A yau shafin TASKIRA zai yi duba ne dangane da abin da ya shafi canjin ra’ayin ‘yan’mata game da samarinsu, duba da irin korafe-korafen da wasu samarin ke yi a kan ‘yan’mata na yadda suke iya sauya ra’ayinsu cikin lokaci kankani. Wannan matsala ce wacce ta addabi samari, wanda kuma hakan ke ci musu tuwo a kwarya, har suke rasa gane inda matsalar take, Shin wai a ina matsalar take?
Ire-iren hakan na faruwa wanda wasu mutanen kan rasa gane inda matsalar ke haifuwa ta fanni iyayen yaran ne ko kuwa ta su kansu ‘yan’matan ne?
Ba komai ya sa ake kallon hakan ba, sai don ganin yadda ‘yan’amata ke fasa auran saurayin da suka amincewa tun a farko ba tare da an same shi da wata matsala ba, ba abin mamaki bane idan aka ce an same shi ne ta rashin yawaita mikawa budurwa wasu kudade ko biya mata bukatun cikin gida kamar dai yadda wasu samarin ke yi, su kashewa mace kudi kafin aure, bayan aure kuma a jigatu, wanda ba kowacce mace ce ke iya gane hakan ba sai me nazari da tunani, da kuma kallon abubuwan da suka faru a kan wata ko a kan wasu.
Tabbas! wannan matsala ce wacce wasu ‘yan’matan kan dauke ta a ba komai ba, ko na ce kankanuwar matsala wacce suke iya magance ta cikin kankanin lokaci. ‘Yan ‘mata da dama na amincewa da samari da zummar suna sonsu irin so na hakika wanda ba za a taba rabuwa har bayan aure, haka dai soyayya za ta ci gaba da kulluwa tsakanin saurayi da yarinya, wanda inda za a buncika za a iya samun cewa macen ita ce wacce ta fara kai tayin soyayyarta wajen namijin tun kafin ya ganta ya ce yana so.
Sai dai wani hanzari ba gudu ba yayin da tafiya tayi tafiya soyayya ta bunkasa har sauran ‘yan’uwa da iyayen yarinya suka san da magana har suka amince ake shirin yin baiko sai zance ya sha bamban, labarin ya canja yarinyar ta sauya akala, amincewar da tayi a baya duk maganar ta shafe ta fasa soyayyar, ta canza wani saurayin daban.
Wasu matan na yin hakan ne yayin da suka ci karo da saurayin da ya fi wanda suka amincewa a farko, ta yiwu sun yi hakan ne domin shi na farko ba shi da yawan kudin da suke bukata, ta yiwu kuma ba shi da kyan da shi na biyu yake da shi, ta yiwu kuma wanda suka canja din dan gayu ne, ko me ilimin boko ne ko fitacce ne wanda duniya ta san da zamansa, ko kuma kalaman bakinsa ne ya haura na farkon da suka amincewa, da sauran abubuwan da su kadai suka san dalilin sauya ra’ayinsu a kan namijin da suka fara amincewa ba tare da wani kwakkwarar hujjar da za su rabu da shi ba.
Shin a ina matsalar take?
Kar dai a manta ba duk ka mata ne aka taru aka zama daya ba, akwai ‘yan’mata da dama wadanda suke tsayawa a kan saurayi guda, ba tare da sun canja akalarsu ba, ba tare da sun warware alkawarin da suka daukarwa saurayin da suka daukarwa ba, ba tare da sun yi duba ko hangen abun kawa ga wasu mazan ke da shi wanda shi saurayin nasu ba shi da shi ba, haka kuma ba tare da sun kalli kyau ko munin wani abu nashi ba.
Akwai ‘yan’matan da ba sa taba tunanin cutar da saurayin da suke so koda da zuciya ne, akwai ‘yan’matan da babu ruwansu da canjawar zamani musamman ta fannin hangen abun hannun namiji ko rokon abun hannunsa da zummar dauka dawainiyarsu ba.
Yanada kyau ‘yan mata su kula su kuma kiyaye da duk abin da bai dace ba ko dan gudun zubda mutuncin kansu ko na iyayensu, ya zamana suna amfani da iliminsu domin shi ne wayewa ba wai yin abin da zai zama abun Allla-wadai ba. Su daina amincewa samarin da suka san ba wai son gaskiya suke yi musu ba karshe su barsu daga baya idan suka rasa wanda suka kama su kara komawa wajen wanda suka bari hakan sam! bai dace ba, domin ba daidai bane, babu wacce za ta so a yi wa dan’uwanta yayanta ko kaninta ko wani dan’uwansu irin hakan ba,