Duk da umarnin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba sojojin Nijeriya da sauran jami’an tsaron kasa na su tabbatar da kawo karshen ayyukan ta’addanci a sassan kasar nan tare da dawo da zaman lafiya kafin karshen watan Disamba na shekarar 2022, ayyukan ta’addanci irin su garkuwa da mutane, kashe-kashe suna ci gaba da cin rayukan al’umma a sassan kasar nan ba kakkautawa.
Wato duk da ba a iya kawo karshen kashe-kashen ba amma masana sun tabbatar daan samu raguwar kashe-kashen a cikin watanni 4 da suka wuce.
Bayani ya nuna cewa, an kashe akalla mutum 671 ciki kuwa da fararen hula, jami’an ‘yansanda dana sojoji tun bayan da Ministan cikin gida, Rauf Aregbesola ya sanar da umarnin na shugaban kasa a taron manema labarai na kasa da kasa da aka yi a watan Satumba na shekarar 2022 na cewa, Shugaba Buhari ya umarci shugabanin rundunonin tsaro su fattataki ‘yan ta’adda su kuma tabbatr da kawo karshen su zuwa karshen shekarar 2022.
Amma abin takaicin shi ne an ci gaba da kashe al’umma tun bayan da wa’adin ya kare. ‘Yansanda 4 sun rasa rayukansu a yayin da ‘yan bindiga suka farmaki tawagar tsohon Gwamnan Jihar Imo Ikedi Ohakim a daidai kauyen Ehime da ke karamar hukumar ta jihar.
Haka kuma, duk da kasancewar sojoji na sintiri a sassan kasar nan amma ‘yan ta’adda sun ci gaba da kai hare-hare tare da sace mutane suna garkuwa da su a jihohin Zamfara, Katsina da Kaduna.
Rahoton da jaridar Daily Trust ta bayar ya nuna cewa, al’ummar Nijeriya sun ci gaba da fuskantar matsaloli daga manyan kungiyoyin ‘yan ta’adda nan kamar su Boko Haram da ISWAP ga kuma rikicin manomja da makiyaya ga kuma ayyukkan ta’addancin ’yann aware na masu neman kafa kasar Biafra (IPOB).
Kididdigar da jaridar Daily Trust ta samar ya nuna cewa, daga cikin mutum 671 da aka kashe a cikin wattani 4 da suka wuce, 614 fararen hula ne, 47 kuma jami’an sojoji ne yayin da 10 daga cikin su jami’an ‘yansanda ne an kuma tabbatar da sace mutun 1,321 a tsakanin watan Satumba zuwa Disamba.
Kashi 80 Na Wadanmda Suka Mutu Da Wadanda Aka Sace Daga Arewa Ne
Daga cikin mutum 614 aka kashe a tsakanin watan Satumba zuwa Disamba na shekarar 2022, bayani ya nuna cewa, kashi 85 na wadanda suka mutu an kashe su ne a yankin arewacin Nijeriya yayin da kashi 15 ne suka fito daga kudancin kasar. Bayanin ya kuma nuna cewa, kashi 57 na mace-macen ya faru ne a jihohi 5 na arewacin Nijeriya, a inda Jihar Benuwai ke a kan gaba da mutuwar mutum 120, Jihar Kaduna na biye da mutuwar mutum 69 sai kuma JIhar Zamfara inda mutum 60 suka mutu sai Jihar Filato inda mutum 48 suka mutu haka kuma mutum 42 sun mutu a Jihar Neja a daidai lokacin da muke magana a kai. Jihohin da aka samu mace-mace sun kuma hada da Abia, Osun, Ekiti da inda mutum dai-dai suka mutun sai Jihar Bayelsa inda mutum 2 suka mutu, Jihar Kano kuma mutum 3, haka kuma a jihohin Nasarawa, Ribers, Gombe da Ondo an rasa rayukan mutum 4 a kowannensu.
Bayanai daga kididdigar jaridar Daily Trust na wadanda aka sace ya nuna cewa, daga cikin mutum 1,321 da aka sace a tsakanin watan Satumba zuwa Disamba ya nuna cewa kashi 84 na wadanda aka sacen sun fito ne daga arewacin Nijeriya, inda kashi 16 kuma aka sace su a kudancin kasar. Haka kuma bayanin ya nuna cewa, kashi 62 na sace-sacen mutane da aka yi an yi ne a jihohi 5 na arewacin Nijeriya wadanda suka hada da Jihar Kaduna, Zamfara, Nija, Katsina da Sakkwato. Jihar Kaduna ne a kan gaba da mutum 256 sai Jihar Zamfara inda aka sace mutum 246 a Jihar Neja an sace mutum 127 a Jihar Katsina an sace mutum 116 yayin da kuma aka sace mutum 74 a Jihar sakkwato.
