Rundunar ‘Yansandan Jihar Kano ta kama wani matashi mai shekaru 30, mai suna Mutawakilu Ibrahim, bisa zargin caka wa kakanninsa wuƙa har sai da suka mutu bayan rigima a kan abinci.
Waɗanda abin ya rutsa da su su ne Muhammad Dansokoto mai shekaru 75 da Hadiza Tasidi mai shekaru 65, inda lamarin ya faru a gidansu dake unguwar Kofar Dawanau, da misalin ƙarfe 9:30 na safiyar ranar Alhamis, 25 ga watan Satumba, 2025.
- Salon Zamanantarwa Irin Na Kasar Sin: Hanya Ce Mallakar Kasar Sin Wacce Kuma Ta Sada Duniya
- Gwamnatin Katsina Ta Bankaɗo Ma’aikatan Bogi 3,488
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Kiyawa, ya bayyana cewa Ibrahim ya caka musu wuƙa a wurare da dama na jikinsu, lamarin da ya janyo musu mummunan rauni.
An garzaya da su asibitin Kwararru na Murtala Muhammad, inda aka tabbatar da mutuwarsu.
Daga baya an miƙa gawarwakin ga ‘yan uwansu domin yi musu sutura.
‘Yansanda sun ce wanda ake zargin yana cikin maye lokacin da ya aikata laifin.
An miƙa lamarin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka domin ci gaba da bincike, kuma za a gurfanar da shi a kotu nan ba da jimawa ba.