Shugaban majalisar dokokin Sri Lanka ya bayyana cewa Shugaba Gotabaya Rajapaksa zai sauka daga mulki a ranar Laraba 13 ga watan Yuli 2022.
Wannan ya biyo bayan gagarumar zanga-zanga da aka yi tsawon rana a yau da kuma zaman tattaunawa tsakanin shugaban majalisar da firaministan kasar da kuma shugabanin jam’iyya.
- An Kashe Mutane 15 A Mashayar Giya Afrika ta Kudu
- NSCDC Ta Bankado Shirin ISWAP Na Kai Hare-Hare A Makarantu Da Cocina A Abuja
Bukatar shugaban ya sauka daga mulki dai ita ce gaba-gaba da masu zanga-zangar ke nema tsawon watanni saboda gazawar hukumomi na magance hauhawarar farashi da karancin abinci da man fetur da kuma magani.
A ranar Asabar, masu zanga-zangar suka kwace iko da gidan shugaba Rajapaksa, inda daga bisani suka cinna wa gidan firaministan kasar, Ranil Wickramasinghe wuta.
Zanga-zangar ta dauki zafi, inda da dama suka jikkata yayin arangama da jami’an tsaron kasar.