A kwanakin baya ne, ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS ya gudanar da wani taro, inda ya yanke shawarar gudanar da gangamin wayar da kan jama’a kan nazari da aiwatar da tunanin Xi Jinping kan tsarin gurguzu mai sigar kasar Sin a sabon zamani a daukacin jam’iyyar tun daga watan Afrilun wannan shekara.
Manufar gangamin wayar da kan jama’a na JKS, ita ce mayar da hankali wajen koyo da samun ilimi a fannoni daban-daban da abubuwan da aka gudanar a cikin jam’iyyar. Tun bayan kafuwar JKS, tsawon shekaru dari, JKS ta gudanar da harkokin koyo da koyarwa iri-iri a cikin jam’iyyar bisa hakikanin bukatunta a lokuta da kuma matakai daban-daban.
Babban sakatare Xi Jinping ya jaddada a cikin jawabinsa cewa, muhimmin aikin gudanar da wannan gangami, shi ne sauya akidar gurguzu mai halayyar kasar Sin a sabon zamani, zuwa wani karfi da zai yi jagora da ma inganta ayyukan ilmantarwa da jagoranci ’yan jam’iyya da jami’ai, don tabbatar da ra’ayin ci gaban jama’a, da yunkurin bunkasa tunanin jama’a na samun alheri, farin ciki, da kuma tsaro. (Mai fassarawa: Ibrahim)