Kamar yadda alkalumma suka nuna daga Hukumar Kula da Al’amuran Jami’o’i ta Kasa, akwai jami’o’i 10 na gwamnatin tarayya, da 22 na Jihohi, sai kuma 58 na masu zaman kansu da aka kirkiro tun daga 2015 zuwa yanzu.
Wasu na ganin wannan wata dama ce ta samun ilimin jami’a, da suke da zabin wadda za su tafi, yayin da wasu kuma na ganin ya dace ya dace a samar masu da duk abubuwan da suke bukata domin ba dalibai su samu ingantaccen ilimi ba ma kamar Jami’oin Jihohi da na gwamnatin tarayya.
- Kotu Ta Tsare Mutane 29 Masu Rajin Kafa Kasar Yarbawa A Oyo
- Mun Ceto Sama Da Mutane 1000 Ba Tare Da Biyan Kudin Fansa Ba – Ribadu
Abin bai ma tsaya kan kudaden da za a tafiyar da jami’o’in ba. Masu fashin baki sun ce har ma akwai sauran matsaloli musamman ma ta bangaren kwararrun malamai da suma za su zama suna da dukkan abubuwan da sauran Jami’o’in duniya ke da su.
Daya daga abubuwan da ke kawo koma-baya ga irin sabbin jami’o’in shi ne, irin Ilimin da suka samu a jami’o’in tamkar koma-baya ne ga sauran Jami’o’in da aka kafa kafin su, yadda ake tsammanin wadanda suka kammala Jami’o’i akwai banbanci mai nisa tsakaninsu.
Ba tare da isassun kudade ba, lamarin fasaha, da samun taimako, yawancin Jami’o’i masu zaman kansu suna ta kokarin yadda za su ci gaba da kasancewa a matsayinsu, zai yi wuya su samar da ingantaccen Ilimi wanda dalibai suke sa ran samu domin abin nasu aiki ne ja.
Binciken da Jaridar Guardian ta yi ya nuna cewa bayan rashin kudade yawancin jami’o’in ba su da dalibai da yawa, ba abubuwan da za su taimaka wajen koyarwar, domin babu kwararrun malaman da za su koyar.
Bamidele ya ce a Jami’ar Ilimi, Kimiyya da Fasaha ta Olumilua Jihar Ekiti, dalibai suna kokari ne wajen taimaka wa kansu wajen samun ilimi tun da jami’ar ba ta da isassun abubuwan da za su taimaka wajen samun ingantaccen Ilimin, sai kuma wani babban lamari shi ne irin yanayin da suke ciki bai dace a ce an kawo batun ilimi ba.
Da yake asalinta Jami’ar Kwalejin Ilimi ce aka daga darajarta zuwa Jami’a a shekarar 2020, abubuwan da aka gada na abin da suka shafi kayayyakin aiki ba za su wadatar ba.
Daliban sun bayyana cewa suna daukar darussa ne a dakunan lacca cikin matsi da takura domin suna da yawa ta yadda wurin ba zai iya daukar su baki daya ba.
A daya bangaren kuma malamai suna zaune ne a gidajen da ba su kamata su zauna a cikinsu ba.
Wannan duk lokacin a matsayin Kwalejin Ilimi ne babu wani abin yabo da za a fada idan ana maganar abubuwan da suke taimaka wa samar da Ilimi da za a zo a gani da suka shafi abubuwan more rayuwa, babu wurin koyon da ya amsa sunansa, babu daukar nauyin zuwa tarurruka na malamai, horar da ma’aikata da ci gabansu, ga batun bunkasa dakin karatu.
Jami’in Yada Labarai na Jami’ar Temitope Akinbisoye, ya ce babbar matsalar da take damunsu ita ce rashin kudade tafiyar da harkokinta.
“Akwai abubuwan da muke son yi amma kowane lokaci gwamnati tana ce mana kamata ya yi mu nemi wata hanya, mu kuma hanyar samun kudadenmu ba ta wuce daukar daliban da muke yi ba wajen ba su gurbin karatu.
Duk da haka kamar yadda ya kara bayani shekara uku da suka wuce lokacin da aka mai da Kwalejin zuwa Jami’a an samu ci gaba domin kuwa an ba wa dalibai 9000 guraben karatu.
A Jihar Oyo ma, lamarin duk daya ne saboda sabbin makarantu suna ta neman yadda za su ci gaba da zama a sunansu daga cikinsu akwai Jami’ar Kola Daisi Ibadan, (KDU-I), Jami’ar Precious
Cornerstone (PCU) Ibadan, Jami’ar Atiba Oyo; Jami’ar Dominion Ibadan, Jami’ar Dominican Samonda Ibadan, da dai sauransu.
Jami’o’in tuni suka fara aiki sai dai babbar matsalar da suke fuskanta rashin isassun kudaden da za su tafiyar da ayyukansu.
Matsalar kudi na ci wa Jami’oi tuwo a kwarya abin da ya hada da daukar ma’aikata da samar musu dukkan abubuwan da za su taimake su wajen gudanar da aikinsu na koyarwa da koyo, da kuma yin bincike wajen yin hakan.
Wata ganawa da aka yi da shi ba da jimawa ba, mataimakin Shugaban Jami’ar PCU, Farfesa Kola Oloke, kira ya yi ga Hukumar Kula da Ilimin Manyan Makarantu (TETFund) da ta rika sa makarantu masu zaman kansu cikin irin taimakon da take ba sauran Jami’o’i mallakar gwamnati.
Ita kuma Jami’ar KDU-I tana da fiye da dalibai 1000 masu karau a sassa daban-daban na Jami’ar.