Alamu masu ƙarfi a safiyar yau Laraba na nuna cewa kungiyar manyan ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Nijeriya (PENGASSAN) na iya dakatar da yajin aikin da take yi biyo bayan sulhu da gwamnatin tarayya ta kulla da mahukuntan matatar man Dangote.
Bayan doguwar tattaunawa a taron sasantawa da aka gudanar a Abuja a ranakun 29 da 30 ga watan Satumban 2025, bangarorin biyu sun amince da kuduri mai dauke da abubuwa biyar.
- Gwamnatin Gombe Ta Haramta Kiwon Dare, Ta Taƙaita Zirga-zirgar Makiyaya Kafin Fara Girbi A Jihar
- Sin Ta Ciri Tuta A Fannin Kimiyya Da Fasaha
Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Mohammed Maigari Dingyadi, a wata sanarwa bayan taron, ya tabbatar da cewa, shiga kungiya, haƙƙi ne na ma’aikata bisa ƙa’ida a ƙarƙashin dokokin mulkin Nijeriya, wanda dole ne a kiyaye.
An kuma amince da cewa ma’aikatan da aka kora za a mayar da su kan ayyukan su cikin wasu kamfanoni na rukunin Dangote ba tare da sun yi asarar albashi ba, kuma babu wani ma’aikaci da za a ci zarafinsa saboda rawar da ya taka a wannan taƙaddamar.
An cimma matsayar ne a gaban manyan jami’an gwamnati da suka hada da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, ministan kudi kuma mai kula da tattalin arziki, ministan kasafin kudi da tsare-tsare, karamin ministan albarkatun man fetur (Gas) da shugabannin NMDPRA da NUPRC, da wakilan kamfanin man fetur na kasa (NNPCL).
Haka kuma shugabannin kungiyar ‘yan kasuwa (TUC) sun halarci tattaunawar tare da shugabannin kungiyar ta PENGASSAN da kuma mahukuntan matatar Dangote.
Idan dai za a iya tunawa dai rikicin ya samo asali ne bayan da matatar man ta Dangote ta kori mambobin kungiyar ta PENGASSAN sama da 800, lamarin da ya sa kungiyar ta fitar da umarnin dakatar da samar da iskar gas ga matatar ta kuma janye ayyukanta a fadin kasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp