Tsokacin yau zai yi duba ne game da irin matsalolin da wasu Matan ke fuskanta musamman ta fannin soyayya. Sau da dama za a ga Amare na nuna wa mazajensu soyayya ta ko ina, wanda kuma hakan bai bar kafafen sada zumunta ba, a cika status da kalaman soyayya, wake-wake kala-kala irin na zamani, duk bayan awa guda ko mintuna a dora, sai dai kuma duk da irin soyayyar da ake zubawa takaitacciya ce ba ta dadewa musamman ga su mazajen, bayan wasu ‘yan kwanaki ko watanni uku zuwa hudu ko kuma shekara guda sai zance ya sha bamban, labari ya canja.
Duk wata soyayya da kulawa da ake nunawa ko ake bayyana ta ta dauke dif! kamar daukewar ruwan sama karshe wulakanci ya biyo baya.
Duk da cewa wasu matan sukan kasance cikin soyayya na tsahon wasu shekaru wanda hakan ke sa wasu su rinka hangen ma’auratan tamkar ba su taba samun sabani a rayuwa ba sabida tsantsan soyayya da kulawar da suke nunawa junansu, wanda kuma sam ba hakan bane hakuri da fahimtar juna ke sawa soyayyar ta su ta dore har tsahon wasu shekaru. Sai dai kuma a yanzu mafi yawan Amare na fuskantar matsaloli na rashin dorewar soyayyar mazajensu, wanda wasu ma sukan fara yunkurin auro wata cikin ‘yan watanni ko shekara guda, duk kuwa da irin soyayyar da mace ke nunawa mijin, yayin da wata ta shigo gidan waccen sai ta zama abar tausayi. Da yawan irin wannan matsalar na faruwa ne ta dalilin hange-hange da wasu mazan ke da shi musamman masu auren sha’awa, da kuma tsananin soyayyar da matan ke nunawa mazajen fiye da son da namijin ke yi wa mace, da rashin dacewar mace da namiji ta fannin mu’amular aure, ko samun canjin zamantakewar rayuwa, da rashin sanin mahimmancin aure, da rashin hakuri, da gina karya tun kafin aure, da banzatar da kai na mace tun kafin aure, da dai sauransu.
Dalilin hakan ya sa wannan shafi ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiyansa game da wannan matsala, ko me yasa wasu mazan ke saurin mantawa da soyayyar da suka nunawa mace tun kafin aure?, A ina matsalar take, laifin waye tsakanin mijin da matar?. Ga dai ra’ayoyin nasu kamar haka:
Hannah Mahmoud Kaduna (Hajia Duduwa Mekan Bari):
Saboda yanzu wasu mazan kamar Auren Sha’awa suke yi da zarar sun samu abin da suke so shikenan macen ta zama kaya sai wulakanci ya kunno kai. A wannan bigiren dai laifin na mazan ne.
Eh! toh gaskiya ban taba haduwa da wacce hakan ya faru da ita ba, idan hakan ya faru da ni zan yi Addu’a kuma zan yi iya kokarina ganin hankalin mijina ya dawo gare ni in sha Allah. Eh! ina da ra’ayin hakan, Eh! toh shawarar da ya kamata a basu ita ce; indai suna san zaman auransu ya yi dadi toh gaskiya sai sun yi hakuri kuma sai da soyayya dan haka su jingine wancan ra’ayin nasu a gefe saboda babu inda zai kai su sai hanyar dana sani wanda kuwa ba a fatan zuwanta.
Hassana Yahaya Iyayi (Maman Noor) daga Jihar Kano:
Ni kaina abin na ci min tuwo a kwarya wallahi da yawa mazan yanzu basu da cika alkawari a wannan fannin, mace ta jajjirce da nuna soyayya da kulawa, status na yau daban na gobe da ban, in kina bin status na mata za ki sha mamaki! madarar raina ! alawar zuciyata, mijina, duniyata.
Amma da zarar namiji ya kyalla ido ya hango wata shikenan kin zama aljihun baya a gurinsa. Maza dai dan Allah dan Annabi a ringa sara ana duban bakin gatari. Laifin na namijin ne, ita fa mace inda ta samu kulawa an wuce wajen to wani namijin babu ruwansa da wata soyaya da zarar ya gama ‘yar murya a waje kin shigo gidan an yi ta ‘yan satitika ko watani shikken fa.
Ni kuwa na ci karo da masu irin wannan matsalar dan ni ganau ce ba jiyau ba, sai dai na ce Allah ya kyauta kawai, To in ka sa mu kanka a cikin irin wadanan kwantar da hankalinka in aure ya karo ku hace kanku ke da amaryar ku zauna lafiya. Dan kuwa abin da ya ci doma ba zai bar awai ba.
