• English
  • Business News
Friday, November 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Matsalar Da Ke Haifar Da Fitsari Mai Kumfa (Foamy Urine)

by Sulaiman and Sani Anwar
1 year ago
Foamy Urine

Mutane kan yi tambaya a kan abin da ke haifar da matsalar fitsari mai kumfa. Kafin sanin dalilin, ya kamata fahimci yadda fitsarin yake:

Fitsari ya kunshi wasu ‘yan kananan tarkacen kazanta, wadanda Koda (kidney) ke tacewa; sannan ta fitar da su daga cikin jini sakamakon ayyukan da jiki ke yi.

 

Kananan tarkacen kazantar da ke cikin fitsarin lafiyayen mutum sun hada da:

1- Ruwa kashi 95 cikin 100.

LABARAI MASU NASABA

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

Amfanin Yawan Shan Ruwa Da Kuma Illolin Rashin Yawan Sha

2- Sinadarin ‘urea’ 9.3 g/l.

3- Sinadarin ‘chloride’ 1.87 g/L.

4- Sinadarin ‘sodium’ 1.17 g/L.

  1. Sinadarin ‘potassium’ 0.75 g/L.
  2. Sinadarin ‘creatinine’ 0.67 g/L.
  3. Sinadarin ‘ammonia 30 micromole/L.
  4. Tarkace mai launin ruwan kwai, wanda ke samuwa ta hanyar lalacewar kwayoyin jini (pigmented products of blood breakdown).

Kazalika, idan mutum na da matsalar rashin lafiya; yawan sinadarin da aka lissafa a sama; zai kasance adadinsu ya fi haka ko kasa da haka a cikin fitsarinsa. Sannan kuma, za a iya samun karin sinadarai a cikin fitsarin nasa ko kuma yanayin fitsarin ya zama kamar haka:

1- Sinadarin ‘protein’ (proteinuria).

2- Sinadarin ‘glucose’ (sugar).

3- Kwayoyin jini (hematuria).

4- Rashin iya yin fitsari mai yawa (oliguria).

5- Yin fitsari mai yawan da ya wuce kima (polyuria).

6- Jin zafi lokacin yin fitsari (dysuria).

 

Abubuwan Da Ke Haddasa Fitsari Mai Kumfa (Causes of foramy urine):

Fitsari mai kumfa ya kasu gida biyu; akwai mai matsala, akwai kuma mara matsala.

 

Fitsari mara matsala na faruwa ne idan:

1- Mutum ya rike fitsarinsa na wani tsawon lokaci ba tare da ya je ya yi ba, alhali kuma ya matse shi.

2- Yayin da mutum ke sakin fitsarinsa yana fita da karfi sosai. Hakan zai sa a ga kamar kumfa na tashi; sakamakon karfin fitar fitsarin.

3- Yin fitsarin a wurin da aka wanke da sinadarin wanki (detergent) ko sabulu (soap) ko kuma sauran sinadarai masu kumfa na wanke bandaki. Ragowar kumfar sinadarin, idan ya hadu da fitsari, zai samar da kumfa ta yadda za a ga kamar fitsarin ne ke da kumfar.

  1. Ya kasance mutum ba ya shan ruwa sosai (dehydration), akwai yiwuwar fitsarinsa ya zama mai kauri (concentrated).

Hakan zai sa fitsarin nasa ya yi kumfa.

5- Daukar tsawon lokaci ana amfani da wasu magunguna na kashe radadi ko rage kumburi ko zazzabi (non-steroidal and ani-inflammatory drugs), kamar ibuprofen, diclofenac, naproden, indomethacin da sauran makamantansu, ya kan sa fitsari ya yi kumfa.

  1. Cin abinci mai zaki sosai (sugar), ko ‘protein’ zalla ba tare da an sirka shi ba, shi ma ya kan sa fitsari ya yi kumfa sosai.

 

Fitsari Mai Kumfa Wanda Ke Da Matsala

Wannan na faruwa ne sakamakon:

1- Ciwon siga (diabetes): Idan mutum na da ciwon siga, Kodarsa na shan wahala wajen tacewa da kuma hana siga da ‘protein’ din cikin jininsa daga shiga fitsarinsa. Da zarar sun shiga, fitsarinsa zai iya yin kumfa.

2- Ciwon Koda (kidney disease): ko da mutum ba shi da ciwon siga, idan yana da ciwon Koda, shi ma zai iya sa fitsarinsa ya yi kumfa.

3- Cutar mafitsara (urinary tract infection – UTI): Idan mutum yana da wannan cuta, kwayoyin cutar za su kasance a cikin fitsarinsa, don haka zai iya yin kumfa.

 

Yadda Za A Magance Yin Fitsari Mai Kumfa (Treatment of foamy urine)

Matakan da za a dauka wajen magance matsalar kumfar fitsari, ya danganta da abin da ya kawo ta. Idan ciwon siga ne ko hawan jini ko koda, sai a yi maganin wadannan cututtukan; domin fitsari ya koma daidai. Idan kuma rashin shan isasshen ruwa ne,  sai a rika shan wadataccen ruwan kuma tsabtatacce akai-kai. Idan kuma yawan rike fitsari ne, sai a rika yin sa da zarar an ji ana bukatar yin sa.

Haka zalika, yana da kyau mutum ya dage wajen cin lafiyayye kuma wadataccen abinci tare da yawan motsa jiki, sannan kuma da kokarin kauce wa shan taba sigari ko giya.

 

Daga taskar Dakta Usman Hassan

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka
Kiwon Lafiya

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

October 25, 2025
Amfanin Yawan Shan Ruwa Da Kuma Illolin Rashin Yawan Sha
Kiwon Lafiya

Amfanin Yawan Shan Ruwa Da Kuma Illolin Rashin Yawan Sha

October 19, 2025
Wasu Daga Cikin Muhimman Alamomin Ciwon Kansa
Kiwon Lafiya

Wasu Daga Cikin Muhimman Alamomin Ciwon Kansa

October 11, 2025
Next Post
tusar gaba

Abubuwan Da Ke Haddasa Tusar Gaba

LABARAI MASU NASABA

An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an

An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an

November 6, 2025
CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST

CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST

November 6, 2025
Baje Kolin CIIE Ya Bayar Da Tabbaci Ga Duniya

Baje Kolin CIIE Ya Bayar Da Tabbaci Ga Duniya

November 6, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT

Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT

November 6, 2025
Manufofin Sin Na Yaki Da Sauyin Yanayi: Gani Ya Kori Ji

Manufofin Sin Na Yaki Da Sauyin Yanayi: Gani Ya Kori Ji

November 6, 2025
Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Gina Ingantaccen Yankin Ciniki Cikin ’Yanci Na Tashar Ruwa Ta Hainan

Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Gina Ingantaccen Yankin Ciniki Cikin ’Yanci Na Tashar Ruwa Ta Hainan

November 6, 2025
Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

November 6, 2025
A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu

A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu

November 6, 2025
Gwamnatin tarayya

Ta’addanci Ba Zai Yi Nasara Ba A Ƙasarmu — Tinubu

November 6, 2025
Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

November 6, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.