Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Lazio, Maurizio Sarri yayi murabus daga aikinsa, bayan da kungiyar ta yi rashin nasara a wasanni biyar daga cikin shida na baya-bayan nan da ta yi a dukkanin gasannin da ta ke ciki.
A ranar Litinin data gabata, Lazio ta sha kashi a gida a hannun Udinese da ci 2 da 1, kari a kan fidda ta daga gasar zakarun Turai da Bayern Munich ta yi a makon da ya gabata.
- Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Kashe Fiye Da Naira Biliyan 2 Domin Ciyarwa A Watan Ramadan
- Dan Majalisar Tarayya Daga Borno Ya Tallafawa Manoma 160 Da Naira Miliyan 140 A Mazabarsa
A shekarar 2021 ne, Sarri ya karbi ragamar kungiyar, inda a kakar da ta gabata ya jagorance ta wajen karewa a mataki na biyu a kasar Serie A, mataki mafi girma da kungiyar ta taba karewa tun bayan da ta lashe gasar a kakar wasa ta shekarar 1999 zuwa 2000.
Tuni dai kungiyar da a yanzu ke mataki na tara a teburin gasar Serie A ta maye gurbinsa da mataimakinsa Giovanni Martusciello, a matsayin mai horaswa na rikon kwarya.
A baya dai Sarri ya yi aiki da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, inda ya jagorancita wajen lashe gasar Europa sannan ya kai ta wasan karshe na gasar Carabao.
Kafin nan ya yi aiki a matsayin mai horas da kungiyar Napoli, inda ya jagorance ta wajen karewa a matsayi na biyu har sau uku a gasar Serie A, kuma ya samu nasarar lashe gasar da kungiyar Juventus a shekarar 2019 zuwa 2020.