Kakakin tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, wanda kuma tsohon shi ne mai ba shi shawara kan tsare-tsare, Kwamared Anas Abdullahi Kaura, ya musanta zargin cewa Matawalle ya saci kudaden jihar a lokacin da yake kan mulki.
Kaura na mayar da martanin ne kan wani rahoto da ke cewa maigidansa, Matawallen Maradun, ya yi wadaka da almubazzaranci da asusun jihar.
- ‘Yansanda Sun Mayar Wa Da Kotu Motocin Da Aka Dauka A Gidan Matawalle – ‘Yansanda
- Matawalle Ya Gwangwaje Jama’ar Zamfara Da Rabon Shanu Da Ragunan Layya
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, a ranar Litinin din da ta gabata ne wasu mutane suka yi kira ga Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) da ta kama tsohon gwamnan bisa zargin karkatar da naira biliyan 70.
Kakakin Matawallen ya ce zargin sam ba shi da tushe balle makama.
“Rahotanni sun nuna cewa masu zanga-zangar ba ’Yan Zamfara ba ne, amma wasu ‘yan boko ne ke shirin bata sunan mutumin da ya yi wa jihar Zamfara aiki iya bakin kokarinsa,” cewar Anas