Shafin TASKIRA shafi ne da ya saba zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, ciki sun hadar da; zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya, da dai sauransu.
Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da yadda a yanzu wasu mazan suke gudun auren ‘yan boko, mata masu ilimi da wayewa. Inda shafin ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiyan sa game da wannan batu; “Shin Ina matsalar take?, ko hakan ya dace?, Ko akwai wata shawara da ya kamata a bawa masu irin wannan tunanin?.
Ga dai bayanan nasu kamar haka:
Sunana Jamila Salisu Ibrahim Jihar Kaduna:
Gaskiya dai inda matsalar take shi ne, rashin wayewa da wasu mazan suke da shi, mafi yawa kuma mazan da suke da rashin ilimi su ke da wannan dabi’ar da take ba, dauwamammiya ba. Hakan gaskiya kwata-kwata bai dace ba, saboda an fi so namiji ya auri mai ilimi, wacce za ta tarbiyyantar da ‘ya’ya kan hanya ta gaskiya, da tarbiyya gurin rayuwa ta yau da kullum. Amma idan aka ce mace ba tada wani wayewa to, ba ita kadai za ta zauna cikin wannan rashin wayewar ba, har sai ya kai ga yaran da aka haifa suma su zama cikin duhun kai, su kasa mu’amala da al’umma. Saboda duk mutum wanda yake da rashin wayewa yana tare da tsatstsauran/baudadden ra’ayi. Shawara ta a nan ita ce su mazan su gane cewa wayewa ba yana nufin rashin tarbiyya ba ko kuma budewar ido ba, face wayewa na nufin fitowar abu daga duhu zuwa ga haske.
Sunana Abba Abubakar Yakubu daga Jos a Jihar Filato:
Maza na gudun auren mace mai zurfin wayewa da ilimi ne saboda tunanin ba za su yi biyayyar aure ba, kuma ba za su iya zaman gida yadda za su kula da aurensu yadda ake so daga mace ba. Wasu mazan na tunanin akasarin mata masu zurfin ilimi suna ganin ba za su iya mika wuya ga mazajen su kamar yadda sauran mata za su yi ba, don ko dai suna da ilimi sosai ko kuma sun fi mazajen daukaka. Babban abin da maza suka fi so a wajen mata shi ne biyayya da girmamawa. Kuma samun hakan yana da wuya a wajen matan da suke ganin sun samu wayewa ko ilimi daidai da mazajen su ko ma fiye. Wannan shi yake sa maza auren yaran mata da idanun su bai gama budewa ba, kuma ilimin su bai yi zurfi sosai ba, wadanda za su dauke su a matsayin yayu ko dai mazajen su da Allah Ya hukunta suna gaba da su, kuma aljannarsu ke karkashin kafafunsu. Domin idan aka duba yadda rayuwa yanzu ta kai wani matsayi da mata masu ra’ayin ‘feminism’ ke kara yawa suna kalubalantar tasirin maza a kansu, da kuma zargin nuna musu kasƙanci da wasu maza ke yi. Don haka yanzu maza ke shakkar auren matan da za su rika kalubalantar ikon su a kansu, ko kuma raina su a cikin gidajen su. Shawara ta a matsayina na namiji magidanci shi ne mata su rika auren mazajen da suka san za su jure zama da su, wadanda za su iya yi wa biyayya, kuma su nemi yardar Allah a tare da su. Sannan ga su mazajen ina mai yi musu nasiha da su rika tallafawa matan su yadda za su yi ilimi, har su yi aiki, watarana su taimaka musu da iyalansu. Harwayau, su daina gudun masu ilimi da wayewa daga cikin mata ‘yan boko, domin shi zaman aure fahimta ce da tarbiyya. Duk girman mace ba ta wuce zama karkashin namiji, har kuma ta yi masa biyayya, matukar ya zauna da ita cikin gaskiya da amana.
Sunana Princess Fatimah Mazadu daga Jihar Gomben Najeriya:
E! to, aure ra’ayi ne, duk da wasu na daukar auren ‘yar boko da masu Ilimi mai zurfi hatsari ne ga rayuwar su, ta fannin rashin girmamawa da ladabi, da sauransu. Gaskiya ni a nawa ba wata matsala, sai dai in shi namijin ne ke da matsala. Saboda mafi akasarin mata a gidan mazajensu suke dawo wa jan wuya, duba da irin yadda namiji ke basu kulawa da akasinsa. Dabi’u da tarbiyya na lalacewa ne lokacin da mace mai Ilimi, mai zurfi ta ga mijinta na kauce hanya, ko yana kin biya mata bukatun gida. Ta kan nuna masa itama da gaske ta yi bokon duk inda yaso juya ta sai ta bankare, saboda tana da sani da karantar rayuwa da yadda za ta yi ta gyara shi a matsayinta na mai Ilimi. Gudun auren mai ilimi ‘yar boko wallahi gibi ne babba a gidan da namiji, saboda tarbiyya, karatu, dabi’u ana daukar ba mahaifiya ne. Ka lissafa in ka auro wacce babu ilimi sosai da kuma mara ilimi kulawar su ga yaranka da kai kanka ma ba daya bane, ni a wuri na auren mace mai ilimi ‘yar boko shi ne gaba ‘more especially’ ta kasance mai yawan ibada da tsoron Allah. To, fa! duniyar gabadaya ta zamo abun alfahri ba mijinta kadai ba. Shawarata a nan dai wallahi in ta gari ce kam ayi, saboda akwai salon rayuwa da suka sani wanda bai yi zurfi ba ba zai taba saninsu ba. Auren mai ilimi ‘yar boko da Arabic in ya hade Allah duniya ce. Allah ya sa mu dace.
