Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya bukaci al’ummar Musulmi da su kara kaimi wajen yin addu’o’i ga Allah Madaukakin Sarki da ya kawo mana zaman lafiya da ci gaba a Nijeriya da Jihar Kaduna musamman a lokutan bukukuwan Mauludi.
A cikin wata sanarwa da gwamnan ya fitar, ya taya daukacin al’ummar Musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad SAW, inda ya yi fatan gudanar da bbukukuwan Mauludin cikin lafiya da kwanciyar hankali.
- ‘Yan Fashin Daji Sun Kai Wani Sabon Hari Sun Kashe Mutum 6 A Yankin Kudancin Kaduna
- Magidanta 137,000 Sun Ci Gajiyar Rabon Kayan Abinci A Kananan Hukumomi 6 Na Jihar Yobe
Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa, bikin watan Maulud na bana wata dama ce ga al’ummar Jihar Kaduna wajen yin koyi da kyawawan dabi’un Manzon Allah SAW domin warkar da zukatan al’umma da sake gina tattalin arzikin jihar da ya tabarbare.
Ya bayyana cewa, Annabi SAW ya koyar da soyayya, hakuri, adalci, juriya da gafara.
Ya ci gaba da cewa, gwamnatinsa za ta ci gaba da karfafa hadin kai tsakanin addinatai mabanbanta da ke jihar.