Ki basu kwanaki, ki yi kallon show! Hajiya. Ba ni da ra’ay, kawai zan ce a takaice soyayyar kafin aure a bari in an zo gida sai a barje ta, da zarrar an cinye ta, a waje tofa ana shiga gidan shikenan sai zaman hakuri da juna to an karar da ita a waje. To shawara dai anan dan Allah Maza a rika kamanta wa, ko babu yawa ita fa soyayya ba ta tsufa kullum sabuwa ce fil.
Zainab Salihu Yabagi daga Jihar Kaduna:
Na farko mafi yawancin lokuta za ki ga an samu sauyi tsakanin ma’aurata, matsalar daga dukkanin su ne, namiji da idan zai zo fira, zai siyo miki abubuwa kamar su kayan kamshi kayan makulashe da dai saura su, ita ma idan saurayinta zai zo, ta caba ado, kamshi ko ta ina, amma da zarar an yi aure duk sai su daina. Matsalar na kowanen sune, a lokaci daya ba laifin fari bare na baki, kawai sai su sauya hali, shi ya daina ji da ita kamar zamanin da take budurwar shi, ita ma yanzu tana ganin ai ta riga ta shiga gyaran jikin ma sai ya gagara.
Akwai wace nasani da take fuskantar irin wanan matsalar a yanzu haka, saboda ita ko da kiran shi tayi idan ya fita wurin aiki sai ya ga kamar tana damunsa. Idan ni ce hakan ya kasance da ni zan zaunar da shi in yi masa tambayoyi, ko shin akwai wani abu ne dana yi masa da yasa ya sauya min halayen, zan yi kokarin lalubo bakin zaren domin in ga na shawo kan matsalar, Ni kam a yandu a ra’ayi na takaitacciyar soyaya yafi, saboda ba za ku sabawa juna da wani abu bayan aure kuma ku daina ba.
Idan da dama, a soyayar wata 3-5 ma sai ayi aure, Shawarata ana shi ne; su tuna cewa su suka ga juna suka aminta da juna, idan har akwai wani abu da ya sa kaunar da suke yi wa juna ya sauya, toh su bunciki kansu, shin menene nake yi mata a baya da yake faranta mata ko nake faranta masa rai, su zauna a matsayinsu na ma’aurata su fahimci juna, saboda idan akwai kyautata a tsakanin ma’aurata zamansu zai dore, babu wanda zai ji kansu, kuma ayi hakuri da juna, a san lokacin da ya kamata ayi magana idan rai ya baci kar hankali ya gushe.
Aisha Abdulaziz Likymo daga Jihar Kaduna:
Ni dai a nawa fahimtar abin da yasa namiji yake canza wa mace bayan aure ya daina nuna mata soyayya shi ne; tun farko ba sonta yake yi ba sha’awarta yake. Laifin namijin ne mata sun iya soyayya tsakani da Allah ba gauraye.
Nasha cin karo da wadanda suka fuskanci hakan, kuma sai ace laifin matan ne Idan ba zai iya zama da ni cikin soyayya da kwanciyar hankali ba gwara ya sake ni tunda dai aure na zo yi da soyayya, kar ya bar ni da ciwon zuciya. Sosai ma kuwa ina da ra’ayi saboda ta nan ana karuwa da fahimtar abubuwa da dama.
Ni dai shawarar da zan ba da ita ce; su yi kokari su nuna wa mazan halin da suke ciki dan su gyara zamansu, in abin yaki ci yaki cinyewa ki rabu da shi tun kafin a tara yara, idan kuma aka tara yara sai ayi ta hakuri kawai.
Raheenat Mamoudou Niger Jihar Niamey.:
Wasu mazan abin da ya sa suke haka shi ne; idan basu samu yarinya a cikaÆ™iyar mace ba ma’ana idan bata kai budurcinta ba, wasu kuma suna canzawa ne idan ita matar ta daina nuna musu kulawa yadda take mishi kafin auren nasu. Wasu kuma suna canzawa ne idan Allah ya hada su da kazamar mace wace ba ta gyara jikinta kullum cikin kazanta ta ke gidanta babu wani gyara idan ta fara haihuwa kuma lamarin ya kara baci dole mijin yayi tunanin aure, na rantse wasu kuma kawai iskanci ya ke saka su yin haka dan kawai su wulakanta matansu. Babbar laifin na mata ne kina mace dole ki san yadda za ki dinga nuna wa mijinki kauna yadda zai mace a Æ™anki, wani lokacin kuma laifin na maza ne saboda ko su za su iya canzawa ako wane lokaci ba tare da dalilin komai ba. Ban taba fuskantar irin wannan matsala ba saboda ban yi aure ba tuÆ™unna, amma mata da yawa suna fuskantar irin wannan matsalolin Idan Ni ce zan dukufa kai kukana wajen rabbil izzati ya karkato min hankalin mijina gare ni na hada da kissa irin tamu ta mata. Idan da ra’ayin idan har Allah ya kawo mijin miji nagari bana so mu dauki lokaci muna soyayya saboda gudun abin da zai je ya dawo, wani lokacin jimawa a na soyayya shi ne yake kawo wasu matsalolin har a rabu ko da yake komai nufin Allah ne. Kirana a gare su shi ne, mata mu gyara idan nace gyara ina nufin mu kasance masu tsabta, ka da mu daina turawa mazajenmu kalaman soyayya idan mun yi aure hakan ya na taka muhimmiyar gudumuwa a zamantakewar aure, ko da auren zai kara ba za ki taba zama bora ba za ki zama matar so. duk yadda namiji ya kai ga taurin kai idan mun iya yadda za mu sarrafa shi zai koma mana tamkar rakumi da akala har a dinga tunanin ko asiri aka yi mishi alhalin tsabar kulawa ce, maza ku ji tsoron Allah ku daina cin zarafin matanku saboda Allah ya na ganinku kuma zai saka mata.