Bayanin ya nuna cewa, mutum dai-dai aka sace a Jihohin Osun da Legas inda kuma aka samu labarain sace mutum biyu-biyu a jihohin Kano, Gombe da Abia, yayin da aka samu rahoton sace mutum uku a JIhar Jigawa inda kuma aka sace mutum biyu a Jihar Bauchi an kuma sace mutum biyar a Jihar Imo.
Kididdigar ya nuna raguwar da aka samu a yawan mace-mace musamman a Jihar Kaduna inda a baya (watan Afrilu zuwa Yuni) mutum 285 suka mutu a tsakianin watan yuli zuwa Satumba kuma mutun 161 ne suka mutu.
•Kudu Maso Gabashin Nijerriya Aka Fi Kashe ‘Yansanda
A kudu maso gabashin Nijeriya inda ‘yan kungiyar IPOB suka zafafa hare-hare a kan cibiyoyn jami’an tsaro, sun samu nasarar kashe jami’an tsaro 24 a jihohin Inugu, Imo, Anambra, Ebonyi da Abia a tsakanin watan Satumba zuwa Disamba. Sai yankin Arrewa maso Yamma inda ayyukan ‘yan ta’adda ya yi sanadiyyar mutuwar jami’an ‘yansanda 9 a jihohn Kebbi, Sokoto, Katsina da kuma Kaduna. Rundunar ‘yansanda ta kuma rasa jami’ai 7 a yankin kudu maso kudancin kasar a jihohin Ribers da Edo an kuma kashe ‘yansanda 4 a arewa ta tsakiya inda jihohin Benuwai, Kogi da yankin Abuja. Haka kuma ‘yansanda 3 sun mutu a yankin kudu maso yammacin kasar nan na jihohin Ekiti da Oyo. Amma kuma duk da harkokin ta’addanci a yankin arewa maso gabas babu rahoton kashe jami’in ‘yansanda a yankin, sai dai an samu rahoton kashe sojoji 10 a Jihar Borno.
•An Kashe ‘Yan Ta’adda Da Dama A Cikin Wata 4
Duk da rashin iya kawo karshen kashe-kashe a Nijeriya da juami’an tsaro suka kasa sun samu gaggarumar nasara tun bayan da Shugaban Kasa Buhari ya bayar da umarnin a kawo karshen harkokin ta’addanci zuwa karshen watan Disamba na shekarar 2022.
Kididdiga ya nuna cewa, jami’an tsaron Nijeriya sun kashe ‘yan ta’adda 267 a Jihar Borno a tsakanin watan Satumba zuwa Disamba. Haka kuma an kashe fiye da ‘yan ta’adda 200 a hare-haren jiragen sama dana sojojin kasa a yankin Jihar Zamfara ta tsakiyar watan Nuwamba.
Haka kuma an kashe wasu ‘yan ta’adda 34 a yankin Jihar Kaduna kamar dai yadda kwamishinan kula da tsaron cikin gida Mista Samuel Aruwan ya sanar.
Bincike ya nuna cewa, wadanda aka kashen zai iya zarce wadannan alkaluma musamman ganin sau da yawa jami’an tsaro na tabbatar da kashe ‘yan ta’adda da dama amma ba tare da bayar da kididdigar yawan wadanda aka kashen ba.
•Masana Sun Ce Al’amarin Tsaro Ya Inganta
Duk da yawan alkaluman kashe-kashe da garkuwa da mutane da aka yi a cikin watanni hudu, masana a bangaren harkar tsaraon sun nuna cewa, an samu ingantuwar harkar tsaro tun bayan da Shugaba Buhari ya bayar da umarnin a kawo karshen ayyukan ta’addanci zuwa watan Disamba. “Ba zai taba yiwuwa ba a kawar da harkokin ta’addanci gaba daya ba” in ji Dakta Tanko masani a harkar tsaro a makarantar yaki ta ‘War College’ da ke Abuja.
“A yankin Arewa maso Gabas al’umma na ta komawa gidajensu bayan hijirar da suka yi, in har babu ingantuwa tsaro ta yaya za su koma?, akwai kuma bukatar jami’an tsaro su hada hannun tare da aiki da al’umma don samun cikakken nasarar da ake buikata.
