Shafi ne da ke zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi Al’umma, ciki sun hadar da; Zamantakewar Aure, Rayuwar yau da kullum, Rayuwar Matasa, Soyayya, da dai sauransu. Kamar kowanne mako shafin na tafe da wasu batutuwan, inda tsokacinmu na yau zai magana game da matsalolin da suke faruwa tsakanin mata masu aiki da kuma mazajensu. Inda muka ji ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin game da wannan batu; Ko me yake janyo matsalolin da suke faruwa?, Ta wacce hanya za a magance matsalar?.
Ga dai bayanan nasu kamar haka;
Sunana Aminu Adamu, Malam Madori A Jihar Jigawa:
To magana ta gaskiya matsalolin suna da dama dake faruwa a tsakanin mata masu aiki da mazajen, domin na farko dai mazajen basa samun cikakkiyar kulawa kama daga girki akan lokaci, tsaftacce gida, tarbiyyar yara dama samun lokaci a zauna da juna domin tattaunawa, wadanan kadan ne daga ciki, wanda a lokuta da dama irin wadannan matsalolin suke kawo rashin fahimta a tsakanin ma’auratan. To abubuwan dake jawo wadannan matsalolin suna shagaltuwa da aikin da a lokuta da dama mata masu aiki suke, su fifita matsayin aikinsu a sama da komai, har suna ikirarin za su iya rabuwa da komai ko kowa akan aikinsu, domin suna ganin kamar sun mallaki komai a rayuwa wannan na daga cikin abubuwan dake jawo matsalolin a tsakanin ma’auratan. To magana ta gaskiya magance wannan matsala abu ne mai sauki muddun aka samu fahimtar juna a tsakanin ma’auratan, ta haka ne kowa zai rinka hakuri da kowa kuma kowa zai kokari wajen ganin ya sauke nauyin daya ke kansa, ka ga sai a samu cikakken zaman lafiya a tsakaninsu sai dai abun da ba a rasa ba. To shawara ta farko ita ce; su yi kokari su samu fahimtar juna a tsakaninsu ta yadda kowa zai yi iya kokarinsa wajen sauke nauyin daya ke kansa da kuma bawa juna kulawar data dace, da kuma taimakon juna har ta fuskar aikin, sai kuma su yi kokari su kaucewa ‘yan gulma da munafikai domin a wasu lokuta da dama suke shiga da fita wajen haddasa fitina a tsakaninsu.
Sunana Fadila Lamido, Daga Jihar Kaduna:
A nawa tunanin yanzu ba a cika samun matsala akan zuwa aikin matar aure ba kamar baya, mazaje da yawa sun fahimci aikin taimako ne gare su koda ace suna iya ciyar da iyalin, aikin na taimaka wa mazaje ta wasu bangarorin, abin da zai iya haddasa matsala akan zuwa aikin matar aure akwai rashin kamun kai na ita matar na farko kenan, na biyu akwai rashin sauke hakkokin da ke kanta na gida dana yaransu, shawarata ga maza tun farko idan ka san matar da za ka aura ba tada nutsuwar da za ka barta ta je aiki ka hakura da aurenta, musamman idan ta yi karatu sosai.
Sunana Sulaiman Kabiru Bununu, A Jihar Bauchi:
Wato a gaskiya matsalar da yake faruwa tsakanin ma’aurata musammanma ta bangaren macen da take aiki; Shi namiji gani yake shi ne a sama saboda shi ne ya aurota ganin futarta ya yi yawa shi ne da kaucewa wasu umarnisa to wannan shi zai sa wasu matsaloli suke kunnowa a tsakanin wadannan ma’aurata. Wato gaskiya abun da ke janyo wadannan matsaloli shi ne dai, amma fa a nawa mahangar ita ce; yawan bin shawarar abokai da kuama sa zargi wannan kenan, sai kuma kaucewa bin umarnin miji. Ta hanyar da za a magance wannan matsalar shi ne tun farko in har ka san ba za ka iya hakuri da yanayin yadda take fita aiki kobkuma yadda take gudanar da al’amuranta da wasu a waje ba to tun farko gara ka ce mata gaskiya kai ba za ta fita aiki ba, sai dai tayi zaman aurenta dan gudun samun matsala irin haka. Shawarar shi ne kawai su kasance masu hakuri da junansu da kuma rikon amana a tsakaninsu.
