Daga ranar 20 zuwa 24 ga wata, an gudanar da taron shekara-shekara na dandalin tattauna tattalin arzikin duniya na 2025 a birnin Davos na kasar Switzerland. A matsayin wani muhimmin dandali na tattauna batutuwan tattalin arzikin duniya, ana kira Davos da wurin da ake saita “Alkiblar tattalin arzikin duniya”.
A halin yanzu, duniya na fuskantar sauye-sauye wadanda ke kara habaka, musamman yadda ake samun saurin bunkasuwar sabbin fasahohi kamar fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam da sauransu, amma a sa’i daya kuma, yakin haraji da yakin ciniki na kara kunno kai. Bisa wannan yanayin da ake ciki, taron shekara-shekara na bana, mai taken “Hadin gwiwa a lokaci mai fasahohi na zamani” yana da ma’ana sosai a aikace. Jama’a kuma sun sake zura idanunsu kan kasar Sin, suna mai da hankali kan ko wane irin sabbin tunani wannan kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya za ta kawo don inganta hadin gwiwa a wannan lokaci mai fasahohi na zamani?
- Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Gudanar Da Liyafar Sabuwar Shekara
- Nazarin CGTN: Amurka Na Dora Laifin Gazawar Shugabancinta Kan Bakin Haure
Shawarwari hudu da kasar Sin ta gabatar, ciki har da inganta dunkulewar tattalin arzikin duniya baki daya, tare da samar da sabon karfi da fifiko ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya, da kiyayewa da aiwatar da ra’ayin cudanyar bangarori da dama tare, da kuma magance sauyin yanayi tare, wadannan shawarwari hudu da kasar Sin ta gabatar, sun sa jama’a sake yin nazari kan muhimmin jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba gabatarwa a Davos, wanda ya nuna alkiblar inganta “hadin kai a lokaci mai fasahohi na zamani”.
Daukacin mahalarta taron suna ganin cewa, wadannan shawarwari suna wakiltar ra’ayoyin yin kirkire-kirkire, daidaito, kiyaye muhalli, bude kofa da kuma more nasarorin da ake cimmawa tare, wadanda kuma suka biya bukatun bangarori daban daban na yin aiki tare don kirkirar sabon sararin ci gaba, kuma suna taimakawa wajen dakile yunkurin wasu kasashe na mayar da wata kasa saniyar ware da kawar da gibin ci gaba da suka kafa, ta yadda dunkulewar tattalin arzikin duniya zai kara inganta, kuma kowa ya ci gajiya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp