• English
  • Business News
Saturday, August 23, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Mayar Da Hankali A Aikin Farfado Da Kwararrun Asibitocin Gwamnatin Tarayyya

by Leadership Hausa
3 months ago
in Manyan Labarai
0
Mayar Da Hankali A Aikin Farfado Da Kwararrun Asibitocin Gwamnatin Tarayyya
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Bayanin da Ministan Ilimi Dakta Tunji Alausa, ya yin a cewa, Shugaban Kasa Ahmed Tinubu, ya amince da kasafin Naira biliyan 110, domin a sabunta kayan aiki a Asibitin Kwararru na Gwamnatin Tarayya18, tabbas wannan abin yabawa ne.

Dakta Tunji ya yi bayani dalla-dalla kan yadda za a yi amfani da kudin, inda ya ce, za a yi amfani da Naira biliyan 70, wajen yiwa Makarantun koyar da aikin likita don mayar da su, daidai da irin na matakin kasa da kasa.

  • Darussan Koyi Daga Salon Bunkasa Kasa Na Sin
  • Ƙungiyar ’yan Majalisar Dokokin Ƙasa Ta APC Ta Amince Da Takarar Tinubu A ZaÉ“en 2027 

Kazalika, ya sanar da cewa, za a kuma yi amfani da Naira biliyan 15, wajen domin gina sabbin dakunan kwanan dalibai.

Tunji, har ila yau, ya bayyana cewa, za a kuma bai wa jami’oin kasar, guda 76, wasu somin tabin kudade, na tafiyar da cibiyoyin lafiyarsu da kuma kara yawan gurben daukar dalibai masu son karo karatun kwarrun kiwon lafiya.

Bugu da kari, duk a cikin wannan shirin, ya hada da, kafa dakunan yin gwaje-gwaje guda takwas, inda ko wanne Asibitin kwararru na Gwamnatin Tarayya, zai samu Naira biliyan hudu, domin samar da kyakyawan yanayi na karatu, ga kwararrun kiwon lafiya, musamman domin a rage kashe kudade, zuwa tura su ketare, domin su samu horo.

Labarai Masu Nasaba

NDLEA Ta Kama Matashi Da Tabar Wiwi Ta Naira Miliyan 10 A Kano

’Yansanda Sun Kama Jagororin ‘Yan Bindiga A Abuja, Sun Ƙwato Makamai Da ₦7.4m

Matakin da Gwamnatin ta dauka, na son yin amfani da Gidauniyar TETFund, domin yin wannan aikin, babban abin jinjinawa ne, wanda idan har ba a samu wata gazawa ba, kamar a sauran ayyukan baya, musamman duba da cewa, Giduaniyar ta samu shedar cewa, ba a santa da gazawa, wajen wanzar da ayyukan da shirye-shiyen da ta sanya a gaba, kan batun ganin an inganta karatu a jami’oin kasar.

Kazalika, Ministan ya ce, daukacin aikin shi ne, domin a dakile yawan ficewar da kwararrun Likitocin kasar ne yi ne, zuwa ketere domin neman aiki, wanda hakan zai sanya, a ciki gaba da raike su a kasar nan, domin su yi aki a cikin kasar.

A karkashin aikin, za a kuma tabbatar da an samar da kayan aiki da samar da masu da karin kudade da kuma kara inganta yanayin mai kyau, da za su gudanar da ayyukansu, na duba marasa lafiya.

Alausa ya ci gaba da cewa, daukin da za a samar a fannin na kiwon lafiyar kasar, za a samar da shi ne, ga manyan bangarorin kimiyya, samar samar da magunguna da na jinya.

A cearsa, za a wanzar da wannan zuba hannun jarin ne, a fannin na zuwa shekaru biyar wanda aka kiyasta, za a kashe kudin da ya kai Naira tiriliyan 1.5 wanda za iya cimma hakan ne, ta hanyar wanzar da shiye-shiyen.

