An saba ganin ana jifar ‘yan siyasa da sauran manyan mutane da ra’ayinsu bai zo daidai da na talakawa ba, kokuma wadanda aka sa wa rai akan samun sauyi amma kuma su ka kasa fitar da kitse wuta, wadannan da sauran dalilai na daga cikin abin da ke sa a jefi mutum a arewacin Nijeriya da sauran yankunan Nijeriya, amma kuma ba a saba ganin ana jifar mawaka ko jaruman fim ko na barkwanci dake kokari wajen nishadantarwa ko fadakar da mutane ba.
A yayin bukukuwan karamar Sallar da aka gudanar a wannan shekarar, an samu wasu fusatattun matasa da suka jefi wasu mawaka da aka gayyato domin su nishadantar da masu kallonsu a jahohin Katsina da Kaduna, mawaki Ngulde wanda akewa lakabi da Sarkin Hoto ya gamu da fushin matasa a Jihar Katsina yayin da ya je domin gudanar da wasannin bikin sallah.
- Yadda Tashar Jirgen Ruwan Apapa-Moniya Za Ta Taimaka Wa Masu Safarar Fitar Da Kaya
- Sin Za Ta Kara Harajin Fito Kan Hajojin Amurka Da Ake Shigarwa Kasar Zuwa 125%
An ga ana jifar mawakin a lokacin da yake rera wakoki a gaban daruruwan mutane da ke kallo, amma kuma rahoto ya bayyana cewar akwai laifin da Ngulde ya yi wa jikokin na Dikko a kwanakin baya, LEADERSHIP Hausa ta samu labarin cewar a kwanakin baya yayin wata ziyara da ya kai birnin Katsina Ngulde ya tsaya a kofar shiga birnin ya kunna wa taba (sigari) wuta domin tsokanar katsinawa.
Ashe kuma hakan bai yiwa na Dikkon dadi ba wadanda akewa kirarin Na Dikko Dakin Kara Kunya Gareku Baku da Tsoro, to a wannan lokacin sai su ka samu damar yin abin da su ka kira ramuwa ga wannan matashin mawakin har ta kai ga sun fasa mashi kai sai da ya je asibiti.
Bayan abin da ya faru da Ngulde a Katsina sai kuma wani faifan bidiyo ya bayyana a kafafen sada zumunta, inda aka ga matasa na jifar matashin mawaki Bilal Billa a lokacinda yake tsaye ya na rera wakoki domin burge masoyanshi, a yayin da ake jifar mawakin kuma an ji Bilal na cewa ” I Lobe You Kaduna” ma’ana ina sonku, wannan ba girmanku ba ne da sauran kalmomi na karfafa gwuiwa.
Lamarin ya faru ne a lokacin da matashin mawakin yake kan dandamali ya na rera daya daya daga cikin fitattun wakokinsa, har zuwa lokacin wannan rahoto, Bilal Billa bai fitar da wata sanarwa a kafafen sadarwar ba, amma kuma faruwar lamarin ya janyo cece kuce inda wasu a bangare guda ke ganin abin da aka yi wa mawakan ya yi daidai yayin da wasu kuma ke ganin hakan bai dace ba.
Wasu na ganin cewar kalmar nan ta bahaushe da ya ce “Bokan Gida Bai Ci”, shi ne ke faruwa a kan wadannan mawakan, wasu kuma na ganin wannan wata hanya ce da aka dauko domin dakile tauraruwarsu da ke haskawa, wasu kuma ke cewa wannan kawai wata hanyar nuna hassada ce da mutanen arewacin Nijeriya ke amfani da ita saboda a kudancin kasar irin wannan ba kasafai yake faruwa tsakanin mawaka da sauran al’umma ba.
Ko ma dai minene dalilin da ya janyo jifar mawakan, ba zai rasa nasaba da banbancin ra’ayi ba kokuma rashin jituwa a tsakanin mawaka da masu saurarensu akan wani abinda su ka taba fafi ko aikatawa a cikin wakokinsu, sau da dama mawakan siyasa na fuskantar wannan kiyayya daga masoyansu wadanda ra’ayinsu ya saba a siyasance.
A wani lokaci can baya shahararren mawakin siyasa a Nijeriya Alhaji Dauda Adamu Kahutu wanda aka fi sani da Rarara ya fuskanci kalubale daga mutane da suke da banbancin ra’ayin siyasa, har ta kai ga wasu fusatattun matasa sun farmaki ofishinsa domin nuna fushi a kan wakokin suka ko tsangwama da yake yi wa gwaninsu a siyasance.
Amma kuma ba kasafai ake samun mawakan nanaye, nishadi ko soyayya da samun tsama tsakaninsu da masoyansu ba, duba da cewar mafi yawan lokutan mawakan kan sosa masu inda yake yi masu kaikayi a fagen soyayya, amma kuma wadannan al’amura da su ka faru a wannan shekarar ya jefa tambaya a zukatan wasu da dama a kan MI YA JANYO JIFAR MAWAKA A AREWACIN NIJERIYA.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp