Alhamdulillah, a ranar Laraba, 31/01/2024 an kaddamar da ASKARAWAN JIHAR ZAMFARA masu suna Zamfara State Community Protection Guards (ZSCPG)
Ya ‘yan uwana masu daraja, lallai duk mai bibiyar lamurran da suke gudana a wannan kasa ta mu mai albarka, wato Nijeriya, tabbas na san yana sane da irin matsalolin da Allah Subhanahu wa Ta’ala ya jarrabe mu dasu, musamman abun da ya shafi rashin tsaro da abubuwan da suke da alaka da shi.
- Hukuncin Zaben Adamawa: Na Rungumi Kaddara – Binani
- Matsalar Tsaro: Gwamna Dauda Ya Kaddamar Da ‘Askarawan’ Zamfara
Akan wannan matsala ta tsaro, hakika mun tabbata, ko shakka babu, Gwamnatocinmu, tun daga na kananan hukumomi, har zuwa na jihohi, har zuwa na tarayya, duk suna iyakar kokarinsu wurin ganin cewa, Allah ya yaye muna wannan ibtila’i da ke damun mu.
Jami’an tsaron mu kuwa, tun daga sojoji, na sama dana kasa dana ruwa, har zuwa ‘yan sanda masu kaki da na farin kaya, har zuwa sibil difens, har zuwa kwastam, har zuwa imagireshan, har zuwa masu kamen masu shaye-shaye, har zuwa ‘yan Hisbah, ‘yan Zarota, ‘yan Karota, kai da duk dai wani jami’in tsaro da muka sani, wallahi duk suna iya kokarinsu, wurin ganin cewa mun samu zaman lafiya a tsakaninmu.
Kamar yadda muka sani ne, wasunsu sun sadaukar da rayukansu, sun yi shahada, wurin kare kasarsu da al’ummarsu. Wasu sun rasa ido, wasu sun rasa hannu ko kafa, wasu duk a wannan hanya sun nakasa har abada, nakasar da ba zasu sake morar kan su ba balle su mori wasu. Kuma duk ba don komai ba wallahi, sai don kishin kasarsu da al’ummarsu.
Kuma dukkaninmu muna sane da koyarwar addinin musulunci, muna sane da irin tanadin da addini yayi akan masu kishin kasa, da kuma sakamakon wanda duk ya sadaukar da rayuwarsa akan kishin kasarsa da al’ummarsa.
Tun daga shugaban kasa, har Gwamnoni, har Shugabannin kananan hukumomi, har ministoci, duk kowa yana bayar da gudummawa, gwargwadon ikonsa, wurin ganin mun samu mun yi bacci da idanuwanmu.
A irin wannan hobbasa da kokari ne, Allah cikin ikonsa, ya kaddari wasu daga cikin Gwamnoninmu suka yi tunanin cewa bari su samar da wasu jami’an tsaro na musamman, domin ganin sun taimakawa jami’an tsaronmu, don ganin an cimma burin da ake so a cimma.
Kuma samar da wadannan Jami’an tsaro, sam wallahi baya nufin cewa, wadannan Gwamnoni sun raina irin kokarin da Shugaban kasa yake yi, ko kokarin da ministoci suke yi, ko kokarin da jami’an tsaronmu suke yi, sam ba haka bane. Kawai an samar da su ne domin a hada hannu, ayi aiki tare, wurin ganin cewa an cimma nasara. Saboda idan mun yi la’akari da girman wannan matsala ta tsaro, to zamu fahimci cewa ba karama bace.
Don haka, muna kira. Don Allah, don Allah, don Allah kowa ya tsarkake zuciyarsa, ayi aiki tare kuma domin Allah.
A cikin irin wannan ne kwanakin baya can, Gwamnan jihar Katsina, Alhaji Dikko Raddah, ya kaddamar da irin wannan runduna. Sannan bayan shi sai ga shi yau Laraba, 31/01/2024, Gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Dauda Lawal shima ya kaddamar da runduna mai suna, ASKARAWAN JIHAR ZAMFARA (ZSCPG).
To anan, kiran da zan yi a gare mu, dukkanin mu, shine, don Allah duk abunda zamu fadi game da wannan yunkuri, to ya zamanto alkhairi ne, idan ba haka ba kuwa muyi shiru.
Dalilin wannan kira shine, domin naji wasu magoya bayan Matawalle suna wasu gunaguni a gefe, game da wannan aiki da Gwamna Dauda Lawal ya kaddamar. Wasu kuma magoya bayan Gwamna Dauda Lawal, su kuma suna wasu ‘yan soke-soke game da Ministan tsaro Bello Matawalle. Wanda wallahi duk wannan bai dace ba, kuma ba daidai bane.
Kamar yadda kowa ya sani ne, mu Zamfarawa an san mu da girmama na gaba, an san mu da da’a, da biyayya, da tarbiyyah, da kunya, da mutunta dan Adam, da halin karimci. Ba’a san mu da halin rashin kunya, ko rashin tarbiyyah, ko rashin da’a, ko rashin mutunci, ko cin mutunci, ko raina mutane ba.
Ya kamata ‘yan siyasarmu su ja kunnen mabiyansu da magoya bayansu. Yiwa babba ko na gaba da kai rashin kunya, ko rashin mutunci, sam ya sabawa karantarwar addininmu, kuma ya sabawa al’adunmu.
Yanzu misali, wasu basu samu damar zuwa taron yau ba, saboda wasu dalilai da suka sha karfinsu, an zage su, ance basu da kishin jiharsu. Wasu kuma sun samu damar zuwa amma an ci mutuncinsu, an wulakantasu a wurin taron. DON ALLAH WANNAN ME YAKE NUNAWA DUNIYA GAME DA AL’UMMAR JIHAR ZAMFARA?
