Matatar Dangote ta fara aikin fitar da man fetur na farko daga lita 650,000 a kowace rana daga matatar man da ke Jihar Legas.
Shugaban Rukunin Kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ne l, ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a yau Talata.
- Zanga-zanga: Ana Tuhumar Mutane 10 Da Laifin Cin Amanar Kasa
- Tinubu Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Hajiya Dada Yar’adua
Ya bayyana cewa man fetur ɗin kamfanin zai maye gurbin dogaro da shigo da da shi da ake yi daga waje tare da rage hauhawar farashin kayayyaki da daidaita darajar Naira a kan dala.
A cewarsa, man fetur din zai shiga kasuwannin ƙasar nan da zarar an kammala tattaunawa da kamfanin man fetur na kasa (NNPCL).
Kazalika, ya shaida cewa ingancin man fetur din ya yi daidai da na ko ina a faɗin duniya.
Dangote, ya kara da cewa wannan rana ce ta murna da godiya ga Allah da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da sauran masu ruwa da tsaki da suka taimaka wajen ganin matatar ta kafu.