• English
  • Business News
Sunday, July 20, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Matsalolin Da Ke Tattare Da Zawarci Da Rashin Yin Aure Da Wuri

by Rabi'at Sidi Bala and Sulaiman
2 hours ago
in Taskira
0
Matsalolin Da Ke Tattare Da Zawarci Da Rashin Yin Aure Da Wuri
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Shafin TASKIRA shafi ne da ya saba zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da; zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya, da dai sauransu.

Tsokacinmu na yau zai yi duba game da abin da ya shafi; zawarci da kuma rashin yin aure da wuri, duba da irin matsalolin da wasu matan ke fuskanta game da abin da ya shafi hakan. Da yawan wasu mutanen ba su da tawakkali na ganin ba su yi aure da wuri ba, ko kuma wani abu ya kasance a rayuwarsu, haka kuma wasu na jahiltar zawarci ta yadda suke yi wa zawarawa kallon ba su zauna a dakunansu ba, wasu ma a takura musu in an zo aure a hana su, mutane ba sa fadar alkhairi a kan zawarci, sanadiyyar hakan ke sa wa har ta kai ga an jefa wasu cikin yanayi mara kyau, kamar; fadawa yaho, shaye-shaye da sauransu. Haka su ma wadanda suka dade ba su yi aure da wuri ba har suka kai wasu shekaru, ana jahiltar zamansu a cikin gida, har a rika ganin cewa idan ba su yi aure ba kamar wadanda suke cikin gidan aure sun fi su kwanciyar hankali, kuma sun fi su rahama gurin ubangiji.

Dalilin hakan ya sa wannan shafi jin ta bakin wasu daga cikin mabiyansa game da wannan batu; “Ko ne za a ce a kan hakan, kuma me ya sa ake jahiltar su, Ko akwai wasu matsaloli wadanda su zawarawan ko wadanda suka dade ba su yi aure ba suke da shi, wanda yake janyo musu kalubale a wajen al’umma ko kuma cikin gida, wanda su kansu ba su sani ba?, Yawan takurawa ko rashin tawakkali ga zawarawa ko wadanda suka dade ba su yi aure ba, me zai iya haifar musu?, Ta wacce hanya ya kamata al’umma ta gyara irin wadannan matsaloli na takura da jahiltar zawarci da kuma rashin yin aure da wuri?” Ga dai bayanan nasu kamar haka:

Sunana Princess Fatima Mazadu Gomben Njeriya:

Wannan abu yana yi min ciwo sosai duk yadda dan’adam ya kai ga damuwa da rashin auren wasu to, su marasa auren ko zawarawan sun fi ka jin zafi, ko dan saboda ya zamo cikekken dan’adam Mai iyalai da kwanciyar hankali. Gaskiya wannan jahilci ne babba, ai ubangiji ke tsarawa dan’adam rayuwar sa ba kai da aka halicce ku tare ba, ko ka ji ana cewa babba ce in ke bazawarace akan wacce take da dakin aure, ai a hankalce ita ce babba tunda Allah ya darajata tanata kara wayewa zaman aure, dole bazawara ita karama ce ko da kuwa ta kai shekaru 40 da dauri, haka budurwar ko saurayin da Allah bai ba su ikon yi da wuri ba, addua za a bi su da shi ba tsegumi ba. Eh! ba za ka ce babu ba, dan kowa da nashi illar ta fannin zawarci da ‘yan mataka, wasu kaddar su ta auren mazaje auri saki ne, wasu kuma rashin hakuri, inda wasu kuma fitinan iyayen miji ko dangi, zugar kawaya da sauransu. ‘yan mata kuma buri da hangen nesa, wasu kuma tasu kaddarar ce ta zo a haka, wasu kuma akan danganta da boyayyar jinya. Ya kan iya haifar musu da munanan dabiu, kamar sata, Zina, Yaho, Dillancin kwayoyi da sauransu. Wasu kuma ko shekaru dubu za su yi ba aure za ka gansu tsab suna kame da kansu saboda sun san Allah ke komai ba bawa ba, shi bawa iyakar sa magana amma bai isa ya canza maka kaddararka ba.

