Matatar mai ta Fatakwal ta fara sarrafa danyen mai bayan jinkirin sanar da lokacin fara aiki har sau bakwai.
A baya matatar ta tsara fara aiki a watan Maris, sannan ta dage zuwa Agusta, da Satumban 2024.
- Gwamnatin Kebbi Ta Dakile Yunkurin Lakurawa Na Satar Shanu
- Mutum 1 Ya Rasu, An Ceto 14 Yayin Da ‘Yansanda Suka Dakile Harin ‘Yan Bindiga A Katsina
Kamfanin Mai na Ƙasa (NNPCL) ne, ya bayyana wannan a matsayin babban ci gaba.
Kamfanin ya ce wannan zai zama mataki na kai wa ga dogaro da kai wajen samar da makamashi da bunkasa tattalin arziki.
An fara gyaran matatar a shekarar 2021 karkashin kamfanin Maire Tecnimont SpA, bayan sanya hannu kan kwangilar dala biliyan 1.5.
A watan Disamban 2023, aikin ya samu jinkiri saboda harkar da ta shafi tsaro da sauran matsaloli.
Fara aikin matatar zai zama babbar nasara ga Nijeriya.