ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, June 22, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Tabarbarewar Tsaro Ta Kara Yawan Yaran Da Ba Sa Zuwa Makaranta

by Rabi'u Ali Indabawa
1 year ago
Tsaro

Masu ruwa da tsaki na ci gaba da nuna damuwarsu kan yara sama da miliyan 10 da ba sa zuwa makaranta a Nijeriya, inda akasarinsu ke zaune a yankin arewacin kasar.

Da yawa daga cikin wadannan yara kamar yadda bayanan LEADERSHIP suka gano, an ce an tilasta wa wadannan yara barin makaranta ne saboda tashe-tashen hankula da wasu nau’ika na rashin tsaro.

  • Za Mu Riƙe Wa Minista Tijjani Muƙaminsa Bayan Hamɓarar Da Tinubu A 2027 – El-Rufai 
  • Ƙungiyar ’yan Majalisar Dokokin Ƙasa Ta APC Ta Amince Da Takarar Tinubu A Zaɓen 2027 

‘Yan Nijeriya da dama da abin ya shafa sun ce kasar na fuskantar bala’in rashin ilimi mai cike da ban tsoro, ganin yadda aka tilasta wa miliyoyin yara barin ajujuwa ba da son ransu ba, ta hanyar ayyuka na ta’addanci, rikice-rikice, da sauran nau’ukan tashe-tashen hankula musamman a yankin Arewa.

ADVERTISEMENT

Misali, bisa binciken da aka yi, tsakanin shekarar 2012 zuwa 2016 kadai, an kashe malamai sama da 600 a lokacin da suke gudanar da aiki domin gina kasa.

Bayanai daga LEADERSHIP sun gano cewa yawancin yaran suna tsakanin shekaru biyar ne zuwa 14, kuma sama da kashi 60 cikin 100 na wadannan yara suna zaune ne a yankin Arewa maso Gabas, yankin da ke fama da tashe-tashen hankula da rashin matsugunai, da kuma tsananin talauci.

LABARAI MASU NASABA

Amurka Ta Dakatar Da Takunkumin Man Fetur Kan Iran

Ya Kamata Farashin Siminti Ya Sauka — Umahi Ga Masana’antun Siminti

Bincike ya yi nuni da cewa an bar dukkan al’ummomi ba tare da ingantattun makarantu ba a jihohi kamar Borno, Yobe, da Adamawa.

Sama da makarantu 1,500 ne aka lalata tun farkon rikicin Boko Haram, inda sama da malamai 19,000 suka rasa matsugunansu, kuma da yawa ma suna fargabar komawa.

‘Yan mata suna cikin hadari, galibi ana tilasta musu auren wuri ko aikin gida ko aikin jima’i maimakon a ba su damar koyo.

Wata kwararriyaa fannin ilimi da ke zaune a Jos, Jihar Filato, Misis Peace Pernam, ta ce, “Ilimi wata hanya ce ta rayuwa mai muhimmanci da ke kawar da fatara, rage matsalar tsaro, da samar da ci gaban kasa, duk da haka, ga miliyoyin yara a yankin Arewa maso Gabas, cikin matsanancin rikici, rashin kyakkyawan shugabanci, wadanda rashin sanya hannun jari ke yanke jin dadin rayuwarsu.

Al’amarin wadannan yaran bai tsaya kadai kididdiga ba. Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya tabbatar da abin da ba a yi tsammani ba: Nijeriya ce ta fi kowacce kasa yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a duniya. Idan ka tara uku za ka samu daya daga cikinsu ba ya zuwa makaranta, wato ba ya samun ilimin boko a halin yanzu.

“Wannan matsalar ba ta tsaya kadai ga ilimi ba, al’amari ne dake bukatar taimakon gaggawaa kasa.

Idan ba a dauki matakin gaggawa ba, Nijeriya na fuskantar afkawa hadarin kasa yin kafada da sa’anninta, wajen ci gaba sace jama’a da rashin kyakkyawar gami da kakaba wa jama’a talauci, tsatsauran ra’ayi, da rashin zaman lafiya.”

A cewar wani mai sharhi kan al’amuran jama’a, Ahmed Idris, matsalar ilimi a Nijeriya na kara ta’azzara, musamman a yankunan da ke da karancin makarantu.