Kun ga irin wadannan abubuwa muke duba wa, muna magana akan su, domin gyaran jiharmu da ci gaban ta fa.
Matukar muna son cin nasara fa sai mun bi tsarin gaskiya fa dole. Idan ba haka ba kuwa…
Mu sani, dukkanin mu muna son samun zaman lafiya da samun ingantaccen tsaro a cikin al’ummarmu. Don haka, don Allah, don girman Allah, don kauna da soyayyar da muke yiwa fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW), ina kira da mu kawar da maganar siyasa, musamman a wannan al’amari na tsaro da ya addabi wannan al’ummah ta mu.
Mun sani cewa, kowa yana da jam’iyyarsa ta siyasa, kuma kowa yana da wanda yake so kuma yake kauna a gidan siyasa, saboda irin kyautatawar da yake gani yake yi masa, ko kuma wani kokari da yaga yana yi a cikin al’ummah. Mu sani, ba wanda za’a hana wannan. Amma idan an zo maganar maslahar al’ummah, ko samar da zaman lafiya da ci gaba, to anan ya kamata, ko ma ace ya zama wajibi, mu kalli al’ummarmu a farkon lamari.
Mu sani cewa fa duk abunda muke yi Allah Subhanahu wa Ta’ala yana kallon mu.
Don haka don Allah, mu zama masu fadin alkhairi ko muyi shiru.
Hadisi ya tabbata daga Manzon Allah (SAW) Daga Abu Hurairah – Allah ya yarda da shi – zuwa ga Annabi (SAW) yace:
“Duk wanda yayi imani da Allah da ranar lahira to ya fadi alkhairi ko yayi shiru. Kuma duk wanda yayi imani da Allah da ranar lahira to ya girmama makwabcinsa. Kuma duk wanda yayi imani da Allah da ranar lahira to ya girmama bakonsa.” [Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi]
‘Yan uwa masu girma! Daga cikin manyan abubuwan da wannan Hadisi na Manzon Allah (SAW) yake karantar da mu shine cewa, in dai har mu Musulman kwarai ne, in dai har mu muminan gaskiya ne, in dai har mun yi imani da Allah da ranar lahira, imani na gaskiya bana karya ba, to mu fadi alkairi a cikin ko wane al’amari da ya shafi rayuwar mu, idan ba zamu iya fadin alkhairi ba kuwa, to sai muyi shiru, shi yafi zamar muna alkhairi.
Domin babu wani abu da mutum zai furta face sai an rubuta shi wallahi. Kuma ko wanne daga cikinmu akwai mala’iku, masu rubutu a tare da shi, suna rubuta duk abunda ya aikata ko ya fadi.
Don haka ya zama dole kuma wajibi mu kiyaye harsunanmu kuma mu kiyaye bakunan mu.
Domin ita siyasa fa ba hauka bace, kuma ba jahilci bane. Kuma shi Musulmi ya kamata ya sani, kuma ya tuna cewa, duk abunda zai yi a rayuwarsa, ya tuna shi Musulmi ne, kuma addini yana da ta cewa a cikin dukkanin rayuwarsa. Kuma duk Musulmin kwarai addini shine zai jagorance shi a duk abunda zai yi.
Kar mu zo muyi ta sakin baki, muna fadin abunda muka ga dama, da sunan siyasa ko adawar siyasa, mu manta da Allah, mu manta da addininmu.
Domin daga karshe dai, wallahi duk zamu mutu, zamu koma ga Allah Mahaliccinmu, mai kowa mai komai. Kuma yayi muna hisabi, yayi muna sakamako a dukkan abubuwan da muka fadi ko muka aikata.
Don haka ya zama tilas mu kiyaye.
A cikin sha’anin harkar tsaron nan ya zama wajibi mu bayar da dukkan gudunmawar da zamu iya bayar wa, kai ko da ta addu’a ce, domin a samu nasara.
Kuma kar mu kushe ma kowa. Domin babu dadi mutum yaga cewa yana iyakar kokarinsa, amma maimakon a yaba masa, sai ayi ta kushe masa. Wannan babu kyau, kuma wallahi ba halin mutanen kirki bane.
Su mutanen kirki har Cullen kokarinsu shine, su bayar da gudummawa a gina ba a rusa ba.
Tun daga Shugaban kasa, har Gwamnoni, har ministoci, har Shugabannin kananan hukumomi, har Jami’an tsaron mu dukkansu, ya zama wajibi mu taya su da addu’o’i da fatan alkhairi. Dukkanisu kowa yana iya kokarinsa, kuma kowa da irin gudummawar da yake bayar wa a cikin wannan matsala ta tsaro.
Kuma su ma a gaskiya in dai har da gaske suke yi, to ya zama dole su ji tsoron Allah, su hada kan su, domin Allah ya taimakesu.
Daga karshe, ina addu’a da rokon Allah Subhanahu wa Ta’ala ya tausaya muna, ya dubi kukanmu, ya jikanmu, ya azurta mu da tsaro, ya azurta mu da zaman lafiya, ya azurta mu da kwanciyar hankali, da ci gaba mai dorewa, a jihar mu ta Zamfara, da ma dukkanin jihohin Najeriya, da Najeriyar baki daya, amin.
Wassalamu alaikum,
Dan uwanku: Imam Murtadha Muhammad Gusau ne ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi Najeriya. Za’a iya samunsa a lambar waya kamar haka: 08038289761.