Yau na karanta wani bayanin da aka wallafa shi a jaridar SCMP ta yankin Hong Kong na Sin, wanda ya yi tsokaci kan yadda karin ‘yan kasuwar kasashen Afirka ke amfani da kudin Sin RMB, maimakon dalar Amurka, wajen ciniki da abokan huldarsu dake kasar Sin.
Cikin bayanin, an yi misali da kasar Kenya, inda a cibiyar kasuwanci ta Eastleigh dake Nairobi, fadar mulkin kasar, ‘yan kasuwa suka kafa wata hanyar biyan kudi don sayen kayayyakin kasar Sin, inda ake biyan kudin kasar Kenya ga wani kamfanin jigilar kaya, daga baya kamfanin zai dauki nauyin biyan kudin Sin RMB ga masu sayar da kayayyaki dake kasar Sin. Ban da haka, an ce a cibiyoyin kasuwanci dake Lagos na Nijeriya ma, ana yin haka wajen gudanar da cinikin waje, wato canza Naira zuwa kudin Sin kai tsaye, sa’an nan a yi amfani da kudin Sin wajen sayen kayayyaki. To, hakan ya nuna wani yanayi na kara yin amfani da kudin Sin RMB wajen gudanar da ciniki a kasashen Afirka.
- Sojoji Sun Kama Ƙasurgumin Ɗan Bindiga, Sun Kashe Shugaban IPOB
- Bisa Rokon Bangaren Amurka Ne Manyan Jami’In Kasar Sin Zai Tattauna Da Takwaransa Na Gwamnatin Amurka Kan Batun Ciniki Da Tattalin Arziki
Sai dai me ya sa ‘yan kasuwan kasashen Afirka ke son amfani da kudin Sin maimakon dalar Amurka, wadda suka fi so a baya? A cikin bayanin jaridar SCMP, an ambachi wasu dalilan da Ovigwe Eguegu, mai nazarin al’amuran siyasa na kasar Najeriya, ya gabatar. Wato da farko, huldar ciniki mai karfi a tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin ta sa ake iya amfani da kudin Sin RMB wajen gudanar da cinikin kasa da kasa. Na biyu kuma shi ne domin halayyar dalar Amurka. A cewar Mista Eguegu, wannan batu ya shafi yadda ake mai da dalar Amurka a matsayin wani nau’in makami, da yunkurin kasar Amurka na lalata huldar ciniki dake tsakanin kasar Sin da sauran kasashe, wanda ke haifar da matsin lamba ga ‘yan kasuwar Afirka, da dai sauransu.
Hakika batun mai da kudin dala makami da Mista Eguegu ya ambata, na nufin yadda kasar Amurka ke amfani da dalar Amurka wajen kwatar dukiyoyin sauran kasashe. Misali, kasar Amurka ta samar da dimbin dala a kasuwa don kyautata yanayin kasuwarta ta hannayen jari, sai dai batun ya sa jama’ar kasashe daban daban fuskantar matsalar hauhawar farashin kayayyaki. Ban da haka, karuwa da raguwar ajiyar kudin ruwa a bankunan kasar Amurka a kai a kai su kan haddasa raguwar darajar kadarorin sauran kasashe, ta yadda kasar Amurka za ta samu damar sayen kadarorin da farashi mai rahusa. Ban da haka, a halin yanzu, kasar Amurka na kara rungumar ra’ayin daukar matakai bisa radin kai, lamarin da zai sanya ta kara amfani da kudin dala a matsayin makami, da haddasa karin matsaloli a sauran kasashe.
Haka zalika, matakan radin kai na kasar Amurka su ma sun girgiza matsayin dalar Amurka sosai. Misali, matakin karbar karin harajin fito kan kayayyakin sauran kasashe da kasar Amurka ta dauka, da nufin kawar da gibin ciniki, yana raunana matsayin dalar Amurka sosai. Saboda, dole ne a kiyaye gibin ciniki da farko, ta yadda sauran kasashe za su samu dalar Amurka a hannunsu, daga baya za a iya dinga amfani da kudin wajen gudanar da cinikin kasa da kasa. Yanzu matakin da kasar Amurka ta dauka shi ne domin neman magance daukar nauyin samar da gibin ciniki, amma hakan tamkar girgiza tushen matsayin kudin dala ne.
Tsohon ministan kudin kasar Amurka John Connally ya ce, dala kudi ne na Amurka, amma matsala ce ga sauran kasashen duniya. Yanzu haka tsarin kudin na haifar da karin radadi ga kasashe daban daban, sakamakon matakan kasar Amurka na kashin kai, lamarin da ya sanya dimbin kasashe neman kauracewa tsarin dalar Amurka. Misali, a rubu’in farkon bana, darajar cinikin da kasar Sin ta yi tare da kasashen Malaysia da Cambodia da kudin RMB, ta karu da kaso 27%, da 24%, bisa makamancin lokacin bara. Kana a nata bangare, kasar Najeriya za ta kulla yarjejeniyar musayar kudin Naira zuwa kudin Sin RMB kai tsaye, tare da kasar Sin, bisa wani labarin da jaridar Vanguard ta kasar Najeriya ta gabatar.
Kudi wani nau’in kayan aiki ne. Idan ana iya amfani da shi cikin sauki, kuma za a iya dogaro a kan sa ba tare da samun hasara ba, to, za a so a yi amfani da shi. Amma idan wani kudi ya kan haifar da matsaloli, to, tabbas za a guji yin amfani da shi. Wannan batu yana cikin tsarin gudanar tattalin arziki, ba wani abu ne da za a iya sauya shi ta karfin siyasa ba. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp