Babban taron wakilan jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 20 da aka kammala, ya gabatar da shawarar farfado da al’ummar Sinawa ta hanyar zamanantar da kasar Sin bisa salonta, matasan da aka yi zanta da su a sassa daban-daban na duniya, sun amince da tsarin zamanantar da kasar Sin.
Wani binciken jin ra’ayoyin matasa ‘yan kasa da shekaru 30 da haihuwa guda 4700 daga kasashe 30 da aka yi, ya nuna cewa, kashi 84.7 cikin dari na wadanda aka zanta da su, sun amince da hanyar raya kasa ya dogara ne da yanayin kasashensu, suna kuma ganin cewa, bai kamata a zamanintar da kasa ta hanya iri daya ba.
Fiye da kashi 80 cikin dari na matasan da aka zanta da su, sun amince da tunanin samun bunkasuwa na kasar Sin bisa tushen jama’a da JKS ta gabatar.
Kungiyar masana ta kafar CGTN da jami’ar Renmin ta kasar Sin ne suka gudanar da binciken jin ra’ayoyin matasan duniya cikin hadin gwiwa, bisa taken “Sin ta kama sabon tafarki”, inda matasa a sassan duniya suka nuna yabo ga nasarorin da Sin ta samu a cikin shekaru 10 da suka wuce.
Daga cikinsu, kashi 78.9 cikin dari sun yabawa nasarorin da Sin ta samu a fannin tattalin arziki, kana kashi 83.1 cikin dari suna ganin cewa, Sin ta samu babban ci gaba a fannin kimiyya da fasaha. Kashi 84.2 cikin dari na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu daga kasashe masu tasowa da kashi 79.5 cikin dari na kasashe masu ci gaba sun amince da tunanin Sin na raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’Adama. (Zainab)