Kamar yadda muka sani, kasashe daban daban na da mahanga da kuma manufofi na diflomasiyya da na raya kasa, da ma wadanda suke aiwatarwa domin ba da gudummawa ga ci gaban duniya baki daya.
A bangaren kasar Sin, mahukuntanta sun jima suna jaddada burin kasar na ci gaba da aiki tare da dukkanin sassa, wajen tattaunawa, da musayar ra’ayoyi game da batutuwan da suka shafi tsaron duniya a dukkanin fannoni. Kasar Sin na fatan yin hadin gwiwa mai ma’ana tare da dukkanin kasashen duniya, domin cimma burin samar da tsaron duniya na bai daya, kuma mai dorewa. Kana tana adawa da duk wani mataki na kafa gungun rukunonin kasashe domin mayar da wasu sassa saniyar ware, kasancewar hakan na iya haifar da rarrabuwar kawuna da ingiza fito-na-fito.
- Kasar Sin Za Ta Kafa Tsarin Ba Da Agajin Gaggawa Na Yau Da Kullum Don Inganta Sakamakon Kawar Da Kangin Talauci
- Xi Ya Sha Alwashin Hadin Gwiwa Da Shugaban Jamhuriyar Congo
Hakan ne ma ya sanya a shekarar bara, yayin taron dandalin Xiangshan karo na 10 da ya gudana a birnin Beijing, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Nong Rong, ya gabatar da makala mai taken “Hadin gwiwa domin aiwatar da manufar wanzar da tsaron duniya don tabbatar da zaman lafiya da tsaron kasa da kasa”. Cikin makalar Nong Rong ya taba alli game da shawarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a watan Afrilun shekarar 2022, wato shawarar nan ta bunkasa tsaron duniya, ko “Global Security Initiative” (GSI), wadda ke kunshe da dabarun da ya kamata duniya ta runguma, wajen cimma nasarar gina tsarin taimakekeniyar jin kai, da tsaro da walwalar daukacin al’ummun duniya.
Tun bayan gabatar da wannan shawara ta “GSI” ne kuma, kasashe da al’ummun sassan duniya daban daban suka rika jinjinawa hangen nesan shugaban na Sin, kuma shawarar ta samu goyon baya da amincewa daga sama da kasashe da hukumomin kasa da kasa da na shiyyoyi sama da 100, aka kuma rubuta ta cikin wasu kundin bayanan hadin gwiwa, da musaya tsakanin Sin da sassan kasashen duniya masu tarin yawa. Har ila yau, kawo wannan lokaci, ana ci gaba da samun nasarori karkashin hadin gwiwar da ake aiwatarwa bisa manufar shawarar ta GSI.
Har ila yau, game da wannan batu na burin kasar Sin na ganin duniya ta kasance cikin yanayin zaman lafiya da kwanciyar hankali, a ranar Asabar 17 ga watan nan na Fabarairu, mamban hukumar siyasa ta kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta Sin, kuma ministan wajen kasar Wang Yi, ya gabatar da jawabi mai taken “Sin ta sha alwashin zama jigon samar da daidaito a duniya mai tangal-tangal”, yayin taron tsaro na birnin Munich na kasar Jamus.
Wang Yi ya yi bitar yadda duniya ke fama da hargitsi da tashe-tashen hankula, kuma bil adam ke ci gaba da fuskantar kalubaloli daban daban, ciki har da ra’ayin ba da kariya ga kasuwanni, da kallon dukkanin matsaloli ta mahangar tsaro kadai, yanayin dke haifar da mummunan tasiri ga tattalin arzikin duniya, yayin da kuma ra’ayin kare bangare guda, da siyasar gungun bangarori ke gurgunta tsarin cudanyar sassan duniya.
Wang ya ce kasarsa ta damu da yadda rikicin Ukraine ke ci gaba da wanzuwa, baya ga rikicin Isra’ila da Falasdinu da ya ki ci ya ki cinyewa. Amma dai duk da haka, ministan wajen na Sin na ganin a matsayin Sin na babbar kasa mai dauke da babban nauyi, za ta ci gaba da gudanar da manufofinta cikin kwanciyar hankali, za ta dage wajen zama karfi mai tasirin gaske dake taka rawar gani wajen wanzar da zaman lafiya.
