Matatar Dangote ta bai wa ɗalibai 473 daga makarantu 10 na sakandare da manyan makarantu bakwai da ke yankin Ibeju-Lekki a Jihar Legas, tallafin karatu.
Wannan shiri yana da nufin tallafa wa ilimin al’umma.
- Ba Ma Cikin Waɗanda Suka Yi Sulhu Da ‘Yan Bindiga – Gwamnatin Katsina
- Samar Wa Nijeriya Sabon Kundin Tsarin Mulki Zai Magance Matsaloli – Moghalu
A cikin wannan shirin, kamfanin ya kuma bayar da kujeru da tebura 804 ga makarantu na sakandare a yankin.
Wannan gudunmawa na daga cikin ƙoƙarin Dangote na inganta muhalli na karatu da bunƙasa ilimi mai inganci.
An gudanar da taron a makarantar Idotun Community Junior High School da ke wani yanki na Lekki.
Ɗalibai, iyaye, da malamai sun taru domin taya ɗaliban da suka ci gajiyar tallafin murna da kuma gode wa kamfanin.
Baya ga tallafin karatu, ɗaliban sun samu kayan karatu kamar littattafai.
An gabatar da tallafin a ƙarƙashin Shirin Tallafin Karatu na Dangote karo na biyar, wanda ya sanya jagororin al’umma da iyalai cikin murna.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp