• English
  • Business News
Thursday, November 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Me Ya Hana Amurka Ta Ce “A Tsagaita Bude Wuta”?

by CGTN Hausa
2 years ago
Amurka

John Kirby, babban jami’in kwamitin kula da harkokin tsaro na fadar White House ya bayyana a gun wani taron manema labarai da aka gudanar a kwanan baya cewa, a ganin Amurka, tsagaita bude wuta, ba ita ce hanyar da ta dace ta daidaita batun Palasdinu da Isra’ila ba, don haka, ba ta fatan ganin an tsagaita bude wuta nan da nan. Ya kara da cewa, Isra’ila na ci gaba da daukar matakai na yakar manyan jami’an Hamas, kuma a ganin Amurka, kungiyar Hamas ita ce kadai ke iya amfana daga tsagaita bude wuta. Sai kuma a makon da ya gabata, mista Kirby ya ce, yanzu lokaci bai yi ba na tsagaita bude wuta a zirin Gaza. 

Sama da mutane dubu 10 na Palasdinu da Isra’ila sun halaka a rikicin da ya barke a tsakaninsu a wannan karo. Amma abin takaici shi ne tun bayan barkewar rikicin, shugaban kasar Amurka da sauran manyan jami’an kasar, duk sun yi shiru game da batun tsagaita bude wuta. Daftarin kudurin da Amurka ta gabatar ga kwamitin sulhu na MDD bai yi bayani a kan batun tsagaita bude wuta ba, baya ga haka, Amurka ta jefa kuri’ar nuna rashin amincewa da kudurin da aka zartas a babban taron MDD, wanda ya yi kira da a tsagaita bude wuta a tsakanin Palasdinu da Isra’ila.

  • Bikin Al’adu Na Inganta Mu’amalar Al’adun Sin Da Najeriya
  • An Mai Da Hankali Kan Ci Gaba Mai Inganci Yayin Taron Koli Kan Harkokin Kudi Na Sin

Ke nan me ya hana Amurka ta ce “A tsagaita bude wuta”, a yayin da ake fuskantar wannan mummunan rikicin zubar da jini?

A hakika, huldar dake tsakaninta da Isra’ila na da muhimmiyar ma’ana gare ta. Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya taba bayyanawa a jawabin da ya gabatar a shekarun da suka gabata cewa, “Da a ce babu Isra’ila, to Amurka za ta kirkiro Isra’ila don kare muradunta a yankin gabas ta tsakiya.” Kasancewar Isra’ila kasa ce mai karfi ta fannin soja da leken asiri, Amurka na daukarta a matsayin babban makaminta a yankin gabas ta tsakiya, abin da ya sa Amurka ta dade tana nuna goyon baya ga Isra’ila. A sa’i daya kuma, a kan ce babu wanda zai ci nasara daga yaki, amma abin ba haka ba ne ga masana’antun samar da makamai na kasar Amurka. Kwana uku kadai bayan barkewar rikici a tsakanin Palasdinu da Isra’ila a wannan karo, farashin hannayen jari na kamfanin Lockheed Martin ya karu da kaso 9%, a yayin da farashin ya karu da kashi 4% ga kamfanin Raytheon, wadanda ke daga cikin manyan kamfanonin samar da makamai biyar na kasar Amurka. Kamar yadda Greg Hayes, babban jami’in kamfanin Raytheon ya bayyana a yayin zantawa da ’yan jarida a kwanan baya cewa, “yaki abu ne na bakin ciki, amma yana kawo mana cinikin makamai.”

Rikici na ci gaba, a yayin da kuke karanta wannan sharhi, ya yiwu fararen hula sun mutu ko jikkata. Amma duk wadannan ba abu ne dake gaban muradunta ba, kuma “hakkin dan Adam” da ke bakinta ya zama banza a gaban muradunta. (Mai Zane: Mustapha Bulama)

LABARAI MASU NASABA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki
Daga Birnin Sin

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka
Daga Birnin Sin

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

November 5, 2025
Next Post
Baje Kolin CIIE Na Kara Jan Hankalin Sassa Kasa Da Kasa

Baje Kolin CIIE Na Kara Jan Hankalin Sassa Kasa Da Kasa

LABARAI MASU NASABA

Amnesty International Ta Soki Tinubu Kan Yi Wa Masu Laifin Take Haƙƙin Ɗan Adam Afuwa

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Don Karɓo Rancen N1.15trn Don Cike Giɓin Kasafin Kuɗin 2025

November 6, 2025
Jirgin Ƙasa Ya Murƙushe Direban Adaidaita Sahu Da Fasinja A Jos

Jirgin Ƙasa Ya Murƙushe Direban Adaidaita Sahu Da Fasinja A Jos

November 6, 2025
Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax

Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax

November 6, 2025
Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata

Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata

November 6, 2025
Gwamnatin Tinubu “Kasuwa Ce Mara Amfani Ga Talaka” – PDP

Majalisa Ta Ɗage Tantance Ministan Tinubu Saboda Rashin Rahoton Tsaro

November 6, 2025
Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

Mao Ning: Harka Da Kasar Sin Mabudi Ne Na Samun Damammaki

November 5, 2025
Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140

November 5, 2025
Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

Li Chenggang Ya Gana Da Tawagar Cinikayyar Kayan Noma Ta Amurka

November 5, 2025
Majalisar Dattawa

Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i

November 5, 2025
Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin

November 5, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.