Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta bayyana cewa kimanin mutane 14,500 ne ‘yan ta’adda suka kashe a yankin yammacin Afirka a cikin shekaru 4 da rabi da suka wuce.
Shugaban Hukumar ECOWAS mai barin gado Jean-Claude Kassi Brou, ya ba da wannan adadi ne a lokacin da ya ke mika wa magajinsa jawabi a hedikwatar hukumar da ke Abuja a ranar Laraba.
- Akwai Bukatar Daina Sayar Da Man Fetur A Kan N165 – MOMAN
- Shugaban Sri Lanka Gotabaya Rajapaksa Ya Tsere Daga Kasar
Ya kara da cewa adadin ‘yan gudun hijira a yankin da ke neman taimakon jin kai ya kai 5,500,000.
Ya ce, “Da farko dai tabarbarewar tsaro ta haifar da barna ba a yankin Sahel kadai ba, lamarin da ya shafi kasashen Mali, Burkina Faso, Nijar da kuma Arewa maso Gabashin Nijeriya, amma nan da nan ya fadada zuwa yankin gabar teku, inda ya afkawa Cote d. ‘Ivoire, Benin da Togo.
Hare-haren ta’addanci da na barayi ya jefa wadannan kasashe cikin tashin hankali, inda kusan mutane 14,500 suka mutu cikin shekaru hudu da rabi, lamarin da ke barazana ga zaman lafiyar mazauna karkara, tare da tilastawa mutane neman mafaka daga yankunansu.
“Don haka, adadin ‘yan gudun hijira da mutanen da suka rasa matsugunansu a yankinmu ya kai kusan mutane 5,500,000 wadanda ke bukatar agajin jin kai.”
Sai dai dan kasar Ivory Coast, ya ce hukumar ta kai dauki don ba da taimako ga wadanda bala’in ya shafa.
Ya ce an bi wani shiri na yaki da ta’addanci a yankin, yana mai jaddada cewa shirin na bukatar jajircewa mai dorewa gami da tallafin kudi daga kasashe mambobin kungiyar domin samar da sakamakon da ake sa ran.