Sunana Malam Abubakar Dallatu Zareku Miga A Jihar Jigawa:
Abu na farko kusan kowa ya san shi, kana tare da ita ne sai wani ya zo ya ce shi abokin karantun ta ne. Matsala a nan ita ce; ya kamata ace, bai kamata wani ya zo wajenta ba, sannan kuma wani lokacin ma suna kebewa hakan gaskiya bai dace ba. Shawarar a nan ita ce; Ya kamata a gyara wannan halayayar, domin muslunci bai yarda da hakan ba, kuma sabawa muslunci ne dole ya yi kishin iyalinsa.
Sunana Hadiza Ibrahim D. Auta. Kaura-Namoda Jihar Zamfara:
Maza da yawa ba sa son auren mace ‘yar boko mai zurfin ilimi da wayewa. A son ran wasu mazan su aure mace daga kammala Sakandare. Idan ma karatun ne ta yi a gidansu, hankalinsu ya fi kwanciya sama da a ce da karatunta suka gan ta. Saboda tunanin da wasu maza suke yi; duk macen da ta yi dogon boko za ta fi karfinsu da aurensu duka. Bugu da kari, suna zargin kamar ta watsar da darajarta ta ‘ya mace a yayin gudanar da bokon. Sannan wayewarta za ta taba musu akidar da suke son bi idan masu ra’ayin juya matansu ne ta inda suka ga dama. Sai dai inda gizon yake sakar; ba kowace mace ce take kasa ganin girman mijinta ba wai don tana da boko ko don ta waye. Sannan ba kowace mace ce boko yake tafiya da mutuncinta ba, don haka a ganina laifi ne idan aka yi musu kallo daya. Don a cikin gida daya za a iya samun kowa da kalar halinsa.
Sunana Lawan Isma’il (Lisary) Rano LGA, Jihar Kano:
A inda matsalar take shi ne sanin kowane mata suna da rauni to, mafiya yawan matan da suka yi boko mai dan zurfi sukan sami wata kalar wayewa, musamman idan karatun addininsu ba mai zurfi bane sukan yi amfani da wannan bokon wajen kawo nakasu a zamansu na aure. Saboda gani suke yi wani abin ma wanda addini ya wajabta su yi wa mijinsu su ki yinsa, saboda wasu suna ganin sun ma fi mazan, musamman idan karatunsu ya zo daidai da namijin. Kuma idan karatun matan ya fi na mazan zurfi da dai sauransu. Ta Wani bangaren ya dace gaskiya, sabida mafiya yawan wasu auren baya karko, kin ga kuwa da ace an yi auren ba a dade ba an rabu gwara ma ba ayi ba. Shawarata a nan ita ce bai kamata ana gudun su ba, amma kafin maganar aure ta yi nisa su mazan suna bincika zurfin karatun matan na boko dana addini, sannan son samu ma idan namijin zai auri ‘yar boko sosai to, ya nemi wacce ta dan dauki lokaci tana son aure Allah bai nufa ba.
Sunana Nabeela Dikko Marubuciya daga Jihar Kebbi Garin Argungu:
A zamanin nan ana ganin wani lamari da ya ja hankalin al’umma: wasu mazan sun fara kauracewa auren mata ’yan boko masu ilimi da wayewa. Wannan batu yana da nauyin amsa, domin ‘duk inda kaho ya dosa, ba ya wuce kunne.’ Idan aka dubi lamarin da ido mai hangen nesa, za a ga cewa matsalar ba ta taso daga ilimi ba, sai dai daga fahimtar juna da tsoron da ke cikin zukatan maza. A zahiri, matsalar ta ta’allaka ne a kan fargaba da kuskuren tunani. Wasu mazan suna daukar cewa mace mai ilimi da wayewa ba za ta iya yin biyayya ba, ko kuma za ta yi musu fin karfi a gida. Wannan kuwa kuskure ne, domin ilimi shi ne fitilar rayuwa. Ilimi haske ne, duhu jahilci ne.