Labarai Masu Nasaba

Shirye-shiryen Bukukuwan karamar Sallah

Muhimmancin Karfafa Iyali Wajen Sadaka A Watan Ramadan

 

Sunana Hussy Saniey, daga Katsina:

Rashin cikakken tauhidi ne ke sanyawa ake jahiltarsu domin rashinsa kawai zai ba mai jahiltar damar ganin kamar wancan din ba yana tafiya ba ne, a bisa zanen kaddararsa ba. Babu wasu matsaloli da suke da shi sai dai na farko, mutane na yi wa budurwar da ta dade ba ta yi aure ba kallon ta tsaya ruwan ido ne har ma wasu na ganin mai kudi take jira, na biyu; zawarawa kuma ana ganin rashin hakuri ne ke fiddo su daga gidajensu bayan duk ba haka ba ne, a rayuwa duk wanda inuwar gemu ta yi wa dadi baran makogwaro ne, abin nufi duk wanda zai so ka yi aure bai kai ka ba domin in ma dadi ne kai ne za ka sha ba wancan ba. Zai iya haifar masu da matsaloli masu yawa ciki har da sanyawa su karbe duk namijin da ya zo masu wanda za a yi nadama. Hanyar gyaran daya a jawo su a jiki a ji miye matsalar su, sannan a taimaka masu da shawarwari a daina nuna masu kyara da hantara. Su yi hakuri su dage da addu’a Ubangiji yana sane da su zai kawo masu mafita, su kuma al’umma su yi hakuri su daina kyarar su, domin ba laifinsu ba ne kaddarar su ce a haka, ba za su iya yi wa kansu abin da Allah bai masu ba.

 

Sunana Khadija Auwal Koki Jihar Kano:

Abu na farko dai rashin tawakkali ne da kuma rashin yadda da kaddara da kuma karancin ilimin addini da kuma rashin yadda da kaddara. Gaskiya wasu ba su da matsaloli wasu kuma suna da su, wasu suna amfani da zawarcinsu wajen ganin sun samu abun duniya a waje, musamman wanda ba sa samu a gidajensu da suka fito ba, haka ma wadanda ba su yi aure ba ba su da lefi wasu ne ke ganin lefinsu suna ganin kamar sun ki aure alhalin ba laifin su ba ne. Hakan zai haifar da babbar matsala domin kuwa ana sa su a cikin damuwa ana ganin kamar sun ki aure bacin kuma lokacin su ne bai yi ba. Ya kamata al’umma su sani cewa komai yanada lokaci kuma komai yanada tasa jarabawar ba jahiltar su ya kamata ana yi ba addu’a za a dinga yi musu akan su ma Allah ya yanke musu domin komai lokacin ba zai yi aure ba har sai lokacin ya yi. Shawara ita ce su yi hakuri kuma su kiyaye mutuncinsu ako’ina kuma su yi ta addu’a Allah zai kawo mafita.

 

Sunana Aisha T. Bello, daga Jihar Kaduna:

Gaskiya wasu ke ja ma wasu, wata mugun hali ke fito da ita wata kuma daga mijin ne ba ta yi sa’a ba, sai mutane su yi ta hantarar ta saboda ba su san abun da ya fito da ita ba. Gaskiya da akwai da zaran mace ta kai minzalin aure ba ta yi ba iyaye su saka ta gaba sai kuma al’umma su ma da nasu, haka kuma bazawara matsala daga gun iyaye sai al’umma su ma da nasu. Yawan takura, zai janyo auren nadama kuma da da-na-sa-ni. Ni ta guna shi ne kada mu zauna muna jahilta mu yi masu adu’a shi ne kawai, saboda kai in bai faru da kai ba cikin ‘yan’uwanka ya faru da wani. Shawara ta shi ne ga wanda ba su yi aure da wuri ba, komai lokaci ne da lokaci ya yi in sha Allah za ki aure in sha Allah, haka ita ma bazawara. Su kuma al’umma su daina jahiltar su bayin kansu bane Allah muna rokon ka duk macen da ta dade ba ta yi aure ba Allah ya bata miji na gari ya Allah.

 

Sunana Hafsat Sa’eed Jihar Naija:

Shi aure rai ne da shi duk yadda ka so da zama da shi idan Allah bai yi za ka zauna ba, babu yadda za ka yi dole sai ka fita. Ga wanda kuma Allah bai sa ya yi aure da wuri ba Allah ne bai kawo masa mijin ba, tunda shi ma ba zai so a ce ya wuce zaman gida ba tare da ya yi aure ba, ina tunanin duk wannan lamari ne na Allah da mutane da suke jahilta bai kamata ba, saboda komai kaddararre ne.

