Yanzu haka ana gudanar da taron kolin kasashen kungiyar BRICS (Brazil, Russia, India, China and South Africa) karo na 15 wanda Afirka ta Kudu ke karbar bakuncinsa. A shekarar 2009 ce aka kafa hadin gwiwar BRIC (Brazil, Russia, India da China), daga bisani bayan shigar Afirka ta Kudu a watan Oktoban shekarar 2010 aka mayar da sunan ya zama BRICS.
’Yan Nijeriya da dama masu kishin ci gaban kasar, sun yi na’am da yadda kasar ta nuna sha’awar shiga hadin gwiwar BRICS tare da takwarorinta na sassan duniya su 40, kamar yadda Jakadan Afirka ta Kudu a hadin gwiwan na BRICS, Anil Sooklal ya ayyana wa manema labarai kwanan baya.
Tambayar da wasu ke yi ita ce, me ya sa Nijeriya ke neman shiga wannan hadin gwiwa na BRICS? Galibin amsar da masharhanta ke bayarwa ita ce, kasar tana neman mafita a kan yadda za ta samu sukunin bunkasa tattalin arzikinta da kuma saukaka yawan dogaron da ta yi da dalar Amurka.
Nijeriya na so ta ci gajiyar hadin gwiwar BRICS kamar takwararta ta Afirka ta Kudu da ta samu ci gaban kasuwanci da kawayenta da kashi 10 cikin 100 a tsakanin 2017 zuwa 2021. Sannan hada-hadar kasuwancinta da kasashen BRICS sun bunkasa daga kudin kasar Rand Biliyan 487 a shekarar 2017 zuwa Rand Biliyan 830 a shekarar 2022.
Haka nan shigarta hadin gwiwar, zai bude mata sabon babin ci gaba ta bangaren bincike da kirkire-kirkire, makamashi, kiwon lafiya da bangaren ilimi. Tuni, har Afirka ta Kudu ta ci gajiyar ayyukan bincike sama da 100 a karkashin BRICS.
Bayan haka, kasancewar an kiyasta kayan da kasashen na BRICS ke fitarwa za su kai kashi daya bisa uku na duniya nan da 2030, sannan su ne ke da kusan kashi 18 cikin 100 na cinikin duniya, da mallakar kashi 26 cikin 100 na fadin duniya da kuma kusan kashi 42 cikin 100 na yawan al’ummar duniya, Nijeriya za ta samu karin masu zuba jari daga kasashen hadin gwiwar baya ga bunkasa fitar da kaya zuwa waje.
Har ila yau, bisa irin rawar da Nijeriya ta taka a Afirka tun fil’azal, kamar shiga gaba wajen taya Afirka ta Kudu yaki da wariyar launin fata, da kashe wutar yakin basasa a Liberiya da Saliyo da gudunmawarta ga ayyukan kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, shiga hadin gwiwar na BRICS zai kara ba ta damar samun fada a ji a duniya musamman kan shirye-shirye da tsare-tsare na kashin dankali da Turawan yamma ke amfani da su.
Tabbas, BRICS hadin gwiwa ne na kasashe masu muradin ’yantar da kansu daga tsarin rashin adalci na kasa da kasa, ita ma Nijeriya na so a dama da ita!
Bugu da kari, mai fashin bakin mu malam Ibrahim Yaya ya rubuta wani sharhi mai take “Shiga Tsarin BRICS Wata Babbar Dama Ce Ta Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashe Masu Tasowa”, inda ya bayyana cewa, yanzu haka birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu ya dauki harami, inda shugabanni ko wakilan kasashen BRICS, da suka hada da Brazil, da Rasha, da Indiya, da Sin da Afirka ta kudu, suke gudanar da taron kolin shugabannin kungiyar karo na 15.
Wannan dai shi ne karo na biyu da nahiyar Afirka ke karbar bakuncin taron kungiyar. Ana sa ran taron na bana zai kasance mafi girma, inda aka gayyaci shugabanni kusan 69.
