REDnote wata manhajar sada zumunta ce da ke samun karbuwa a kasar Sin, kuma ni kaina ina bibiyar shafukan REDnote. Sai dai a kwanakin nan, na tarar da dimbin masu bibiyar shafin TikTok da suka fito daga kasar Amurka, wadanda suke kiran kansu “TikTok Refugee”, wadanda ke ta kaura zuwa REDnote, kuma a cewarsu, dalilin hakan shi ne don tinkarar matsalar haramcin da gwamnatin kasar Amurka ka iya sanya wa TikTok.
Lallai a baya, gwamnatin kasar Amurka ta fake da sunan wai “tsaron kasa”, kuma ta bukaci kamfanin Bytedance da ke mallakar TikTok, da ya sayar da TikTok din ga bangaren Amurka kafin ranar 19 ga watan shekarar 2025, in ba haka ba, za ta haramta yin amfani da manhajar a fadin kasar. Sai dai ba a yi zaton hakan ya sa dimbin masu bibiyar shafukan TikTok na kasar ta Amurka za su kama REDnote, a maimakon zabar manhajojin sada zumunta ta cikin gida ba. A game da hakan, wasu daga cikinsu sun ce, dalili shi ne don nuna rashin gamsuwa da yadda gwamnatin Amurka ta yi.
- Ma’aikatar Wajen Sin: Yamadidin Da Ake Yi Na “An Tilasta Wa Mutane Yin Aikin Dole” Karya Ne
- Xi Ya Zanta Da Babban Jagoran Vietnam Da Shugaban Sri Lanka
Aria Lynn Grayson, mai bibiyar shafin TikTok ce daga Los Angeles, wadda ta kan samar da hotunan bidiyo game da ilmin kwalliya. A hoton bidiyon da ta bayar a shafinta na REDnote, ta ce, “Gwamnatin kasarmu tana yunkurin haramta yin amfani da TikTok, wai manhajar tana barazana ga tsaron kasa, kuma wai kasar Sin na neman satar bayananmu, amma a hakika kasancewar mu masu ziyartar shafukan yanar gizo, musamman na shafukan TikTok, mun san abubuwan da ke faruwa a duniya.” Sai kuma wata mai bibiyar shafin TikTok da ake kira Amy daga jihar Massachusetts, tana ganin cewa, kasar Sin ba ta sha’awar sanin “me mu ka fi son ci”. Ta ce, “A hakika, gwamnatin kasar Amurka ita ce take sa ido a kan al’ummarta da satar bayananmu.” Ta kara da cewa, aminanta da yawa na TikTok sun sadu da juna a shafin REDnote, “Ina matukar jin dadin yin musaya tare da ‘yan Amurka masu bibiyar TikTok da suka kaura zuwa nan, a ganina tamkar juyin juya hali ne muka yi. Muna jin dadin yin musuyar ra’ayoyi tare da mutanen kasar Sin ta dandalin, duk da kasancewar bambancin al’adu a tsakaninmu.”
“Barkanku dai, mutanen kasar Sin, ni dan kasar Amurka ne, idan kuna bukatar taimako wajen koyon Turancin Ingilishi, to, ina nan!” “Barkanmu dai! Ni mai nazarin halittun teku ne daga jihar California, kuma zan so in samu abokai a nan, kuma ina son koyon Sinanci, kuma zan iya taimaka muku koyon Turancin Ingilishi!” “Ko za ku iya nuna min titunan kasar Sin?”…
Kamar yadda Amy ta fada, dimbin masu bibiyar shafin TikTok sun yi musaya sosai tare da masu bibbiyar shafin REDnote, bayan da suka sauke manhajar, inda suke yin amfani da Turanci ko kuma Sinancin da tamkar suka fassara da wata nau’in manhaja, suna nuna harkokin da suka shafi rayuwarsu ta yau da kullum. Kuma masu bibiyar shafin REDnote na kasar Sin ma sun yi musaya sosai tare da su. Akwai kuma wani dan Amurka da ya samu sakwannin fatan alheri kusan dubu biyar daga Sinawa masu bibiyar shafin REDnote, sa’o’i kadan bayan da ya bayyana fatan samun gaisuwar fatan alheri daga mutanen kasar Sin a shafinsa na REDnote a ranar haihuwarsa.
“A daidai lokacin da ake fuskantar tsamin dangantaka a tsakanin Sin da Amurka, an sada sabuwar zumunta a tsakanin kasashen biyu ta wata manhajar da a baya mutanen kasashen waje ba sa amfani da ita sosai.” In ji jaridar Wallstreet Journal. A duk lokacin da take da fifiko a fannin fasahohi, ta kan tabo maganar ‘yancin tattalin arziki, a lokacin da ba ta da shi kuma, sai ta jaddada muhimmancin “tsaron kasa”, wannan mataki ne da gwamnatin kasar Amurka ta saba dauka. Sai dai a wannan karo, al’ummar kasar ba su yarda a kwace hakkinsu ba.
Yau kimanin shekaru 54 da suka gabata, ta diplomasiyyar wasan kwallon tebur, kasashen Sin da Amurka suka bude kofar yin cudanya da juna, tare da farfado da huldarsu, matakin da ya haifar da muhimmin tasiri ga yanayin duniya. Bayan tsawon shekaru 54, a lokacin da huldar kasashen biyu ke kara fuskantar kalubale, muna fatan dandalin REDnote zai zamanto tamkar sabuwar hanyar da za ta kara fahimtar da al’ummar kasar Amurka game da hakikanin yanayin da ake ciki a kasar Sin, da karfafa cudanya a tsakanin al’ummomin kasashen biyu, ta yadda za a farfado da huldar kasashen biyu, don kwantar da hankulan al’ummar kasashen biyu da na duniya baki daya.