Matatar Dangote ta rage yawan dogaron da Nijeriya ke yi na shigo da man fetur daga kasashen waje, a cewar rahoton watan Janairun 2025 da OPEC ta fitar.
Rahoton ya bayyana cewa samar da man fetur da kuma fitarwa daga matatar ke yi ya fara sauya al’amuran kasuwannin man fetur a Turai, inda yanzu dole su nemo sababbin hanyoyin sayar da man fetur.
- Me Ya Sa “TikTok Refugee” Na Amurka Suke Ta Kama REDnote Ta Kasar Sin
- Tattalin Arziki: Dalilin Da Ya Sa Ba Zan Iya Ci Gaba Da Taimakawa Gwamnatin Tinubu Ba – Sarki Sanusi II
Tsawon shekaru, Nijeriya ta dogara da shigo da mai saboda gazawar matatun mai mallakar gwamnati.
Wannan ya sa ƙasar ta kasance cikin matsananciyar damuwa game da sauye-sauyen farashin mai a duniya.
Lamarin ya ƙara taɓarɓarewa a 2023 lokacin da Shugaba Bola Tinubu, ya cire tallafin mai, wanda ya haifar da tashin farashin litar man fetur daga Naira 200 zuwa sama da Naira 1,000.
Matatar Dangote, wacce ta fara aiki a watan Disamban 2023, tana sauya kasuwar mai a hankali.
Matatar tana Jihar Legas, kuma an kashe dala biliyan 20 wajen gina ta.
Tana kuma tace gangar mai 350,000 a kowace rana, tare da burin kai wa gangar mai 650,000 a kowace rana kafin ƙarshen 2025.
A yanzu, matatar na samar da man fetur, dizal, da man jiragen sama ga ‘yan kasuwar cikin gida, wanda ya rage shigo da mai daga ƙasashen waje kuma ya sauya yanayin kasuwannin duniya.