Ya ce yara da yawa har yanzu suna tafiya mai nisa zuwa makaranta, idan kuma sun halarci makarantar za ka samu babu kwararrun malamai.

Wani lokaci kuma, ana samun karancin ingancin malamai.

“Rashin ingancin koyarwa ya sa dalibai ba za su iya karatu ko yin lissafi ba bayan sun shafe shekaru a makaranta, don magance wannan, dole ne gwamnati ta ba da fifiko ga Ilimi kyauta da yin amfani da fasaha don cike gibin.

Ilimi shi ne ginshikin rage talauci, aikata laifuka, da rashin aikin yi, gina hanyoyin koyar da sana’o’i da kuma samar wa ‘yan Nijeriya makoma nan gaba,” in ji shi.

Wani malami da ke zaune a Abuja, Peter Ojo, ya yi gargadin cewa Nijeriya ba za ta iya kaucewa barazanar da ke kunno kai wacce ‘yan zamani marasa ilimi ke yi ba.

A cewarsa, dangantakar ilimi da ci gaban tattalin arziki ba abu ne da za a iya musantawa ba.

Ya ce, “Ta hanyar ba da fifiko ga ilimi, kasar za ta iya canza matasanta zuwa ga samar da canji mai kyau da ci gaban kasa. Bayan haka, magance duk wata matsala ta zamantakewa ta dogon lokaci dole ne sai an bi ta hanyar ilimi.”

Ya kuma kara bayyana yadda ake fama da karancin kudade a fannin ilimi, inda kashi 7.3 cikin 100 ne kawai na kasafin kudin kasar da aka ware wa ilimi, wanda bai kai kashi 15-20 bisa 100 da hukumar UNESCO ta ba da shawarar ba.

Ya ce rashin kudi a matsayin wani muhimmin al’amari da ke taimaka wa gurbacewar ababen more rayuwa, cunkoson ajujuwa, da rashin isassun kayan koyarwa, rashin wadatar dalibai da malamai da karancin ababen more rayuwa a makarantu duk su ke haifar da wadannan matsaloli.

Sai dai ya amince da ci gaban da wasu jihohin Nijeriya suka samu a baya-bayan nan, kamar su Enugu, Jigawa, Kano, da Kaduna, wadanda suka ware sama da kashi 26 na kasafin kudinsu ga ilimi a shekarar 2025.

A ‘yan kwanakin nan, gwamnatin tarayya da na jihohi da wasu kamfanoni masu zaman kansu na kokarin ganin an shawo kan matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta a Nijeriya. A kwanakin baya, babbar sakatariyar hukumar kula da ilimin bai daya ta kasa (UBEC), Aisha Garba, ta ce hukumar za ta fadada rajista da shigar da su cikin tsarin ilimin boko domin rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a kasar nan, musamman a yankunan karkara.

Ta kuma bayyana cewa galibin yaran da ba sa zuwa makaranta suna zaune ne a yankunan karkara kuma aksarinsu ‘ya’yan talakawa ne, inda rashin daidaiton tattalin arziki ke haifar da fatara a gidaje da dama.

Ta kuma jaddada bukatar kara bayar da shawarwari don magance muhimman kalubalen ilimi a Nijeriya.

Har ila yau, gwamnatin tarayya ta kaddamar da wani sabon shiri mai suna ‘Lumina Programme’, na magance yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a Nijeriya.

Karamar ministar ilimi, Farfesa Suwaiba Ahmad Ahmad, ta bayyana cewa shirin zai samar da ilmin karance-karance da kuma ilmin lissafi, musamman ga yara mata a cikin al’ummomin da ke da wuyar isar da sako.

A Kaduna, gwamnatin jihar ta ce za ta horas da mambobin kwamitin kula da makarantu (SBMC) 8,700 domin inganta ilimi a matakin farko a jihar.

Mukaddashin shugaban hukumar kula da ilimin bai daya ta Jihar Kaduna (KADSUBEB) Mubarak Muhammad ne ya bayyana hakan a Kaduna kwanan nan.

Har ila yau, wata kungiya mai zaman kanta (NGO) mai suna IA-Foundation, ta tara Naira miliyan 30 a taron agajin da ta gudanar kwanan nan a birnin Landan domin tallafa wa ilimin yaran da ba sa zuwa makaranta a Nijeriya.

