Duniya ta shirya tsaf, tare da dakon muhimmiyar ganawar da za a yi gobe Laraba tsakanin shugabannnin manyan kasashe mafiya karfin tattalin arziki biyu na duniya, wato Sin da Amurka, karo na farko bayan tattaunawar da suka yi a tsibirin Bali, yau shekara 1 da ta gabata.
Rikici tsakanin Sin da Amurka, abu ne dake da mummunan tasiri ga ilahirin kasashen duniya ba wai kasashen biyu kadai ba, don haka, mai da wuka kube da dakatar da takalar fada da Amurka ke yi a kai a kai da hada hannu da Sin wajen jan ragamar al’amuran duniya, zai haifar da kyakkyawan tasirin da zai shafi kowanne lungu da sako na duniya, tare da samar da zaman lafiyar da muke muradi.
- Akwai Bukatar Sin Da Amurka Su Hada Hannu Domin Kyautata Dangantakarsu
- Yajin Aiki: TCN Ya Musanta Rahoton Datse Wutar Lantarki A Fadin Nijeriya
Ziyarar manyan jami’an Amurka a Sin, da ma na Sin a Amurka, ta share fagen tattaunawar shugabannin biyu, don haka abun da dukkanmu ke fata shi ne, ganin an aiwatar da sakamakon tattaunawar a aikace ba wai a fatar baki ba, kasancewar Amurka ta saba yin amai tana lashewa. A ganina tabbas zuwa yanzu, ta ga yadda dabi’arta ke hana ruwa guda, ko a dangantakarta da Sin ko kuma a harkokin duniya.
Kamar yadda ta sha nanata cewa ba ta neman takara ko cacar baki da Sin, to za mu yi fatan ganin kyautatuwar dangantaka, inda za su hada hannu wajen taimamakeniya da tuntubar juna da kara hadin gwiwa don ganin ci gaban kasashen biyu ba wai kokarin dakile kasar Sin ba.
Za mu yi fatan ganin Amurka ta daina yada jita-jita dangane da kasar Sin, haka kuma ta daina tsoma baki cikin harkokinta na gida. Dabaru da matakn Sin, sun riga sun dace da yanayinta da muradun al’ummarta, don haka, bai kamata a nemi kakaba mata wani ra’ayi na daban ba.
Muna fatan ganin an hada hannu tare da kokarin samar da duniya mai makoma ta bai daya da jituwa da girmama juna tsakanin mabanbanta al’ummomi da matsakaiciyar wadata, ta yadda za a shimfida ingantacciyar wurin rayuwa ga zuri’o’in dake tafe.
Haka zalika, muna sa ran ganin an gudanar da tattaunawar lami lafiya kamar yadda aka tsara da samun kyawawan sakamako, tare da dawowar shugaban kasar Sin gida lami lafiya. (Faeza Mustapha)