Duk da ayyukan samar da zaman lafiya da jami’an tsaron mu suka kaddamar a sassa daban-daban na jihohin arewa 19 da babbar birnin tarayya Abuja har yanzu an kasa samar da tsaro ga al’ummumun yankin. A kullum labarin kashe-kashe da sace-sacen mutane ke mamaye kafafen yada labarai. Bayan haka kuma sai gashi a ‘yan kwanakin nan an fuskanci hadurran kwalekwale da ambaliyar ruwa da suka yi sanadiyyar rasa rayukan mutane da dama a yankin na arewa.
Bayani ya kuma nuna cewa, duk da dai aikin kasa suke yi amma Ministocin tsaro biyu da muke da su, Mohammed Badaru Abubakar da Bello Matawalle daga bangaren arewacin kasar nan suke.
Haka kuma, mai ba shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu da babban hafsan tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa suma daga arewacin Nijeriya suka fito amma haka bai yi tasiri ba wajen kawo karshen matsalar a yankin na arewa.
- Sin Ta Yi Kira Ga Gamayyar Kasa Da Kasa Da Su Mutunta ’Yancin Kan Sudan Ta Kudu A Lokacin Mulkin Rikon Kwarya
- Ɗan Takarar Shugaban Ƙaramar Hukuma Zai Biya Naira Miliyan 10 A Kano
Harkokin samar tsaro 5 da sojoji ke tafiyarwa a jihohin arewacin Nijeriya 19 a halin yanzu sun hada da ‘Operation Hadin Kai’ a yankin arewa maso gabas, inda ake tunkarar ‘yan boko haram da ‘yan kungiyar ISWAP; ‘Operation Hadarin Daji’ a arewa maso yammancin kasar nan inda ake fatattakar ‘yan bindiga da’yan ta’adda sai kuma ‘Operation Safe Haben’ da ke gudana a yankin arrewa ta tsakiya duk dai a yaki da ake yi da ‘yan ta’adda da kuma matsalar tsaro gaba daya.
Haka kuma jami’an tsaro na nan a karkashin shirin ‘Operation Whirl Punch’ a yankin arewa maso yammaci da kuma ‘Operation Whirl Stroke’ a arewa ta tsakiya suna fafutukar kawo zaman lafiya a rikicin manoma da makiyaya.
Ayyukan jami’an tsaro na samar da tsaro a sassan arewa 5 da ke gudana domin kawo karshen ta’addanci, rikicin manoma da makiyaya da garkuwa da mutane ya kai ga kashe ‘yan ta’adda fiye da mutum 5,169 an kuma samu nasarar kama ’yan ta’adda 6,780.
Bayani ya nuna cewa, duk da samu nasarar ceto mutum fiye da 3,713 daga hannun ‘yan ta’adda a cikin wata 7 amma har yanzu ba a hangi rana ko lokacin da za a kawo karshe matsalar tsaron a arewa ba, domin har yanzu ana ci gaba da kasha-kashe da sace-sacen mutane a sassan arewa kuma abin sai karuwa suke yi.
Dukkan wadannan ayyukan da jami’an tsaron ke a jihohi 19 har da Abuja sun kai ga mace-mace, kame- kamen ‘yan ta’adda da kuma ceto da dama daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su a cikin wata 7 da suka gabata amma hakan bai kai ga sanya natsuwa ga mutanen yankin ba domin suna a kullum cikin fargaba a ken a ta’asar ‘yan ta’adda.
Haka kuma jam’an tsaro sun sami nasarar kashe ‘yanta’adda 5,169 sun kuma kama 6,780 tare da ceto mutum 3,713 daga hannun masu garkuwa da mutane a cikin wata 7.
Sun kuma yi nasarar kwato makamai fiye da 2,783 da hannun ‘yan ta’addan a daidai lokacin da muke magana.
A tsokacin wani tsohon janar na soja, mai suna Manjo Janar James Nyam (mai ritaya), ya ce ayyukan sojoji ba zai iya kawo karshen matsalar tsaron da muke fuskanta ba, musamman ganin an zo wannan matakin ne sakamakon tabarbarewar harkokin gwamnati a tsawon shekaru.