Sunana Muhammad Isah Zareku Miga A Jihar Jigawa:
Abu na farko shi ne ba kowa ne yake son auren mace wacce ta yi nisa a karatu ba, musamman karatun boko. Matsala a nan ita ce, mutane suna kin auren ‘yan boko ne saboda tsoron kin cikyakkiyar biyayya a zamantakewa ta aure. A gaskiya bai dace ba, suma ya kamata ana aurensu, saboda ba duk aka zama daya ba.
Sunana Khadija Auwal Koki A Jihar Kano:
Da farko dai a ganina gaskiya ra’ayi ne, domin kuwa ita mace mai ilimi cigaba ce a cikin al’umma, kuma cigaban ‘ya’yanka ce. Kuma idan ta yi ilimin kai ma za ka amfana, kuma duniya ma za ta amfana da ita. Abin da ya sa suke gudun auransu, saboda sun san me suke yi, su kuma wasu mazan sun fi san auran wacce ba ta san me take ba. E! to, gaskiya wasu daga cikin matan sukan yi wasu dabi’u na rashin da’a ko tarbiyya, wanda su kuma mazan sukan duba wannan su ga cewar ba za su iya auran su ba. Gaskiya hakan bai dace ba, domin kuwa suna amfani da wannan kalaman na cewa; wadanda suka cigaba da makaranta idonsu ya bude wajan kashewa samari masu niyyar auransu gwiwa, wajan ganin kamar za su auro wacce za ta raina su ko kuma wacce idon ta ya bude. A gani na duk wanda yake da niyyar auran macen da ta cigaba da karatu ya aura, sannan ka da ya duba magan-ganun mutane wajan ganin sun waye ko sama da haka. Sannan kuma a kara da addu’a da neman zabin Allah.
Sunana Sa’idu Abdullahi Damaturu Jihar Yobe:
Wasu mazan suna jin tsoron cewa mace mai ilimi ba za ta girmama su ba ko kuma za ta raina su. A’a, hakan bai dace ba. Ilimi bai kamata ya zama dalilin tsoro ko kiyayya ba. A karfafa maza su fahimci cewa mace mai ilimi na iya zama abokiyar rayuwa nagari. Aure nagari yana bukatar fahimta da mutunta juna ba tsoron ilimi ba.
Sunana Aisha T. Bello daga Jihar Kaduna:
Mafi yawancin maza suna ganin macen da ta yi boko ta waye kamar ba ta da nutsowa, suna ganin idonta ya bude ba za su iya auren ta ba, kuma wasu ba haka suke ba, gaskiya wasu ke bata wasu. A’a gaskiya saboda ‘yan boko mutane ne kamar mu, ina son na yi amfani da wannan damar gun janyo hankalin maza masu wannan ra’ayin na gun mata ‘yan boko in mace ta yi karatun boko za ta taimaki al’umma ne bakidaya, saboda maza masu kudun mata ‘yan boko su bari. Shawara ta a nan ita ce, maza masu gudun ‘yan boko shi ne idan ka auri ‘yar boko ko bata yi aiki ba, za ta taimake ka a gida ko gun yaranku. Ilimi shi ne gishirin zaman duniya, Allah ya bamu dacewa.
Sunana Muktari Sabo Jahun A Jihar Jigawa:
E! to, babu shakka wasu mazan suna gudun mata ‘yan boko masu ilimi da wayewa, ba don komai ba sai dan matsalolin da ake samu da wasu daga irin wadannan matan ta dalilin wayewar da suke ganin suna da ita, zamantakewar aure da su tana zuwa da matsala sosai. Kin auren nasu bai dace ba, domin duk wayewar ta in ka aure ta, za ka iya canza ta indai kai ma ka waye. Amma idan ta sami wanda bai waye ba, to fa ta sami rakumi da akala sai yadda ta yi da shi. To, masu irin wannan tunani ya kamata su duba, domin ba kowacce ‘yar boko ce take da matsala ba. Masu matsalar tun a soyayyar ku, za ka gane ko wacece ita indai kana nazartar ta.
Sunana Hassana Yahaya Iyayi (Maman Noor), Daga Jihar Kano:
Hmmm to wani lokacin ne su ‘yan boko sai a hankali amma fa ba duka ba. Gaskiya dai basu da wani matsala a nawa ganin dai. Sam bai dace ba wallahi ai shi ilimi abin so ne, wasu suke bata wasu cikin ‘yan boko, kuma ma dai ina ga masu wannan hali to, boko akida ne babu ilimin addini. To su dai nemi zabin Allah, dan wasu masu ilimin boko wallahi hmm adai yi shiru kawai. Babbar shawara a nemi zabin Allah shi ne.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp