Wani matashi da ba a san kowane ne ba ya cinna wa wani masallaci wuta, yayin da jama’a suke tsaka da gudanar da sallar Asuba a garin Laraba Abasawa da ke Karamar Hukumar Gezawa a Kano.
Lamarin dai ya faru ne yayin da mutane ke yin sallar Asuba, wanda ya yi sanadin jikkatar masallata da dama.
- ‘Yan Ta’adda 23 Sun Mutu A Rikicin ‘Yan Bindiga A Zamfara
- Hukumar NSCDC Ta Kama Wasu Mutane 9 Da Ake Zargi Da Aikata Fashi A Kano
A cewar rahotanni daga yankin, matashin da ba a san kowane ne ba, ya yi amfani da fetur wajen banka wa masallacin wuta.
Wani ganau, ya shaida cewar matashin ya kulle masallacin ta waje yayin da jama’a ke sallah sannan ya kunna wutar, lamarin da ya jefa masallatan cikin tsaka mai wuya.
Wani ganau ya shaida wa Daily Trust cewa “Ya dauki tsawon lokaci kafin mutanen da ke wajen masallacin su fuskanci abin da ke faruwa su kai wa mutanen dauki.”
Akalla mutane 20 ne zuwa yanzu suka samu munanan raunuka, inda hukumomi suka garzaya da su Asibitin Koyarwa na Murtala Muhammad, domin ba su agajin gaggawa.
Rundunar ‘yansandan Jihar Kano, har yanzu ba ta ce komai kan faruwar lamarin ba.