Ya ce nasarorin da ake ganin an samu a kan ‘yan ta’adda da ta’addanci ba zai yi maganin ainihin matsalolin da ake fuskanta ba, zai da yi maganin matsalar ne daga sama-sama.
Ya kuma kara da cewa, amfani da karfin soja ba zai taba kawo karshen matsalar tsaro da tabarbarewar gwamnati ya haifar da shi a tsawon shekaru ba, gwamnati ta kasa biya wa al’umma bukatunsu na yau da kullum.
“In har ana son a samu cikakken zaman lafiya dole a yi maganin matsalolin da rashin iya mulki ya haifar, wadanda suka hada rashin adalci, samar da aikin yi ga matasa da shigar da su cikin siyasar kasa, yaki da talauci da bayar da igantaccen ilimi ga al’umma gaba daya.
“In har ana ci gaba da zaluntar al’umma to babu irin karfin soja da zai samar da zaman lafiya a tsakanin al’umma.
“Muna ta kokarin maganin matsalar tsaro amma ba daga tushe ba, in har bamu yi maganin matsalaar daga tushe ba, ba za mu taba samun tsaron ba, wannan shi ne abin da shugabanin siyasa da dama basu sani ba ko kuma suka ki sa hankali a kai,” in ji shi.
Shi kuwa babban jami’i a hedikwatar tsaro ta tarayya, Manjo Janar Edward Buba, ya ce, duk da nasarar da jami’an tsaronmu ke samu a fagen daga, kashi 30 ne kawai na maganin matsalar tsaron da ke arewa, sauran kashi 70 yana tattare da baza adalci daga gwamnati ga al’umma, ta hanyar samar musu da ababen more yaruwa da kuma shigar da su a tsarin tafiyar da gwamnati suma su san ana yi dasu.
A wani bangare kuma majalisar dokokin Jihar Nasarawa ta nuna damuwar su a kan yadda harkokin masu garkuwa da mutane ke karuwa a sassan Jihar a ‘yan makwannin nan.
Mataimakin shugaban majalisar, Mista Muhammad Oyanki, ya bayyana haka a zauren majalisar a karkashin dokar ‘yancin fadin albarkacin baki a zaman majalisar ranar Litinin, a garin Lafia.
A nasa martanin, shugaban majalisar Mr Danladi Jatau, ya umarci shugabannin kananan hukumomi su gaggauta kiran taro na musamman domin tattauna matsalar tsrao a yankinsu, ya ce, ya kamata taron ya samu wakilcin jami’an tsaro da sarakunan gargajiya na yankin, inda ake sa taron zai tattauna tare da fitar da hanyoyin kawo karshen matsalar tsaron gaba daya.
Ya kuma gode wa Oyanki da dukkan ‘yan majalisar a bisa gudummawarsu ga tattaunawar, ya kuma yaba wa Gwamna Abdullahi Sule da jami’an tsaron jihar a bisa kokarinsu na kawo karshen matsalar tsaron.
Ya nemi a tabbatar da ana bin dokokin yaki da masu garkuwa da majalisar ta kafa a kwanan nan.
Shugaban majalisar ya kuma nemi hadin kan al’umma ga jami’an tsaro domin su samu nasarar fattakar bata gari ta hanyar basu bayanan sirri.
A halin yanzu ‘yan bindiga na ci gaba da tafka ta’asa a sassan arewacin Nijeriya, inda aka bayar da rahoton yadda suka kashe mutum12 a jihohin Taraba, Zamfara, Neja da Kaduna a cikin makon jiya.
A Jihar Taraba an kashe mutum 7 ciki har da direban wata mota da sanyin safiyar ranar Litinin a kan hanyar Takum zuwa Wukari.
Wata majiya daga garin Takum ta bayyana wa manema labarai cewa, dukkan fasinjojin sun fito ne daga garin na Takum suna kuma kan hanyar su ne ta zuwa Wukari inda ‘yan bindigan suka kai musu hari a tsakanin garin Chanchangi a karamaar hukumar Takum da kauyen Saai da ke Jihar Benuwai.