Kafin wannan taro na Munich ma, ministan wajen na Sin ya ziyarci kasashen arewaci da yammacin Afirka hudu, da suka hada da Masar da Tunusiya, da Togo da Ivory Coast, kuma sakon sa ga kasashen na kunshe da burin Sin na tallafawa duk wasu matakai na wanzar da zaman lafiya a sassan duniya, musamman ma muhimmin aikin nan na ganin an gaggauta shawo kan ricikin Isra’ila da Falasdinu yadda ya kamata.
Masharhanta na cewa, ziyarar Wang a wadannan kasashe na Afirka wadda ita ce ziyarar farko da ya gudanar a kasashen waje a wannan shekara ta bana, na nuni da muhimmanci da Sin din ke dorawa ga diflomasiyyar kasa da kasa, da burin Sin na ganin ta taka rawar gani a fannin wanzar da zaman lafiya da lumana, musamman la’akari da yadda minista Wang ya sanya Masar a matsayin zangonsa na farko na ziyarar da ya gudanar a Afirka, a matsayin Masar din na muhimmin jigo a siyasar gabas ta tsakiya.
A birnin Alkahiran Masar, Wang ya bayyana bukatar kiran taron tattauna batutuwan da suka shafi wanzar da zaman lafiya mai nasaba da tashin hankalin dake wakana a Gaza. Kaza lika ya jaddada bukatar nan ta kafa kasashe biyu masu cin gashin kan su, a matsayin matakin shawo kan rikicin na Isra’ila da Falasdinu.
A zahiri take cewa, baya ga batun raya alakar cinikayya da kasuwanci, da bunkasa shawarar nan ta “Ziri Daya Da Hanya Daya” mai nasaba da zuba jari domin raya ababen more rayuwa a Afirka, a hannu guda, kasar Sin ta dukufa, wajen amfani da dukkanin damar ta don cimma burin wanzar da zaman lafiya, karkashin hadin gwiwa da sauran sassan kasa da kasa, ciki har da kawayen ta kuma abokan tafiya na nahiyar Afirka
To sai dai fa duk da wannan kokari da Sin take yi na ganin sassan kasa da kasa sun yi hadin gwiwa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a dukkanin sassa, wani babban kalubale da duniya ke fuskanta shi ne yadda wasu manyan kasashen duniya masu fada a ji ke daukar wasu matakai dake mayar da hannun agogo baya.
Bahaushe kan ce “Zaman Lafiya Ya Fi Zama Dan Sarki”, kuma ita fitina na iya shafar wanda ya jawo ta da ma wanda bai ji ba bai gani ba. Don haka masharhanta da dama ke ganin kamata ya yi duniya ta dunkule wuri guda, ta rungumi tafiya daya ta tabbatar da warware rikice-kirice ta hanyar siyasa, kana manyan kasashe masu fada a ji su kauracewa yin baki biyu, ko goyon bayan bangare guda, ko yunkurin cin gajiya daga yaki, yayin da ake kara fuskantar yanayi mai hadari a sassan duniya daban daban.
Wannan mahanga dai ba ta rasa nasaba da yadda ake ganin wasu kasashen yamma, musamman Amurka na daukar matakai da har yanzu ba su kai ga samar da wata fa’ida a fannin warware rikicin da gabas ta tsakiya ke fama da shi ba.
Abu ne a fili cewa duk da kokarin da Amurka ke yi na nuna kanta a matsayin mai shiga tsakani a yankin Gabas ta Tsakiya, musamman a wannan gaba da rikici tsakanin Isra’ila da Hamas ya ki ci ya ki cinyewa, da yawa daga kasashen yankin na kallon Washington a matsayin “Kanwa Uwar Gami”, wadda shigarta batun ba abun da ya haifar sai kara dagula al’amura.
Sanin kowa ne cewa matakan soji kadai ba sa iya warware duk wani rikici, kamar yadda tarihi ya tabbatar da hakan a sassan duniya daban daban, maimakon kawo karshen tashin hankali ma, matakan soji na iya ingiza fadadar rikici. Don haka lokaci ya yi da za a komawa shawarwari domin samun mafiya ta dindindin.