Sunana Rahama Musa (Mama), Dan Zomo Sule Tankarkar A Jihar Jigawa:
Gaskiya ne akwai matsaloli masu yawa kamar wajen kula da miji da kuma tarbiyyar yara a bangaren kula da miji; ya kamata mace ta sani wannan mijin nata sh ine samun farin cikin aikinta saboda da bai amince ba ba za ta yi ba. Kuma idan muka koma shari’ar musulunci aljannarsa tana karkashin kafafunsa shi mijin na ta. To akwai kula da tsaftar gida gaskiya mace ba tada hujjar yin kanzata saboda ita ma’aikaciya ce, hasali ma sai dai idan dama can ma kazamar ce saboda ko wanne irin aiki ki ke yi akwai lokacin zuwansa da kuma lokacin tashi dan haka sai ki duba misali; malamar makaranta za ta je wurin aiki 8am ta tashi 2pm to kin ga wannan kamata yayi idan tayi sallah kar ta koma bacci sai ta fara aikin gyara gidanta da kuma dora girki idan tana da kayan abincinta ma a gida har girkin rana ma za ta iya yi kafin karfe takwas yayi in sha Allah, Allah ya kara hada kan mata da mazajensu ya kuma kara saukar da albarka a tsakaninsu, don Alfarmar Annabin rahama.
Sunana Hafsat Sa’eed, Daga Jihar Neja:
Matsalolin dake faruwa tsakanin mata masu aiki da kuma mazajensu shi ne; rashin samun lokacinsu ga matansu, rashin kula da tarbiyyar yayansu wasu kuma zargin matan. Rashim fahimta ina ganin indai za su zauna su fahimci juna to da ba za su rinka samun matsala ba. Hanyar ita ce; su zauna su fahimci junansu shi ne kawai. Shawarata garesu maza wanda matansu ke aiki shi ne; su yi hakuri domin kuwa aikin matan nasu yana taimakawa sosai.
Sunana Lawan Isma’il (Lisari), Jihar Kano Rano LGA:
Matsalolin suna da yawa amma babba daga ciki ita ce; zargi, kishi da kuma cin amana da zargi ga wasunsu. Mu tsaftace aikinmu da zuciya daya, sannan kowa yana kula da iya aikinsa duba da sun san juna a matsayinsu na ma’aurata, sannan uwa uba suna tuna cewa duk abin da suka yi Allah yana gani. Shawarata anan ita ce indai har kai namiji ya gamsu da iyalinka za ta iya kula da hakkin auren da yake kanta to ya kawar da kai a kanta, sannan ya ci gaba da tayata da addu’a. Allah kasa mu dace.
Sunana Sa’adat Tahir, Daga Jihar Bauchi:
Ko ma wadanne irin matsalolin ne suke faruwa ni a tawa fahimtar daga wajen namijin take faruwa, sabida kafin ya auri mace ai ya san wacce irin mace zai aura, kuma shi ya bata damar yin aikin, kin ga kenan ai ya san abubuwan da suke faruwa a cikin sha’anin aiki tunda shi ma dole ba za a ce baya aikin ba, abin da nake gani shi ne; kowannensu ya kasance me kyakkyawan zuciya ba tare da zargin juna ba, sabida duk abin da za a ce mace tayi toh shi ma namijin ai yanayin ninkinsa tunda duk rashin mutuncin mace muddin tanada aure sai ta rage wasu abubuwan ko dan mutuncin kanta da kuma gudun abubuwan da mutane za su rinka fada a kanta, koda mu ba mu shiga daga ciki ba amma ai muna kallon mata masu auren yadda abubuwan suke kasancewa a kansu da kuma labaran mazajen wasu daga ciki. Abin da ya sa na ce haka kuwa shi ne; su mazan ai ko a wajen aiki maza ne suke fara kula matan kowanne gurin aiki akwai hakan, mace bata zuwa wajen namiji ta ce za ta ja shi sai dai shi namijin ya ja macen, dan haka a tsarkake zuciya tare da yi wa juna nasihohi da tunatarwa sai a zauna lafiya.