‘Yan Nijeriya sun fara azumin wata Ramadana a bana cikin matsanancin rashin wutar lantarki a daidai lokacin da ake fuskantar matukar zafi a kasar.
Da ma dai kasar ta dade tana fama da matsalar wadatacciyar wutar lantarki, sai dai bayanan sun nuna cewa a wannan lokaci rashin wutar lantarkin ya yi matukar karuwa.
- Ci Gaban Kasar Sin Na Ingiza Bunkasar Tattalin Arzikin Duniya
- Mun Gano Famfo 5,570 Da Ake Amfani Da Su Wajen Satar Danyen Mai — NNPCL
A wannan karon dai, gwamnatin Nijeriya ta dora alhakkin karancin wutar lantarkin kan rashin isasshiyar iskar gas. Abin da ya sa ko a watan jiya ma’aikatar wutar lantarkin tare da hadin gwiwar ma’aikatar albarkatun man fetur na kasar nan suka kafa wani kwamiti domin ya lalubo hanyar magance karancin gas da kamfanonin samar da wutar lantarki ke fama da shi.
Sannan a daya bangaren kuma, akwai matsalar lalata manyan turakun wutar lantarki wanda ake zargin wasu bata-gari suna yi. Na baya-bayan nan shi ne na lalacewar babban layin wutar lantarki na Shiroro zuwa Katampe kamar yadda babbar jami’ar hulda da jama’a ta kamfanin rarraba wutar lantarki (TCN), Ndidi Mbah ta bayyana.
Misis Mbah ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya cewa, wannan ne karon na biyar da ake samun irin wannan matsalar ta katsewar babban layin wutar lantarki tsakanin watan Fabrairu zuwa Maris.
Sai dai shugaban kamfanin SkyMark Energy and Power Ltd, Muhammad Sale Hassan, sannan ya kasance mai sharhi kan harkokin makamashi yana ganin cewa wannan laifin na kamfanoni masu zaman kansu ne (Discos), wadanda suke rarraba wutar lantarki.
Ya ce kamfanonin ba su da kwarewa da isasshen karfin jari da za su iya ci gaba da gudanar da aikin rarraba wutar lantarki. Sai dai kamfanonin sun sha musanta irin wadannan zargi da ake musu.
Mai sharhin ya ce suna samun matsala ne a bargaren rarraba wutar lantarki, amma ba a bangaren samar da ita ba.
Ko a makon jiya ma, ministan wutar lantarki na Nijeriya, Bayo Adelabu ya yi barazanar kwace lasisin kamfanonin rarraba wutar lantarki na kasar nan, saboda yawan dauke-dauken wutan da ake yi. Yana mai cewa ba za a lamunci yanayin da suke saka mutane na karancin wutar lantarki ba a fadin kasar nan.
Sai dai masana na ganin cewa dole ne gwamnatin Nijeriya ta shafa wa fuskarta toka idan tana so ta kawo karshen matsalar wutar lantarki, domin kuwa da wahala muradinta na samar da ci gaba a kasar ya cika muddin ba a samar da isasshen hasken wutar lantarki ba.