Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana cewa ‘yan Nijeriy sun kashe dalar Amurka biliyan 2.13 wajen shigo da kayan abinci daga kasashen ketare a shekarar 2023.
A cewar rahoton kiddiga na zanga-zango da CBN ya fitar, akwai bukatu da dama da kasashen waje ke da su kan Afrika duk da cewa nahiyar na matukar fifita sayo kayan abinci daga can.
- Jami’ai Sun Yi Kira Da A Karfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Afirka Karkashin Dandalin FOCAC
- Za A Fara Rabon Takin CBN Kyauta, Sai Dai Masana Sun Ba Da Shawara
Wannan dai na zuwa ne a yayin da farashin kayayyakin abinci da ake shigo da su cikin Nijeriya ya karu zuwa babban mataki, inda ya kai har zuwa kaso 34 cikin 100 a cikin shekara guda tsakanin watan Afrilun 2023 zuwa Afrilun 2024.
Farashin kayan abinci dai ya yi tashin gwauron zabi a nahiyar Afrika sakamakon lamuran da suka shafi harkokin duniya, inda nahiyar ke kan gaba-gaba wajen shigo da kayayyaki a kasashen waje domin amfanin kai da kai.
Makuden kudaden da ake kashewa wajen sayo kayan abinci a kasashen waje na daga cikin manyan damuwowin da ke shafan tattalin arzikin Nijeriya. Kasar tana da dubban albarkatun gona, kuma akwai sa’ayin da ake ta kan yi wajen fitar da abincin gida duk a kokarin ganin an rage dogaro da shigo da kayan abinci a kasashen waje.
Sai dai, matsalolin da suka shafi na rashin kyan hanyoyi, matsalar tsaro, canjin yanayi su na taka rawa wajen dakile manufar da aka sanya a gaba na dogara da abincin gida.
Gwamnatin tarayya ta taba yin fatali da shigo da kayayyakin abinci na kasashen waje a wani matakin magance tsadar kayan abinci da kuma matsin rayuwa da al’umma suka shiga.
Tulin kudin da aka kashe wajen sayo kayan abincin kamar yadda masana suka ce, kai tsaye na nuni da cewa gwamnatin Nijeriya har yanzu ba ta dauki matakin magance matsalar yunwa da fatara zuwa shekarar 2030 ba, kamar yadda ke kunshe cikin shirin cimma muradin karni na majalisar dinkin duniya.
A shekarar 2023 kamar yadda kiddigar ya nuna, an kashe dala miliyan 245.7 wajen shigo da kayan abinci a watan Janairu, dala miliyan 163.6 a watan Fabrairu, dala miliyan 268.4 a watan Maris, dala miliyan 240.9 a watan Afrilu, dala miliyan 238.3 a watan Mayu da kuma dala miliyan 206.1 aka rasa wajen sayo kayan abinci a watan Yuni.
A watan Yuli na 2023 kuwa, babban bankin kasar nan ya ce an fitar da kudin da ya kai dala miliyan 58 wajen sayo kayan abinci kawai, dala miliyan 95.3 a watan Agusta, dala miliyan 119.9 a Satumba, dala miliyan 132.4 a Oktoba, dala miliyan 235.9 a Nuwamba da kuma dala miliyan 126.2 a watan Disamban bara.
A watan Afrilun 2024, rahoton hauhawar farashin kayan abinci da hukumar kidddiga ta kasa (NBS) ta fitr, ya karu daga kaso 15.92 cikin dari zuwa 40.53, sakamakon tashin farashin fulawa, garri, buredi, alkama, semolina, doya, mangyade, kifi, nama, hatta, kaji, mango, ayaba, kayan marmari na lambu, lipton na shayi, bombita, miliya, madara, da dai sauran nau’ikan kayan abinci.
Da yake tofa albarkacin baki kan wannan lamarin, shugaban kungiyar manoma a Nijeriya, Kabir Ibrahim, ya ce a halin da ake ciki duk da wannan adadin kudin da aka kashe wajen shigo da kayayyakin, ba wai an amincewa da a shigo da kowani irin kaya ba ne.
Ya ce, tabbas za a iya samun karuwar adadin a wannan shekarar sakamakon kara dogara da ake yi wajen sayo kayan abinci daga kasashen waje.
Kabir ya nuna cewa a shekarun da aka hana shigo da kayan abinci daga kasashen waje ba a kashe wadannan makuden kudaden ba, amma yanzu an dauko hanyar ci gaba da salwatar da makuden kudade domin shigo da kayan abincin kasashen waje.
Ya nuna cewa idan da za a maida hankali kan kayan abicin da ake nomawa a cikin gida, zai kawo karshen matsaloli da dama.