Kwanan baya, babban ministan kasar Singapore Lee Hsien Loong da ke ziyara a kasar Sin ya yaba wa bunkasuwar kasar Sin sau da dama, lamarin da ya jawo hankalin akasarin ra’ayoyin kasa da kasa. Wasu na ganin cewa, Lee Hsien Loong ya amince da yadda kasar Sin ke kara azama kan bude kofa da yin hadin gwiwa, da samun ci gaba da zaman lafiya a duniya, tare da karyata kalaman wasu na nuna rashin yakini kan makomar kasar Sin.
Dalilin da ya sa Lee Hsien Loong ya yabawa kasar Sin shi ne domin kasarsa ta Singapore ta ci riba daga yin hadin kai da kasar Sin, kana ya kalli ci gaban kasar Sin bisa sanin ya kamata daga dukkan fannoni. Har ila yau, ya amince da yadda kasar Sin take kiyaye dunkulewar tattalin arzikin duniya, zurfafa yin gyare-gyare a gida da bude kofar ga waje, da sa kaimi ga yin hadin gwiwa da kasashen waje. Kamar yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fada yayin da yake ganawa da mista Lee, yayin da ake fuskantar barazana da kalulabe, ba wata kasa da za ta kare kanta. Dole ne a tsaya tsayin daka kan hadin kai, bude kofa da damawa da juna. (Tasallah Yuan)