Saleh M. Hassan:
Tun farkon ita soyayyar da kuma auren ba a yinsu ne bisa ga turban da Allah da Manzo (SAW) suka tanadar. Akwai wasu dokoki ko nace sharuda da aka shardanta a addinance wadanda sune ya dace abi domin kaucewa shiga ko fadawa irin wadannan masalolin. Da kuwa za a bi wadannan dokokin to da hakika za a samu dai-daio na gaskiya a tsakanin masoya har zuwa ga aure. Yanzu idan muka koma a baya yadda ma’auratan da suke rike aurensu aurensu sam! baya lalacewa kamar namu a yanzu sabida sun yi gwargwadon iyawar su na bin wadannan dokoki mu kuma yanzu rawar ta can ja gaskiya. Finally In this our own generation mafi yawa ba su yin aure Don Allah Sai don manufofinsu, kuma da zarar manufar da aka yi aure dominta ta kauce sai ki kalla an fara samun masala kuma ba za a daina samun masalar ba sabida ba a yi abun don Allah ba.
Hafsat Yusuf Muhammad:
Da farko za ki ga namiji yana sonki kamar ya cinye ki wallahi wata soyayya ce ta daban wacce masoya suke yinta tun daga waje idan kuma kin je gidan, soyayar ba ta dadewa sai ya fara wulakanta ki sabida ya gama dakebabu yadda za ki yi da shi kuma idan kin haihu sai ya fara neman wata ke kuma ki shiga layin wulakanci, kuma wallahi ke ce kika ba da kan ki tun farko tun daga waje mijin da zai aure ki yana tabaki babu abin da bai sani ba ta yaya zai ganki da daraja da mutunci tsakani da Allah fa, amma wasu kuma ra’ayin mijinta ne wulakanci sai dai tayi hakuri shiyasa yawanci muke tsintar kanmu a haka sai dai Allah ya shirya mu, ya kuma ganar da mu ameen. Matsalar inda take a gurin mace ne sabida lokacin da ya zo yace ina sonki kika amince toh fa sai ya ce zai tabaki maimakon ki nuna masa bacin ranki sai ki ki sabida kar ransa ya baci ya rabu da ke, amma idan kin nuna masa bakya so idan har dan Allah yake sonki wallahi ba zai kara yi miki komai ba. Kuma ba soyayya ba kauna ma zu ku yi idan kun yi aure kuma za ki ga babu fada babu wulakanci sai kaunar juna, ni dai na ce laifin mace ne sai kin ba da fuska har namiji zai yi miki abu wata kuma wallahi kaddarar ta ce hakan. Gaskiya ne na taba ganin wacce haka ta faru gare ta kuma duk irin wannan ce sai dai Allah ya shirya masu yin hakan marasa yi ma Allah ya tsare su ya kara ganar da mu baki daya. Idan ni ce matakin da zan dauka addu’a zan tayi ita kadai ce za ta fitar da ni cikin halin dana shiga da kuma istigifari Allah ya ya yafe mana zunubanmu baki daya, ya kuma ganar da mu Allah ya kare mu da kariyarsa ameen. Gaskiya ne ina da ra’ayin takaitacciyar soyayya sabida wani zubin wallahi ba ta da amfani doguwar soyayyar a waje, idan naje gidansa sai mu yi kauna domin tafi dadi za mu fi san junanmu Allah ya raba mu da doguwar soyayya. Shawarar da zan bawa masu fuskantar irin wannan matsalar su yi kokari su gyara halinsu sai Allah ya duba su sabida duniya ba daya bace idan kana ganin ka cuci matarka wallahi sai Allah ya kama ka sabida ka zalunce ta, ke kuma ki bishi sau da kafa da kuma addu’a Allah ya ganar da mu ameen ya Allah, Allah kuma ya ba mu zaman lafiya amin.