Bugu da kari, duk da kalaman jami’ai daban daban daga tsagin Amurka, dake nuni ga burin kasar na ganin an shawo kan rikicin Isra’ila da Falasdinu, shaidun zahiri na nuna sabanin hakan. Ga misali, irin tallafin da Amurka ke baiwa Isra’ila ta fuskar ayyukan soji, da tura karin dakaru zuwa yankin, da ma yadda ta hau kujerar naki game da kudurin kwamitin tsaron MDD na shigar da karin agajin jin kai zuwa Gaza, sun nuna inda Amurkar ta karkata.
Hakan ne ma ya sa masu fashin baki da dama ke ganin ziyarar baya bayan nan da sakataren wajen Amurka Antony Blinken ya kai yankin Gabas ta Tsakiya ba za ta haifar da wani “da mai ido ba”, maimakon hakan ma mai yiwuwa yanayin da Falasdinawa ke ciki a Gaza da kewaye ya kara tabarbarewa.
Wannan mummunan yanayi na jin kai da ake fuskanta a Gaza, ya ma sanya wasu kawayen Amurka na nahiyar Turai fara sukar yadda kasar ta mayar da Isra’ila ’yar lele. Ko da a baya bayan nan ma jaridar New York Times ta wallafa wani rahoto dake cewa, sama da jami’ai 800 daga Amurka da Birtaniya da kungiyar tarayyar Turai sun wallafa budaddiyar wasika mai kunshe da suka game da yadda gwamnatin Amurka ke goyon bayan mahukuntan Isra’ila a yakin da suke yi a Gaza.
A daya bangaren, yayin taron da aka gudanar game da tattauna batutuwan yaki da ta’addanci, a zauren kwamitin tsaron MDD na ranar Alhamis 15 ga watan nan, wakilin dindindin na kasar Sin a majalisar Zhang Jun, ya jaddada muhimmancin karfafa hadin-gwiwa domin yakar barazanar ta’addanci. Yana mai kira da a murkushe duk wani nau’i na ta’addanci, da zummar tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.
Mista Zhang ya ce, ta’azzarar rikicin Palesdinu da Isra’ila ya janyo karin munanan laifuffukan nuna kiyayya da ake aikatawa a kasashe daban-daban, tare da karuwar fuskantar barazanar hare-haren ta’addanci. Don haka mataki mafi muhimmanci a halin yanzu shi ne, a tabbatar da tsagaita bude wuta a zirin Gaza, ta yadda za a kai ga kaucewa kara tabarbarewar yanayi a yankin gabas ta tsakiya.
A bangaren nahiyar Afirka kuwa, jami’in ya ce yankin yammacin Afirka da na Sahel na fuskantar babbar barazanar hare-haren ta’addanci, kuma babban dalilin da ya sa haka shi ne karancin kwarewar aiwatar da matakan murkushe yanayin. Don haka ya zama wajibi MDD da sauran kasashen duniya su yi la’akari da bukatun kasashen Afirka, ta yadda za su kara ba su taimako.
Daga wadannan kamalai na Zhang Jun, za mu iya kara fahimtar mahanga da burin kasar Sin, cewa har kullum kasar na mai da hankali sosai ga halartar hadin-gwiwar kasa da kasa a fannin yaki da ta’addanci, da wanzar da tsaro, da zaman lafiya a dukkanin sassan duniya. Bugu da kari, a ’yan kwanakin da suka gabata, kasar Sin ta fitar da takardar bayani kan tsarin doka, da matakan yaki da ta’addanci, wadda a cikinta aka yi bitar muhimman ayyuka, gami da nasarorin da kasar ta Sin ta samu a fannin yakar ta’addanci, da kuma matakan da a nan gaba za ta ci gaba da ingantawa, ta fuskar hadin-gwiwa tare da sauran kasashe, domin aiwatar da shawarar kiyaye tsaro a duniya, wadda shugaban kasar ya gabatar.
Masharhanta dai na ganin lokaci ya yi da Amurka za ta yi karatun ta nutsu, ta yi watsi da duk wasu matakai da ka iya rura wutar tashin hankali a gabas ta tsakiya, domin kaucewa tsunduma yankin cikin karin tashin hankali da rudani. Maimakon haka, kamata ya yi kamar yadda kasar Sin ke nuna kyakkyawan misali, Amurka da sauran kasashe masu fada a ji su dunkule wuri guda, su rungumi hakikanin matakan farfado da zaman lafiya da daidaito a dukkanin sassan duniya, da kauracewa aiwatar da manufofi na kashin kai domin cin gajiyar wani bangare daya kadai.