 

Sunana Comr. Ibrahim Lawan Stk, Sule Tankarkar Jihar Jigawa:

Mafi akasarin mutane musamman mata a wasu lokutan sukan kasancewa mararsa tawakkali ganin sun kasance ba su yi aure da wuri ba, sakamakon ganin cewa tuni kawayensu sun jima a gidajen mazajensu a inda wasu ma hadda yaransu sannan ba komai bane yake kawo hakan face ganin cewa mutane da dama za su ke musu wani irin kallo daban-daban a inda wata za take ganin ko tana da wani aibu ne da ba ta san da shi ba, kode a ahalinta tuni iri-iri da sake-sake mararsa kyau, sannan wasu mutane naganin cewa mata sun fito daga dakunan mazajensu ne sun zama zawarawa domin rashin samun wata biyan bukata ta iyu a rayuwar zamantakewar aure ta yau da gobe ta iyu kuma ta wani bangaren ne a inda wasu ke ganin cewa duk macen da take zawarci to kamar tana tallata kanta ne a kasuwa, domin samun kudi ko wata biyan bukata ta ta ta musamman hakan ya sa mutane da yawa ke kallon lamarin ta wata fuska daban. Ta iyu akwai ta iyu kuma babu kawai lokaci ne bai yi ba, Allah bai kawo ba, amma a wasu lokutan akan alakanta hakan da asali, tarbiyya da kuma halin da mace ta tsinci kanta na mu’amular yau da gobe a cikin mutane. Hakan na iya haifar da matsaloli wadanda suka hada da damuwa da rashin farin ciki tare da walwala da kuma fadawa yawace-yawace da kuma tare da neman maza domin samun biyan bukatar kai da kuma samun kudi don biyan bukatar yau da kullum. Ta hanyar fadakar wa da wayar da kai na mutane tare da fahimtar da su abubuwa da addini ya zo da shi wanda ya jibanci lamarin aure.

 

Sunana Anas Bin Malik Achilafia Yankwashi A Jihar Jigawa:

Zawarci, da rashin Aure da wuri a wannan zamani yana tattare da yanayin tarbiyya da halayen da mace da kuma yadda ta dauki kanta. Domin da yawa wasu matan zawarci da ya hana su zaman Aure yana tattare da hali, da tarbiyarta, da kuma matsayin da ta dauki kanta, duk da cewa akwai wadanda su ba haka ba ne a tattare da su kawai jarrabawa ce, haka shi ma rashin yin Auren yanada alaka da yadda Mace ta dauki kanta, ko dai ta zurfafa son abin duniya, ko kuma burin irin na littafin marubuta. Kuma su yawanci mata idan suna zawarci, ko kuma sun jima ba su yi aure ba, ba su fiye kame kansu, su zauna a cikin gida tare da yawaita addu’o’i ga halin da suke ciki ba, sai su za ci yawo tare da nuna kira da dirin da Allah yai masu na hallitta su ne za su ba su mazajen Aure, ko kuma sakin fuskawa kowanne irin manemi da nuna bukatar hakan a gare su, ba tare da sun tantance halayensa ba. Wata-kila ko saboda sun matsu da su yi auren ne dan yadda a gida iyaye, ko abokai da ‘yan’uwa suka dame su da maganar wadda har idonsu ya rufe ba sa kallon tsawon rai da za su kasance da wanda suka Aure, bare su tantance nagartarsa. Ina ganin su ma iyaye da ‘yan’uwa bai kamata su matsa masu lamba ba, ko kuma dora masu laifin rashin zabar wadanda za su Aura ba, idan ya kasance tana da masu zuwa, to ai bai zama lallai ta ga wanda ya kwanta mata a rai ba, ko kuma yanada nagarta da kyawawan halayen da za ta amince da aurensa ba.

 

Sunana Ibrahim Garba Bizi Yobe Nijeriya:

Rashin fahimtar su shi ya sa ake musu kallon haka, saboda rashin sanin matsakaicin halin da suke ciki. A’a ba wata matsala sai ma sanin darajar aure da ya kara musu, amma wasu a cikinsu ba sa fahimtar aure zaman hakuri ne. Radadin aure bai cutar da su ba amma bakin jama’a sai ya cutar da su. Sai ana bi ana wayar wa mutane kai akan ba laifinsu bane. Shawara ta daya ce su ji kamar ba su ji ba, su gani kamar ba su gani ba, su cigaba da addu’a alkhairi ne.

