihar borno, Kwamishinan Matasa da Samar da ayyukan yi, Honarabul Sa Inna Buba, ya bayyana cewa, Gwamnatin Jihar Borno karkashin jagorancin hazikin gwamna, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayar da umurnin a dauki matasa har 200 wadanda suka fito daga kananan hukumomin Borno ta Arewa da kuma Borno ta Yamma, domin a horar da su akan abin da ya shafi harkar POS, Agency banking da kuma shirin Babban bankin kasa CBN na e-Naira.

Labarai Masu Nasaba

An Yi Garkuwa Da Wani Mai Hidimar Ƙasa Da Ɗalibi A Jos

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Hutun Sati 2 A Ƙasar Faransa

Kwamishinan Matasa da Samar da ayyukan yi Honarabul Sa Inna Buba, ya kara da bayyana cewa, tun da a halin yanzu harkar tsaro ya inga a Jihar Borno, Gwamnatin Jihar Borno ba za ta yi kasa a gwiwa ba, wajen ganin ta ci gaba da samar da dinbin matasan jihar ayyukan yi wanda zasu dogara da kansu.ya jinjina ma kamfanin Bizi Mobile, bankin Micro, da kamfanin Kama Integrated serbices limited a bisa namijin kokarinsu na ganin sun ci gaba da hada gwiwa da Gwamnatin Jihar Borno karkashin jagorancin Farfesa Babagana Umara Zulum domin ci gaba da inganta rayuwa Matasan Jihar Borno baki daya.

A yayin da yake nasa jawabin, Shugaban karamar hukumar Biu, wanda Sakatariyar karamar hukumar ta wakilta, Hajiya Larai Magira, ta gode wa Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum a bisa yadda ya jajirce wajen ganin ba’a bar matasan Jihar Borno a baya ba.

A cewar ta, Gwamnatin Jihar Borno karkashin jagorancin Farfesa Babagana Umara Zulum ya fi kowannn Gwamnan da ke kasar nan son inganta rayuwar matasa da samar masu da ayyukan yi.

Hajiya Larai Magira, ta ja hankalin matasan karamar hukumar Biu da su kasance jakadu na gari a lokacin da suke daukar horarwar da kuma bayan taron. Ta ce, ya zama wajibi ga Matasan da su rungumi wannan sana’ar da suka koya domin ganin sun zama abin alfahari a cikin al’umma, saboda lokacin dogaro jira aiki daga gwamnati ya wuce.

Sannan tayi kira ga dalibai da a halin yanzu suke zaune a gida a dalilin yajin aikin da Malaman jami’a ke gudanawar a halin yanzu. Da cewa, ga dama ta samu a gare su domin ganin sun rungumi wannan shiri na e-Naira Babban bankin kasa CBN ya zo masu da shi, domin ganin sun mayar da shi babban sana’ar da zasu ci gaba da dogaro da shi a yayin da suke zaune a gida da kuma bayan sun koma karatu.

Domin a cewar ta, zaman gida babu karatu ko aiki na iya jefa rayuwar su a cikin hatsarin gaske.

Shima a nasa jawabin a wajen taron horarwar, Shugaban Rukunonin Kamfanin Bizi Mobile Cashless Consultant limited, Dakta Aminu Bizi ya jinjina ma Gwamnatin Jihar Borno karkashin jagorancin Farfesa Babagana Umara Zulum a bisa Namijin kokarinsa ta yadda yake inganta rayuwar matasan Jihar Borno.

A cewar Dakta Aminu Bizi, ya zama wajibi a yaba ma Gwamnatin Jihar Borno, kuma a shirye kamfanin sa yake ya ci gaba da hada gwiwa da Gwamnatin Jihar Borno domin ci gaba da samarwa Matasan Jihar Borno da dinbin ayyukan yi.

Dakta Aminu Bizi ya kara da bayyana cewa, saboda hazakar da kamfanin Bizi Mobile ke da shi, Babban bankin kasa na (CBN) ya bai wa kamfaninsa ragamar horar da matasa akan duk wani abu da ya shafi harkar Agency Banking, shirin e-Naira da dai sauran abin da ya shafi hada hadar kudi irin na zamani.

Dakta Aminu Bizi ya bayyana cewa, a karkashin shirin e-Naira na Babban bankin kasa (CBN) a halin yanzu kamfaninsa ya horar da kuma samarwa da Matasa sama dubu 100,000 ayyukan yi a fadin kasar nan baki daya. Kuma a cewarsa, kamin nan da karshen wannan shakerar, kamfaninsa na Bizi Mobile zai horar da kuma samarwa da sama da matasan kasar 200,000 ayyukan yi akan abin da ya shafi Agency banking da kuma shirin e-Naira.