“Tabbas an samu raguwar hare-haren ‘yan Boko Haram, da yawa daga cikin su suna ta mika wuya, an kuma samu cikakken tsaro a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja. ‘Yan Nijeriya na zirga-zirgar su a halin yanzu cikin aminc,” in ji shi.
Wani tsohon mataimaikin shugaban rundunar ‘yansandan Nijeriya, (AIG), Wilson Inalegwu ya tabbatar da samu ingantuwar lamarin tsaro a Nijeriya, “Al’umma da dama na iya tafiye-tafiye a ba tare da wani tsoro ba kamar yadda ake yi a can da, an samu karuwar tsaro a kan hanyoyinmu.”
Inalegwu wanda tsohon kwamishinan ‘yansandan Abuja ne ya kuma nuna takaicinsa a kan yadsda ake samun karuwar hare-hare a kan jami’an tsaro musamman a kan ‘yansanda a yankin kudu masu gabashn kasar nan.”
“A tunani na harkokin IPOB dana ‘Eastern Security Network’ irin na ‘yan tawaye ga gwamnatin tarayya ne shi ya sa suke ganin juami’an tsaro musamman ‘yansanda a matsayin abokan gaba,” in ji shi.
•Masana Sun Nemi A Bayar Da Karfi A Kan Neman Bayanan Sirri Daga Al’umma
Dukkan su, Dakta Ahmed da AIG Inalegwu (Mai ritaya), sun bayyana cewa, in har ana son a kawo karshen manyan matsalolin tsaron kasar nan dole a sauya fasalin tsarin jami’an tsaronmu, daga tsarin da aka san shi a da zuwa yadda za a yi aiki tare da al’umma don hada hannu a kawo kaeshen matsalar tsaro a kasar baki daya.
“Inda nine shugaban kasa ba zan sake ba jami’an tsaro wani wa’adi ba kuma amma zan dai basu dukkan tallafin da suke bukata na ganin an samar da tsaro a Nijeriya zan kuma yi amfani da dukkan hukumomin gwamnati don su zaburantar da al’umma wajen bayar da gudunmawar ganin suna bayar da bayanan sirri ga jami’an tsaro don su samu nasarar murkushe harkokin ‘yan ta’adda gaba daya,” in ji Dakta Tanko Ahmed.
Shi kuwa AIG Wilson Inalegwu (Mai Ritaya), ya bayyana cewa, za a iya cimma gaggarumn nasara a yaki da ta’addanci ta hanyar amfani da da bayanan sirri daga al’umma tare da kuma yin kuste a cikin ‘yan ta’addan ta yadda za a rika sanin halin da suke ciki a lokacin da suke shiryawa da kuma tattauna yadda za su kai hari tun kafin su kai harin.
•Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Gum A Kan Wa’adin Da Ta Bayar
A halin yanzu kuma fadar shugaban kasa ta ki cewa komai a kan wa’adin da ta ba jami’an tsaro na su kawo karshen harkokin ta’addanci a Nijeriya zuwa ranar 31 ga watan Disamba 2022.
Mataimakin shugaban kasa na musamman na kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, bai amsa sakon da aka yi masa ba bayan da ka yi ta kiran wayarsa a daidai lokacin da ake shirya wannan rahoton.
Amma kuma idan za a iya tunawa a jawabinsa na shiga sabuwar shekarar 2023, shugaban kasa ya bayyana cewa, gwamnatinsaa za ta samar da sabbin tsare-tsare wadanda za su kai ga kawo karshen mastalar tsaro da bunkasar tattalin arzikin kasa tare da kuma yaki da cin hanci a dukkan bangarorin gwamnati.
Shugaban kasan ya ce, yakin da ake yi da masu garkuwa da mutane da sauran ayyukin ta’addanci a yankin arewa maso yamma na samun nasara sosai, ya kuma bayar da misali da dawowar harkokin zirga-zirgar jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja.
Ya kuma kara da cewa, an samu gaggarumin nasara a fattakar ‘yan ta’adda a yankin arewa maso gabas, wanda hakan ke nuna nasarar da ake samu a yankin gaba daya a wannan shekarar.
“Zamu ci gaba da fattakarsu da tarwatsa harkokin ‘yan ta’adda a dukkan sassan Nijeriya tare da aiki da al’umnma domin samun cikakiyyar nasara a kan ‘yan ta’adda don sai an hada hannun da mutane gaba daya,” in ji shugaban kasa.