 

Sunana Hassana Yahaya Iyayi (Maman Noor Graphics) daga Jihar Kano:

A zahirin gaskiya mutane ba sa kyautawa shi zawarci kaddara ce babu yadda za a yi mutum ya so yana zaman aurensa ya dawo gida zaman zawarci sai kaddara. Babu wani abu da suke da shi sai gaza gani irin na al’umma da sa’ido irinsu na su kawai. A gaskiya zai haifar masu da damuwa da kuma fadawa cikin halaka ta wata fuskar daban. Muta ne su kame bakinsu dan irin wannan abubuwan marasa kan gado ita kaddara ba ta wuce ta fada kan naka ‘yar ba, ato. Su yi hakuri su kara hakurin da juriya su mika lamarinsu ga Ubangiji In sha Allah! Allah na jin su kuma yana ganinsu in sha Allah! Allah zai kawo mafita mafi alheri a cikin rayuwar su.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Kamfanin Puma Zai Biya Man City Fam Biliyan 1 A Shekara 10 Domin Samar Wa Kungiyar Kayan Wasa

Next Post

Amfanin Kabewa A Jikin Mace

Related

‘Yansanda Sun Hana Hawan Sallah A Kano Saboda Tsaro
Taskira

Shirye-shiryen Bukukuwan karamar Sallah

4 months ago
Muhimmancin Karfafa Iyali Wajen Sadaka A Watan Ramadan
Taskira

Muhimmancin Karfafa Iyali Wajen Sadaka A Watan Ramadan

4 months ago
Me Ke Kawo Saurin Talaucewa Bayan Kammala Aikin Gwamnati?
Taskira

Me Ke Kawo Saurin Talaucewa Bayan Kammala Aikin Gwamnati?

5 months ago
Maganin Zubewar Mama Da Yadda Ake Gyara Shi 
Taskira

Yadda Mata Ke Daukar Yara Don Taya Su Aikin Gida

7 months ago
Yawaitar Ambaliyar Ruwa: Ina Mafita?
Taskira

Yawaitar Ambaliyar Ruwa: Ina Mafita?

10 months ago
Me Ya Fi Ci Wa Samari Da ‘Yan Mata Tuwo A Kwarya Game Da ‘Ramadan Basket’?
Taskira

Me Ya Fi Ci Wa Samari Da ‘Yan Mata Tuwo A Kwarya Game Da ‘Ramadan Basket’?

1 year ago
Next Post
Amfanin Kabewa A Jikin Mace

Amfanin Kabewa A Jikin Mace

LABARAI MASU NASABA

Bayan Shekaru 20 Yana Bacci, Yariman Saudiyya Ya Rasu

Bayan Shekaru 20 Yana Bacci, Yariman Saudiyya Ya Rasu

July 20, 2025
Amfanin Kabewa A Jikin Mace

Amfanin Kabewa A Jikin Mace

July 20, 2025
Matsalolin Da Ke Tattare Da Zawarci Da Rashin Yin Aure Da Wuri

Matsalolin Da Ke Tattare Da Zawarci Da Rashin Yin Aure Da Wuri

July 20, 2025
Kamfanin Puma Zai Biya Man City Fam Biliyan 1 A Shekara 10 Domin Samar Wa Kungiyar Kayan Wasa

Kamfanin Puma Zai Biya Man City Fam Biliyan 1 A Shekara 10 Domin Samar Wa Kungiyar Kayan Wasa

July 19, 2025
An Yi Taron Farko Na Shugabannin Matasa Na Dandalin Zaman Lafiya Da Tsaro Na Sin Da Afirka

An Yi Taron Farko Na Shugabannin Matasa Na Dandalin Zaman Lafiya Da Tsaro Na Sin Da Afirka

July 19, 2025
Yadda Donal Trump Ya Lashe Zaben Shugabancin Amurka

Putin Ya Fita Daga Raina – Trump

July 19, 2025
Kasar Sin Ta Ba Da Rahoton Samun Ci Gaban Aikin Gona Mara Gurbata Muhalli Ba Tare Da Tangarda Ba

Kasar Sin Ta Ba Da Rahoton Samun Ci Gaban Aikin Gona Mara Gurbata Muhalli Ba Tare Da Tangarda Ba

July 19, 2025
Dole Mu Hada Kai Da ‘Yan Siyasa Don Ciyar Da Masana’antar Kannywood Gaba -Shugaban MOPPAN

Dole Mu Hada Kai Da ‘Yan Siyasa Don Ciyar Da Masana’antar Kannywood Gaba -Shugaban MOPPAN

July 19, 2025
Xia Xueying: Muna Sayo Kashi 90% Na Kayan Aikinmu Daga Kasar Sin

Xia Xueying: Muna Sayo Kashi 90% Na Kayan Aikinmu Daga Kasar Sin

July 19, 2025
Lamine Yamal Na Fuskantar Bincike Kan Bikin Zagayowar Ranar Haihuwarsa A Spain

Lamine Yamal Na Fuskantar Bincike Kan Bikin Zagayowar Ranar Haihuwarsa A Spain

July 19, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.