A dangane da martanin da Amurka ta yi na cewa, kasar Sin ta sanar da kakaba takunkumi kan kamfanonin Amurka dake samar da kayan soja, don karkata hankalin duniya daga lamarin balan-balan din da ya shiga samaniyar Amurka, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Wang Wenbin ya musanta hakan, yayin da aka tambaye shi a wani taron manema labarai da aka saba gudanarwa Juma’ar nan.
Wang Wenbin ya yi nuni da cewa, idan aka maganar karkatar hankalin duniya, ina son in tambayi Amurka dalilin da ya sa ta ga balan-balan a samaniya a tsayin mita 18000 amma ta kyale gajimare mai kunshe da sinadarin vinyl chloride a samaniyar jihar Ohio dake kasar. Kana me ya sa ta sanar da yin bincike kan fashewar bututun Nord Stream da farko amma ba ta yi bayani ko kadan ba bayan da ‘yan jaridan Amurka suka gabatar da sabon rahoton bincike? Bai kamata Amurka ta yi amfani da aikin soja wajen mayar da martani mai tsanani kan wannan batu, da kuma zargin kasar Sin domin yunkurin siyasar batun ba. (Zainab)