Majiyar ta ce, an bude wa motar wuta ne inda anan take mutum 7 suka mutu ciki har da direban da aka bayyana sunansa a matsayin Kabiru.
An ce ‘yan bindigan basu saci komai ba a cikin motar, ana zargin ‘yan ta’adda ane daga dazukan Jihar Benuwai. A wannan hanyar ne ‘yan bindiga suka kashe wani basarake daga Chancangi da dansa a watan Yuli.
Tuni hanyar ta zama tarkon mutuwa inda ’yan ta’adda ke kai hari suna cutar da mutane da rana tsaka da kuma dare.
Jami’in ‘yan sandan jihar Taraba DSP Kwache Gambo, ya ce, cikin wadanda aka kashe akwai malami a jami’an tarayya ta Wukari da wani baban ma’aikaci na makarantar kiwon lafiya ta garinTakum.
Haka kuma, a ranar Litinin ne ‘yan ta’adda a hare-hare biyu da suka kai kauyen Magazu ta karamar hukumar Tsafe suka sace mutane da dama. A hari na farko ‘yan ta’addan sun kai wa matafiya a cikin motoci da misalin karfe 5:15 na yamma inda suka kashe direban motar suka kuma sace mutane da dama.
Daga nan kuma suka sake dawowa daidai inda suka tafka wanncan ta’asar da misalin karfe 6:30 suka farmaki wata mota kirar Golf suka kwashe dukkan fasinjojin da ke ciki.
Majiyarmu ta bayyna cewa, a hari na farko da ’yan ta’adda sun kulle hanyar inda suka yi ta harbin kan mai uwa da wabi, a kan haka wasu motoci 4 suka fada daji sakamakon harbe-harben da ake kai musu.
Masu sharhi sun bayyana cewa, ayyukan ta’addanci ya dawo dakarfinsa a ‘yan kwanakin nan a kan hanyar Funtuwa zuwa Gusau kamar yadda mazauna garin Magazu da Tsafe suka bayyana.
Da aka tuntube shi, Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Zamfara CP Muhammad Shehu Dalijan ya tabbatar da aukuwar hari daya ne daga cikin hare-haren da aka kai babbar hanyar Gusau zuwa Funtuwa, “Na dai ji labarin harin da aka kai wa wani direba amma sauran hare-haren ba ni da labarinsu, da zaran na samu labarin su zan tuntube ka.” In ji shi.
Akalla manoma biyu suka rasa rayukansu yayin da aka sace mutane da dama lokacin da ‘yan ta’adda suka kai hari yankunan Mariga da Mashegu da ke karamar hukumar Neja.
Wadanda suka ji ciwo da yara kananan na nan a babban asibitin Kontagora. Kauyukan da aka kai wa hari sun hada da Durgu, Bobi, Kurigi, Wamba, Mongoro, Igwama, Kasuwan-Garba a karamar hukumar Mariga da kuma Uro da ke karamar hukumar Mashegu.
Mazauna garin sun bayyana wa manema labarai cewa, an kai harin ne da misalin karfe 5 na yammacin ranar Lahadi an kuma sace musu shanaye da dama.
Kokarin tuntubar kwanishinan tsaron cikin gida na Jihar Neja, Birgediya Janar Bello Abdullahi Mohammed ya ci tura domin baya daukar wayar da aka yi masa domin jin martanin gwamnati a kan harin da aka kai.
Haka kuma jami’in watsa labarai na rundunar ‘yansanda na jihar, SP Wasiu Abiodun ya ce a halin yanzu bashi da cikakken bayani a kan hare-haren amma zai tuntube mu da zaran ya samu cikakken bayanai, amma har zuwa hada wannan labarin ba mu ji duriyyarsa ba.
Bayani ya kuma nuna cewa, ‘yan bindiga sun farmaki kauyen Kwassam da ake karamar hukumar Kauru a Jihar Kaduna in suka kashe wani mai suna Doctor Ishaya suka kuma yi awon gaba da mutum 8.