A yayin da suke zantawa da wakilinmu, matasan sun nuna godiyarsu ga Gwamnatin Jihar borno, da karamar hukumar Biu, da duk wadanda suka shirya taro horarwar akan yadda zasu dogara da kansu.

Matasan, sun nuna dinbin godiyar su ga Gwamnatin Jihar Borno karkashin jagorancin Farfesa Babagana Umara Zulum a bisa yadda ya basu dama domin ganin sun sami aikin da zasu dogara da kansu, saboda a cewar matasan, da dama daga cikin su, sun jima da kammala karatun digiri amma babu aikin yi a gare su.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: BiuBizi MoneyBornoe-MoneyHoroMatasaPOS
ShareTweetSendShare
Previous Post

Aihinin Abin Da Ke Hana Mata Zaman Aure

Next Post

Ya Kamata A Koyi Fasahohin Raya Demokuradiyya Na Sin

Related

Sauye-sauyen Manufofin Gwamnati Na Iya Hana Masu HND Zuwa NYSC
Labarai

An Yi Garkuwa Da Wani Mai Hidimar Ƙasa Da Ɗalibi A Jos

6 hours ago
Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Hutun Sati 2 A Ƙasar Faransa
Labarai

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Hutun Sati 2 A Ƙasar Faransa

7 hours ago
Sojoji
Labarai

Sojoji Sun Harbe Wasu ‘Yan Ta’adda 2 A Taraba

8 hours ago
Buhari Ya Taya Amusan Murnar Lashe Zinari A Gasar Tsere Ta Duniya
Labarai

Tinubu Ya Taya Amusan Da Gumel Murnar Samun Nasarori A Ɓangarori Daban-daban

9 hours ago
NSCDC Za Ta Fara Sanyan Ido Kan Muhimman Abubuwan More Rayuwa A Jihar Kano
Manyan Labarai

NSCDC Za Ta Fara Sanyan Ido Kan Muhimman Abubuwan More Rayuwa A Jihar Kano

11 hours ago
Shawarar Inganta Jagorancin Duniya Ta Haifar Da Damar Wanzar Da Daidaito Da Adalci
Ra'ayi Riga

Shawarar Inganta Jagorancin Duniya Ta Haifar Da Damar Wanzar Da Daidaito Da Adalci

12 hours ago
Next Post
Ya Kamata A Koyi Fasahohin Raya Demokuradiyya Na Sin

Ya Kamata A Koyi Fasahohin Raya Demokuradiyya Na Sin

LABARAI MASU NASABA

Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo

Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo

September 16, 2025
Shawarwarin Sin: Ingantattun Hanyoyi Masu Sauki Na Warware Sabani

Shawarwarin Sin: Ingantattun Hanyoyi Masu Sauki Na Warware Sabani

September 16, 2025
Sauye-sauyen Manufofin Gwamnati Na Iya Hana Masu HND Zuwa NYSC

An Yi Garkuwa Da Wani Mai Hidimar Ƙasa Da Ɗalibi A Jos

September 16, 2025
Sin Da Amurka Sun Yi Tattaunawar Keke-da-keke Kan Batutuwan Cinikayya Da Manhajar TikTok

Sin Da Amurka Sun Yi Tattaunawar Keke-da-keke Kan Batutuwan Cinikayya Da Manhajar TikTok

September 16, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Hutun Sati 2 A Ƙasar Faransa

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Hutun Sati 2 A Ƙasar Faransa

September 16, 2025
Sin Da Ghana Na Fadada Hadin Gwiwa A Bangaren Ciniki Da Zuba Jari

Sin Da Ghana Na Fadada Hadin Gwiwa A Bangaren Ciniki Da Zuba Jari

September 16, 2025
Sojoji

Sojoji Sun Harbe Wasu ‘Yan Ta’adda 2 A Taraba

September 16, 2025
Yawan Hatsin Da Aka Girbe A Kasar Sin Tsakanin Shekarar 2021-2025 Ya Kai Wani Sabon Matsayi

Yawan Hatsin Da Aka Girbe A Kasar Sin Tsakanin Shekarar 2021-2025 Ya Kai Wani Sabon Matsayi

September 16, 2025
Buhari Ya Taya Amusan Murnar Lashe Zinari A Gasar Tsere Ta Duniya

Tinubu Ya Taya Amusan Da Gumel Murnar Samun Nasarori A Ɓangarori Daban-daban

September 16, 2025
Sin Ta Daga Zuwa Mataki Na 10 A Jadawalin GII Na Kasashen Dake Kan Gaba A Fannin Kirkire-Kirkire

Sin Ta Daga Zuwa Mataki Na 10 A Jadawalin GII Na Kasashen Dake Kan Gaba A Fannin Kirkire-Kirkire

September 16, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.