Shugabar kungiyar ta IA-Foundation, Misis Ibironke Adeagbo, ta ce za a tura asusun ne domin taimakawa muhimman ayyukan kungiyar kai tsaye.

Tsaro
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Nijar Ta Rattaba Hannu A Kan Dokar Haramta Auren Jinsi
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Za Mu Iya Sayar Da Manmu Ba Tare Da Wata Matsala Ba -Iran
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Dattawan Arewa Sun Buƙaci Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta-baci Kan Tabarbarewar Tsaro
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Nijeriya Ta Karbi Ƴan Nijeriya 268 Da Suka Tsero Daga Afirka Ta Kudu

MASU ALAKA

Duk Da Sabani Tsakanin Ɗangote Da NNPC Jiragen Ruwa Ɗauke Da Man Fetur Sun Iso Nijeriya
Kasashen Ketare

Amurka Ta Dakatar Da Takunkumin Man Fetur Kan Iran

June 22, 2026
Ya Kamata Farashin Siminti Ya Sauka — Umahi Ga Masana’antun Siminti
Manyan Labarai

Ya Kamata Farashin Siminti Ya Sauka — Umahi Ga Masana’antun Siminti

June 22, 2026
Yanzu-Yanzu: An Kashe Manoma 18 Da Raunata Wasu A Wani Sabon Hari A Filato
Manyan Labarai

Yanzu-Yanzu: An Kashe Manoma 18 Da Raunata Wasu A Wani Sabon Hari A Filato

June 22, 2026
Next Post
Ramuwar Gayya: Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda Da Yawa A Borno

Ramuwar Gayya: Sojoji Sun Kashe 'Yan Ta'adda Da Yawa A Borno

LABARAI MASU NASABA

Duk Da Sabani Tsakanin Ɗangote Da NNPC Jiragen Ruwa Ɗauke Da Man Fetur Sun Iso Nijeriya

Amurka Ta Dakatar Da Takunkumin Man Fetur Kan Iran

June 22, 2026
Ministan Wajen Sin Ya Gana Da Mataimakin Sakataren Majalisar Koli Ta Tsaron Iran 

Ministan Wajen Sin Ya Gana Da Mataimakin Sakataren Majalisar Koli Ta Tsaron Iran 

June 22, 2026
Hada-hadar Sayayya Ta Gudana Bisa Daidaito Yayin Bikin Gargajiya Na Dragon Boat Na Bana

Hada-hadar Sayayya Ta Gudana Bisa Daidaito Yayin Bikin Gargajiya Na Dragon Boat Na Bana

June 22, 2026
Ya Kamata Farashin Siminti Ya Sauka — Umahi Ga Masana’antun Siminti

Ya Kamata Farashin Siminti Ya Sauka — Umahi Ga Masana’antun Siminti

June 22, 2026
Jam’iyyar APC Ta Tafka Asarar Mabiya A Gombe, Sun Bi Pantami PDP

Jam’iyyar APC Ta Tafka Asarar Mabiya A Gombe, Sun Bi Pantami PDP

June 22, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Gargaɗi Masu Ɓoye Gas Ɗin Girki

Gwamnatin Tarayya Ta Gargaɗi Masu Ɓoye Gas Ɗin Girki

June 22, 2026
Kotu Ta Bayar Da Umarnin Tsare Sowore A Gidan Yarin Kuje

Kotu Ta Bayar Da Umarnin Tsare Sowore A Gidan Yarin Kuje

June 22, 2026
Yanzu-Yanzu: An Kashe Manoma 18 Da Raunata Wasu A Wani Sabon Hari A Filato

Yanzu-Yanzu: An Kashe Manoma 18 Da Raunata Wasu A Wani Sabon Hari A Filato

June 22, 2026
Yanzu-Yanzu: Firaiministan Birtaniya Keir Starmer Ya Yi Murabus

Yanzu-Yanzu: Firaiministan Birtaniya Keir Starmer Ya Yi Murabus

June 22, 2026
Sojoji Sun Ceto Mutanen Da Aka Sace, Sun Daƙile Hari A Kaduna Da Zamfara

Sojoji Sun Ceto Mutanen Da Aka Sace, Sun Daƙile Hari A Kaduna Da Zamfara

June 22, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.