Sai dai, tun fil azala, kalubalen da kasar ke fuskanta shi ne, na Nijeriya na yin sakaci, wajen rashin wanzar da shirye-shiyen da aka dauka

Karin wani abin takaicin shi ne, fannin kiwon lafiyar kasar, musamman a kwararrun Asibitocin, sun koma tamkar abin damauwa ga ‘yan Nijeriya da kuma su kwararrun Likitocin, duba da yadda aka yi watis da ba su kulawar da ta kamata da yawan samun aikata badakalar cin hanci da rashawa, wanda hakan ya kara durkusar da fannin na kiwon lafiyar, wanda kuma hakan ya janyo, ba sanar inganciyyar kula da kiwon lafiyar da ya dace da kuma samar da ilimantar wa.

A nan za mu iya cewa, ya kamata Gwamnati baya ga samar da kayan aiki a Asibitocin, t ya kuma zama wajbi, ta zabo wasu Makarantun horas da kwararun Likitoci domin a daga darajar Makarantun.

Kwararrun Asibitocin kasar nan dai, sun jima da lalacewa da rashin ingantattun kayan aiki duba da cewa, ba su da Gadajen kwantar da marasa lafiya da suka wuce, goma kacal.

Akasarin ‘yan Nijeriya da ke bukatar a duba lafiyarsu, suna yin tururuwa zuwa kwararrun Asibitocin kasar, amma matsalar, suna shafe awowi, domin neman Gadon da za a kwantar da su don su yi jinya.

A wasu lokacin samun Asibtin, ya danganta ne da irin karfin iko da mai bukatar yake da shi.

Domin a dakile wannan matsalar, muna kira ga Gwamnati da mahukunatn irin wadannan kwararrun Asibitocin na Gwamnati, da su tabbtar da suna tattala kudaden da ake ware masu, a cikin kasafin kudin kasa, ba wai kawai batun yiwa Asibitocin garanbawul bane, amma a samar da kayan aiki na zamani, musamman mayar da hankali kan jin dadi da walwalar kwararn Likitocin.

Hakazalika, dole ne Gwamnati ta tabbatar da wanzar da samar da ingantaccen albashi, da samar da kyakyawan yanyin aikin aiki na kwararun Likitocin kasar, wanda hakan zai ba su damar samar da sakamako mai kyau, da ake bukata a fannin.

A saboda wadannan dalilan, ya zama wajibi, Gwamnatin Tarayya da rinka yin aiki kafada da kafada da kwararrun mahukuntan kiwon lafiya da sauran amsu ruwa da tsaki domin a samar da wata manhaja kan wannan aikin tare da cimma kudurin da aka sanya a gaba, kan lokaci.

Ya kamata a zuba hannun jari wajen bai wa kwararrun Likito horo domin a inganta kwarewarsu da kuma walwalarsu.

Bugu da kari, akwai bukatar a wadatar da Asibitocin kasar da kayan aiki na zamani, musamman domin a samu damar ci gaba da duba lafiyar marasa lafiya da kuma ilimantar da kwararrun Likitocin.

Ya kuma wajaba a samar da kayaan aiki na zamani da za a rinka duba manyan larorin cuttuka, kamar irinsu, Cutar Daji, wanda hakan zai sanya, masu irin wadannan larorin, ba sai sun fita zuwa Asibicin da ke ketare, domin neman lafiya ba.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Asibitoci
ShareTweetSendShare
Previous Post

‘Yan Sama Jannatin Shenzhou-20 Sun Kammala Aiki A Wajen Tashar Sararin Samaniyar Kasar Sin

Next Post

Yadda Tabarbarewar Tsaro Ta Kara Yawan Yaran Da Ba Sa Zuwa Makaranta

Related

NDLEA Ta Kama Matashi Da Tabar Wiwi Ta Naira Miliyan 10 A Kano
Manyan Labarai

NDLEA Ta Kama Matashi Da Tabar Wiwi Ta Naira Miliyan 10 A Kano

3 hours ago
Mahara Sun Kai Hari Banki A Kogi
Manyan Labarai

’Yansanda Sun Kama Jagororin ‘Yan Bindiga A Abuja, Sun Ƙwato Makamai Da ₦7.4m

22 hours ago
An San Masu ÆŠaukar Nauyin Boko Haram, Kariya Ake Ba Su – Tsohon Babban Soja
Manyan Labarai