Manufar kungiyar dai ita ce, sake fasalin yanayin tattalin arziki da siyasa na kasashe mambobin kungiyar, inda suka kirkiro majalisar kasuwanci ta BRICS, yarjejeniyar bayar da tallafi na gajeren lokaci, da sabon bankin raya kasa wanda ke tallafawa ayyukan raya kasa a kasashen kungiyar.
Haka kuma taron na bana, wanda zai gudana daga ranar 22 zuwa 24 ga watan Agusta, zai mayar da hankali wajen rage dogaro kan dalar Amurka da ma yadda kasar ta Amurka ke yin babakere a harkokin kudi na duniya. Sauran fannonin sun hada da kara fadada wakilcin kungiyar, da tsarin cinikayya tsakanin kasashen kungiyar.
Bayanai sun nuna cewa, yanzu haka sama da kasashe 40 sun bayyana aniyarsu ta shiga kungiyar, har ma 22 daga cikinsu sun gabatar da bukatarsu a hukumance. Wannan ya kara tabbatar da karuwar tasirin kungiyar a harkokin kasa da kasa da ma karfinta na sake fasalta harkokin kudi a duniya a nan gaba.
Masu fashin baki na cewa, yadda karin kasashe ke fatan shiga kungiyar, hakika zai ba su damar kara cin gajiya a fannin tattalin arziki da cinikayya fiye da tsarin da kasashen yamma ke amfani da shi a halin yanzu.
BRICS ta zama wata dama ko zabi ga musamman kasashen da tattalin arzikinsu ke bunkasa da takwarorinsu kasashe masu tasowa, maimakon dogaro kan tsari ko hukumomin kudi na kasashe yammacin duniya, kamar bankin duniya ko IMF da makamantansu masu cike da danniya da babakere, don haka wannan wata babbar dama ce, abin ke zama tamkar maganar malam Bahaushe wato, Gida biyu maganin gobara.
Sai dai masharhanta na gargadin kar a yi kitso da kwarkwata, a lokacin da aka bayar da damar shigar wasu kasashe cikin kungiyar, domin kar su fake da wata mummunar manufa ko zama ’yan kanzagin kasashen yamma da nufin yiwa kungiyar zagon kasa.
Sannan game da dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Afirka ta kudu, an yi bayani cewa, a bana ne aka cika shekaru 25 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Afirka ta Kudu. Ziyarar aikin da shugaba Xi Jinping ya kai Afirka ta Kudu a wannan karo, ita ce ta hudu da ya ziyarci Afirka ta Kudu a matsayinsa na shugaban kasar Sin. A jiya Talata, yayin da shugabannin kasashen biyu suka yi shawarwari, sun amince da yin hadin gwiwa tare da inganta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Afirka ta Kudu zuwa wani sabon matsayi, da gina al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya ta Sin da Afirka ta Kudu.
Afirka ta Kudu ita ce kasa ta farko a nahiyar Afirka da ta shiga hadin gwiwar aiwatar da shawarar “ziri daya da hanya daya”, kuma ta zama babbar abokiyar cinikayyar kasar Sin a Afirka tsawon shekaru 13 a jere. Ayyukan wutar lantarki bisa karfin iska da kamfanonin kasar Sin suka gina da ma gudanarwa a Afirka ta Kudu sun haskaka gidaje dubu 300 a yankin.
Afirka ta Kudu na daya daga cikin manyan wuraren zuba jari ga kasar Sin a nahiyar Afirka. A watanni 6 na farkon bana, yawan ciniki tsakanin Sin da Afirka ta Kudu, ya karu da kashi 11.7 cikin 100 kan na shekarar bara.
Kamar yadda aka tsara, yayin taron kolin BRICS, shugabannin kasashen Sin da Afirka ta Kudu, za su jagoranci taron shugabannin kasashen Sin da Afirka. Wannan ya kara tabbatar da cewa, kasashen Sin da Afirka ta Kudu suna son kafa wani dandalin zurfafa hadin gwiwar Sin da Afirka, da sa kaimi ga bunkasuwar masana’antu da dunkulewar nahiyar Afirka, da taimakawa kasashe masu tasowa na duniya samun ci gaba tare.