Matatar Dangote ta rage farashin lita ɗaya na man fetur daga Naira 880 zuwa Naira 865 daga wajen dakon mai.
Wannan sabon farashi an tabbatar da shi a ranar Alhamis, kuma ana sa ran hakan zai taimaka wajen rage farashin mai a faɗin Nijeriya.
- USAID Za Ta Dawo Aiki A Wasu Ƙasashen Duniya – Gwamnatin Amurka
- Mata Sun Yi Zanga-zanga Kan Yawaitar Satar Mutane A Kogi
Wannan mataki ya biyo bayan shawarar da Gwamnatin Tarayya ta yanke na ci gaba da sayar da ɗanyen mai a farashin Naira ga kamfanonin tace mai na cikin gida.
“Muna maraba da wannan sabon farashi,” in ji Chinedu Ukadike, mai magana da yawun ƙungiyar dillalan man fetur (IPMAN).
“Yana nuna haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da ‘yan kasuwa masu zaman kansu wajen kawo wa ‘yan Nijeriya sauƙi.”
Wata sanarwa da Ma’aikatar Kuɗi ta fitar ta ce: “Wannan tsari ba na wucin gadi ba ne. Tsarin sayar da ɗanyen mai a farashin Naira wata dabara ce ta bunƙasa tace mai a cikin gida da kuma bunƙasa tsaron makamashi a Nijeriya.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp