Jama’a, me za ku ce idan kun ji an ce “na’urar daga kaya ka iya haifar da barazana ga tsaron wata kasa”? Tabbas za ku dauki zancen a matsayin abin dariya. Sai dai an ji zancen ne a bakin wani babban jami’in kula da tashar jiragen ruwa na Los Angeles ta kasar Amurka.
A kwanakin baya, jami’in ya ce, na’urorin daga kaya da kasar Sin ta samar ka iya haifar da barazana ga tsaron kasar Amurka, don haka kuma, gwamnatin Biden na shirin zuba biliyoyin daloli wajen samar da na’urorin a cikin gida.
- ‘Yan Sama Jannatin Sin Sun Kammala Aikin Gyara Na’ura A Wajen Kumbo A Karon Farko
- Yadda Sin Ke Dora Muhimmanci Ga Zamanintarwa Da Ci Gaba Mai Inganci
Duk da cewa hakan abin ban dariya ne, amma ba a rasa jin irin wadannan abubuwa cikin ‘yan shekarun baya bayan nan. Daga shigowa da kayan karafa da goran ruwa da motoci, zuwa daliban da ke dalibta a kasar, har ma da tafarnuwa da gajeren shirin bidiyo, tamkar dukkansu na iya “haifar da barazana ga tsaron kasar Amurka”. Amurka ta kusan haukacewa domin “tsoron kasar Sin”.
Amma sabo da me take wannan tsoro? In mun yi nazari, za mu gano cewa, saurin bunkasuwar kasar Sin cikin shekarun baya bayan nan ya sa wasu Amurkawa, da sauran wasu kasashen yamma damuwa da rashin jin dadi. Don haka suke son kafofin yada labaransu su yi ta yayata kalamai na wai “barazana daga kasar Sin”, tare da shafa wa kasar kashin kaza, bisa ga yadda suke zarginta da dana wa kasashe masu tasowa “tarkon bashi”, ga shi har na’urar daga kaya da ta samar na iya leken asiri……A ganinsu, kome na kasar Sin barazana ce.
Sai dai hakan ya tono mana gaskiya game da yadda Amurka ke fakewa da “tsaron kasa” wajen dakile kasashen da take dauka a matsayin abokan takara. Sanin kowa ne, Amurka ta sha yin zancen “’yancin takara” da “’yancin ciniki” a yayin da take zargin wasu kasashe da rashin ’yanci a kasuwanninsu. Amma yayin da kasashe masu tasowa ke dada bunkasa, tare da cimma nasarori wajen kirkire-kirkiren fasahohi, Amurka ita kanta kuma masana’antunta na raguwa, nan da nan sai Amurka ta manta da ‘yancin ciniki da na takara, kuma ta dauki matakai iri iri na dakile abokan takararta, da ci gaban sauran kasashe. A zahiri dai, “tsaron kasa” dalili ne kawai da ta sanar na yin kariyar ciniki da babakere, a yunkurin kare cikakkiyar moriyarta.
Sai dai a zamanin da muke ciki na dunkulewar tattalin arzikin duniya, kasa da kasa sun kasance suna cude-ni-in-cude-ka, duk wata nasarar kirkire-kirkire ta kan samu ne bisa hadin gwiwar sassan duniya daban daban. Katse huldar tattalin arziki da sauran kasashen duniya ba zai yi komai ba, illa lalata karfin kasar da ta yi hakan, da ma tsananta matsalolin da take fuskanta.
Shawara ga kasar Amurka ita ce ta mai da hankali a kan gano bakin zaren warware matsalolin da take fuskanta, kuma ta kalli ci gaban sauran kasashe yadda ya kamata, tare da rungumar hadin gwiwar kasa da kasa, hakan zai kawar da damuwarta game da kasar Sin, da ma gano hanyar kara raya kanta. (Mai Zane:Mustapha Bulama)