A wannan makon mun zo muku da sabon salo, maimakon tattaunawa da Mabiya shafin Taskira, mai karatu da kai za mu yi. Sai ka kalmashe kafa ka gyara zama, mu je zuwa…
Bari mu fara wannan batu da soyayyar da ke faruwa tsakanin tsofaffi maza da kuma kananan yara jikokinsu. Bisa halitta duk wani mutum da irin abin da yake sha’awa. Haka ma yake a cikin maza da mata kowanne da irin bangaren da ya fi sha’awar soyayya ko aure.
- Har Yanzu Ƙanjamau Na Kashe Mutum Guda Duk Bayan Minti Ɗaya – Majalisar Ɗinkin Duniya
- Kamfanonin Nijeriya Sun Kara Wa Ma’aikatansu Albashin Naira Tiriliyan 4.6 Cikin Wata 6 -NBS
A dabi’a irin ta mace, ba ta cika kula namiji wanda suke shekarunsu kusan daya ba ko ya grime ta da shekaru kadan bare kuma ta tsaya tana sauraron wanda ta girme shi. Duk da yake akwai wasu matan da su kuma sun fi sha’awan kananan yara maza. Haka nan yake ga wasu ‘yan matan da suke soyayya da mazan da za su yi jika da su.
Dattijan maza ba sa doguwar soyayya idan suka ga mace suna so. Don haka duk dattijon da aka ga yana doguwar soyayya da mata, to akwai alamun tsohon kawai ne. Irin wadannan tsofaffin akwai kananan ‘yan mata da su kuma irinsu suka fi kulawa a soayya, saboda da dalili kamar haka:
– Rashin Sanin Ciwon Kai- wasu kananan matan suna fadawa tsundum cikin soyayya da dattijai ne saboda rashin wayo na karancin shekarun da za su iya tantance maza. A irin wannan yananyin idan mace ta hadu da dattijon najadu ya soma lalata da ita, ta rika bin tsoffi kenan suna zina da ita.
– Kusanci: Akwai wasu kananan ‘ya’ya mata da sun fi samun yin kusanci da tsoffin maza fiye da samari. Wannan kusance na bada damar samun shakuwar da za ta yi sha’awar wannan dattijon, saboda wasu halayensa na kirki ko kuma na banza. Yadda za ta rika ganin duk namijin da bai da irin wadannan shekarun ba zai samun abin da take sha’awar ganin sa da su ba.
– Rigakafin Yaudara: Su dai tsoffin da suke soyayya da kananan ‘yan mata ba su cika musu alkawarin aure ba bare ma su saka a ransa za su aure shi kuma daga baya ya yaudare ta. Wannan shi ma dalili ne da ‘yan mata kananan ke kula tsoffin maza da soyayya.
– Rashin Takura: Ita mace koda kuwa babba ce ba ta son takura ko a sakamata idanuwa. Su kuwa wadannan dattawan najadu tun da sun san ba auren su za su yi ba, ba ma sa so asan suna hulda da kananan yaran bare kuma su takurawa rayuwar yarinyar. Saboda wannan dama na watayawa da ‘yan matan suke samu wajen wadannan tsoffin suke ba su sha’awar yin soyayya da su.
-Son Abun Duniya: Da yake wasu tsoffi masu soyayya da kananan yara suna da abin hannunsu. Kuma ba su shakka ko jin za fi kashewa irin wadannan ‘yan matan, hakan ya sa ‘yan mata kanana suke matukar son yin soyayya da dattawan maza, domin samun biyan bukatunsu da zai iya tinkarosu ako da yaushe.
Wadannan suna cikin dalilan da ya sa kananan ‘yan mata suke nacewa wajen yin soyayya da dattawan da suka haifi iyayensu.