Daga ranar 5 zuwa ta 10 ga watan nan, an shirya bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin daga ketare, wato CIIE a takaice, karo na 7 a birnin Shanghai na Sin, inda kasar Najeriya ta nuna boyayyen karfinta a fannin cinikayya.
Shugabar kwamitin inganta aikin fitar da kayayyaki ta kasar Najeriya Nonye Ayeni ce ta jagoranci tawagar Najeriya wajen halartar bikin CIIE na wannan karo, inda suka nuna dimbin kayayyakin kasar Najeriya, irinsu amfanin gona, da ma’adinai, da dai sauransu. Kana a yayin da take hira da abokin aikina Murtala Zhang, Malama Ayeni ta ce, yadda kasar Sin ta yarda da shigowar gyada daga Najeriya cikin kasuwannin Sin zai amfani manoma da ‘yan kasuwa na Najeriya. Tana kuma fatan yin amfani da damammakin da kasar Sin ta samar, don neman sayar da karin kayayyakin Najeriya zuwa ketare.
- Ya Kamata A Dakatar Da Duk Wasu Wasanni A Sifaniya Saboda Ambaliyar Balencia – Ancelotti
- Shugabannin Sin Da Italiya Sun Kalli Kayayyakin Tarihi Da Aka Dawo Da Su Kasar Sin
Ban da Najeriya, sauran kasashen Afirka da suka nemi damammaki a wajen bikin CIIE na bana sun hada da Benin, da Madagascar, da Namibia, da dai sauransu. A bikin CIIE na bara, Abarba ta kasar Benin ta samu karbuwa sosai, har ma an kulla kwangilolin da darajarsu ta kai dalar Amurka miliyan 60. Ganin wannan misali ya sa dimbin kasashen dake nahiyar Afirka suka halarci bikin CIIE na wannan karo, tare da kayayyakinsu, irinsu ruwan zuma, da naman rago, da kashu, da dai makamantansu.
Tun daga watan Satunban bana, kasar Sin ta sanar da yafewa kayayyakin kasashe marasa karfin tattalin arziki, ciki har da kasashe 33 dake nahiyar Afirka harajin kwastam. Kana a wani ci gaba, kasar Sin ta kara fadin yankin baje kolin kayayyakin kasashen Afirka, a bikin CIIE na wannan karo, da samar da rumfunan baje koli fiye da 120 kyauta ga kasashe 37 marasa karfin tattalin arziki. Wadannan matakai sun nuna yadda kasar Sin ke kokarin taimakon kasashen Afirka, wajen fitar da kayayyakinsu zuwa kasar Sin, da halartar tsarin samar da kayayyakin na duniya.
Hakika, da ma an tsara bikin CIIE din ne domin taimakawa sauran kasashe samun damar fitar da kayayyakinsu zuwa kasuwannin kasar Sin, wanda ya kasance irinsa na farko a duniya. Sai dai watakila, wani ya yi tambaya game da ko mene ne dalilin da ya sa kasar Sin ta shirya bikin? kuma me ya sa take taimakon sauran kasashe da damar sayar da kayayyakin su, tare da neman riba a kasuwannin Sin?
To, dalili na farko shi ne manufar kasar Sin ta tabbatar da cin moriyar juna, yayin da take hadin gwiwa da wata kasa ta daban. Idan mun dauki hadin gwiwar Sin da Afirka a fannin ciniki a matsayin misali, za mu ga yadda kasar Sin ke kokarin neman samun daidaito a fannin cinikin da ake yi tsakanin bangarorin 2, inda ta saukaka aikin fitar da kayayyakin abinci na Afirka zuwa kasar Sin, da sanya karin kamfanonin Afirka amfani da dandalin kasuwanci na yanar gizo na kasar Sin wajen fitar da kayayyaki zuwa kasar.
Ban da haka, wani dalili na daban shi ne manufar kasar Sin ta bude kofa ga kasashen waje. Ta hanyar kara bude kofarta ga ketare, kasar Sin ta zama babbar abokiyar huldar ciniki ta kasashe da yankuna fiye da 150, cikin shekaru gwammai da suka gabata, inda ta kasance kan gaba a duniya, a fannonin yawan hajojin da take cinikinsu, da yawan jarin da take janyowa daga ketare, da wanda take zuba wa sauran kasashe. Wadannan nasarori sun shaida amfanin manufarta ta bude kofa, a fannonin raya kai, gami da haifar da moriya ga dukkanin kasashen duniya. Kuma dole ne kasar ta dauki karin matakai na bude kofa, don samar da damammaki na samun ci gaban bai daya a duniya, don kawar da mummunan tasirin da wasu matakan radin kai da wasu kasashe suka dauka suka haifar.
A karshe, tabbatar da cin moriyar juna, ko bude kofa, dukkansu na da alaka da babbar manufar kasar ta gina al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai daya. A ganin Sinawa, don cimma burin tabbatarwa daukacin dan Adam da ci gaba mai dorewa, abin da ya fi muhimmanci shi ne tabbatar da nasarar kowa, a maimakon sanya wani bangare shi kadai cin nasara. Ya kamata al’ummun kasashe daban daban su yi kokarin musayar ra’ayi da hadin kai, don neman kawar da rikici, da tabbtar da moriyar dukkan bangarori cikin daidaito, gami da samun ci gaba na bai daya a hadin gwiwarsu. (Bello Wang)