An San Masu ÆŠaukar Nauyin Boko Haram, Kariya Ake Ba Su – Tsohon Babban Soja

1 day ago
Yawaitar Haduran Kwale-kwale A Arewa: Ina Mafita?
Manyan Labarai

Yawaitar Haduran Kwale-kwale A Arewa: Ina Mafita?

1 day ago
Gwamnatin Tinubu “Kasuwa Ce Mara Amfani Ga Talaka” – PDP
Manyan Labarai

Bukatar Farfado Da Cibiyoyin Bincike Don Bunkasa Kasa

1 day ago
EFCC Na Neman Surukin Atiku Abubakar Ruwa A Jallo
Manyan Labarai

EFCC Na Neman Surukin Atiku Abubakar Ruwa A Jallo

2 days ago
Next Post
Yadda Tabarbarewar Tsaro Ta Kara Yawan Yaran Da Ba Sa Zuwa Makaranta

Yadda Tabarbarewar Tsaro Ta Kara Yawan Yaran Da Ba Sa Zuwa Makaranta

LABARAI MASU NASABA

Shirin Ahmed Isa Na Brekete Family: Maslaha Ko Matsala?

Shirin Ahmed Isa Na Brekete Family: Maslaha Ko Matsala?

August 23, 2025
Zargin Shan Guba: ’Yan Nijeriya Biyu Sun Mutu A Libya

Zargin Shan Guba: ’Yan Nijeriya Biyu Sun Mutu A Libya

August 23, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

Yadda Wani Mai Unguwa Ya Yi Wa ‘Yar Shekara 12 Fyade A Gombe

August 23, 2025
NDLEA Ta Kama Matashi Da Tabar Wiwi Ta Naira Miliyan 10 A Kano

NDLEA Ta Kama Matashi Da Tabar Wiwi Ta Naira Miliyan 10 A Kano

August 23, 2025
Garkuwa Da Mutane: Wani Ba’indiye Da Ake Zargi Ya Nemi Shafa Wa ‘Yan Nijeriya Kashin Kaji

Garkuwa Da Mutane: Wani Ba’indiye Da Ake Zargi Ya Nemi Shafa Wa ‘Yan Nijeriya Kashin Kaji

August 23, 2025
Matasa Sun Nemi A Tura Sojoji Don Korar Ƴan Bindiga Daga Kwara

Matasa Sun Nemi A Tura Sojoji Don Korar Ƴan Bindiga Daga Kwara

August 23, 2025
Hotuna: Shettima Ya Wakilci Shugaba Tinubu Wajen Jana’izar Sarkin Zuru

Hotuna: Shettima Ya Wakilci Shugaba Tinubu Wajen Jana’izar Sarkin Zuru

August 23, 2025
Minista Ya Buƙaci Kafafen Yaɗa Labarai Da Su Guji Tallata ’Yan Ta’adda Da ’Yan Bindiga

Gwamnatin Tarayya Ta Sha Alwashin Kama Waɗanda Suka Kashe Masallata A Malumfashi 

August 23, 2025
Gwamnatin Tarayya Na Hasashen Samun Naira Biliyan 300 Kan Noman Dabino A Yobe

Gwamnatin Tarayya Na Hasashen Samun Naira Biliyan 300 Kan Noman Dabino A Yobe

August 23, 2025
Ya Zama Wajibi Nijeriya Ta Cimma Wa’adin Tura Cocoa Tarayyar Turai A Disambar 2025

Ya Zama Wajibi Nijeriya Ta Cimma Wa’adin Tura Cocoa Tarayyar Turai A Disambar 2025

August 23, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.