Ilimi shi ne ginshikin rayuwa da ake bukata domin girma, daukaka ko ci gaban mutum, al’umma, hukuma, ko kuma kasa. Yana ba da babbar gudunmawa ta bangaren zamantakewa, tattalin arziki, ci gaban fasahar al’umma. Idan kuma aka yi la’akari da Nijeriya ana yi wa ilimi kallon a matsayin wani abu da ake amfani da shi wajen yin gyaran wasu wuraren da ake yi kallon akwai matsaloli idan aka yi maganinsu dukkan al’amura a bangarorin za su tafi kamar yadda ya dace.
Kasancewa a matsayin Malamain makaranta a halin da ake ciki yanzu ya sha bamban da yadda aikin koyarwa yake a shekarun da suka gabata, al’amarin ilimi ya dauki wani sabon babbi daga yadda aka san shi a baya, hakan kuma shi ne yasa abubuwa suka kasance akwai matsala da sa kyama ga wadanda suke fatan daukar aikin koyarwa a matsayin wani aiki ne da yake da daraja ko kima a Nijeriya.
- Gwamnatin Tarayya Ta Kara Karbo Bashin Dala Biliyan 3.45 Daga Bankin Duniya
- Kuskure Ne A Ɗauka RARARA Ba Kowan Komi Ba Ne – Farfesa Malumfashi
Aikin koyarwa ana iya yi ma shi Kallon shi ne matakalar da ake amfani da ita wajen koyawa dalibai ’yan makaranta shi ilimin ta hanyar amfani da dabarun da suka dace.Aiki ko sana’ar koyarwar ce ta samar da sauran kwararru ta ayyukan da suke yi, yadda al’umma suke bunkas ko ci gaban ya danganta ne ga irin hazikan Malaman da suka daukar ma ransu za su yi aikin koyarwa.Wannan kuwa ba tare da sun yi la’akari da irin rikon sakainar kashin da ake yi wa Malaman Makaranta da aikin na sun a koyarwa ba,
Ba kamar yadda wasu suke tunani ko Kallon al’amarin ba domi kuwa aikin koyarwa ya wuce shiga cikin aji, rike alli, da kuma bayar da umarni ba, abin ya yi daidai da sanin makamar da yadda za a sayar da labari ga wanda ya shirya sayn shi, sai shi a matsyin shi na Malami ya san hanya mafi dacewa yadda zai tsara labarin hanyar mafi dacewa,ta yadda shi mai son sayen za iyi na’ama abubuwan da labarin ya kunsa.Idan har ya yi hakan abin ba tsaya kan yana bada umarni bane da wasu bayanai, ko ilimi a zukatan dalibai ba wanda abin zai masu amfani duk tsawon rayuwarsu.
Aikin koyarwa wani abu ne da ake yi ma Kallon da akwai kima da ganin darajar masu yin shi ne da haka ne kuma ake yi ma sana’ar kallo har ila yau na mafarin dukkan wadansu ayyuka na kwararru da Malamai ana ganin kimar tasu ne saboda irin dabarar da suke da ita ta koyar da ilimi.
Koyarwa a matsayin aiki wata sana’a ce ko aikin da yake tabbatar da isar da sakun da ake son a sani ko ayyukan da suka kamata saboda dorewar mutane da kuma inda suke.Irin wadannan ayyukan sai da ilimi ake gudanar da su na yadda za ayi maganin matsala ko matsalolin da za a iya fuskanta da ba kasafai akn hadu da su ba,wata kwarewa ce da ke cikin aikin na koyarwa saboda dorewar al’umma.
Yayin da ake samun ci gaban al’amura hakanan ma yadda ake aiwatar da aikin koyarwa da yadda yake a tsarin ilimi na Nijeriya, sai wasu sabbin matsaloli suka bayyana da suke fuskantar aikin koyarwa a Nijeriya wadanda suka hada da: