Ma’aikatar noma da raya karkara ta kasar Sin, ta ce Sin ta yi nasarar kyautata yanayin rayuwar mazauna yankunan karkara, inda ta yi nasarar bunkasa kwazon karfafa sassa masu rauni, a fannin samar da ababen more rayuwa a shekarar 2023. Har ila yau, an kaddamar da tsare-tsaren tsaftace muhalli a sama da kaso 95 bisa dari na kauyukan Sin.
Bugu da kari a shekarar 2023, sama da kaso 73 bisa dari na iyalai dake yankunan karkarar Sin na da makewayi mai tsafta, yayin da a daya bangaren kaso sama da 40 bisa dari na gidajen dake yankunan karkarar kasar ke da tsarin sarrafa dagwalon bandakuna. (Mai fassara: Saminu Alhassan)