Da yake tabbatar da aukuwa harin a tattaunawa ta wayar salula da aka yi da shi, dan majalisar wakilai mai wakilatar yankin, Hon. Zakari Ahmad Chawai ya ce, yankin ya fuskanci hare-hare da dama a ‘yan kwanakin nan.
“Kwana hudu da suka wuce, ‘yan ta’addan sun farmaki yankin Dawaki inda suka yi garkuwa da wasu mutane sai kuma gashi sun sake kai hari yankin Kwassam inda suka yi barna mai yawa,” in ji shi.
Ya kara da cewa, masu garkwuan sun kashe mutum daya suka yi garkuwa da mutum takwas yayin da suka kuma sace dukiyar da ba kai ga kiyastawa ba zuwa yanzu.
Kifewar Kwalekwale
Bayan yadda matsalar tsaro ke lakume rayukan al’umma a yankin arewa, hadurran kwalekwale da cin rayukan al’umma.
Ko a ranar Lahadi hadarin kwalekwale ya yi sanadiyyar mutuwa mutum 5 in da har zuw yanzu ana neman fiye da mutum 13 a hadarin da ya auku a rafin Dundaye dake karamnar hukumarWamakko ta jihar Sakkwato.
Bayani ya nuna cewa, kwalkwalen kirar katako yana dauke ne da mutum 35 wanda hakan ya nuna sun yi yawa fiye da ka’iddar da aka kayyade wa jirgin, wanda ya yi sanadiyya kifewar jirgin.
Wani mai suna Muhammad Bello da aka yi abin a gabansa y ace, nauyin mutane ne ya sa kwalekwalen ya cika da ruwa har ya kife, amma an samu nasarar ceto wasu da ransu.
Mataimakin Darak a hukumar bayar da agajin gargajiya (NEMA) ya jagoranci mataimakin gwamnan Idris Muhammad Gobir, da Snata Aliyu Magatakar Wamakko inda suka kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan wadanda suka mutu da kuma wadanda suke jinya. Wannan shi ne hadarin kwalekwale na 4 a cikinmako daya, wanda hakan yake tayar da hankulan al’umma.
Ambaliyar Ruwa
Wani abin da kuma ya lakume rayukan al’ummar arewa a cikin ‘yan makwannin nan shi ne ambaliyar ruwa.
Zuwa yanzu kimanin Mutane 16 ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwan sama a Jihar Jigawa.
Babban sakataren hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Jigawa (SEMA) Alhaji Haruna Mairiga ne ya bayyana haka a lokacin da yake ganawa da manema labarai a ofishinsa da ke sakatariyar jihar da ke birnin Dutse.
Alhaji Haruna ya kuma bayyana cewa, kimanin Mutane 3,936 ne suka rasa gidajensu yadda kuma gidaje 3,834 suka rugurguje gamida mutane 2,734 wadanda suka rasa gonakinsu.
Haka kuma ya bayyana cewa, ambaliyar ta kuma shafi kananan hukumomi goma cikin kananan hukumomi 27 dake fadin jihar.
Sannan ya kara da cewa, hukumar ta SEMA tare da goyon bayan gwamnan jihar Malam Umar Namadi ta kafa kwamitoci don bada tallafin gaggawa a matakan mazabu, kananan hukumomi da kuma jiha baki daya.
Haka kuma an kafa sansanin wadanda gidajensu ya rushe har guda goma wadda aka yi amfani da makarantun gwamnati a wadannan kananan hukumomi goma da al’amarin ya shafa.
Haka kuma Ambaliyar ruwan wadda ta faru sakamakon share sa’o’i ana sheka ruwan sama ta yi sanadiyyar lalata hanyoyi ciki har da babbar hanyar Malawan Babaldu wadda ta hada jihohin Bauchi, Gombe, Adamawa, Taraba da ke cikin Jihar ta Jigawa.
Bayanai sun kuma nuna yadda ambaliyar ta kasha mutane da dama da lumaawon gaba da albakatun gona a jihohn Bauchi, Yobe, Kaduna Zamfara da sauransu.