Daga ranar 26 zuwa 30 ga watan ne ake gudanar da taron baje kolin tsarin samar da kaya na duniya na kasar Sin ko CISCE karo na 2 a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
Alkaluma sun nuna cewa, kamfanoni, da hukumomi, da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 620 suna halartar taron, adadin da ya karu da kaso 20% kan na karon da ya gabata. Kana yawan mahalarta taron da suka fito daga kasashen ketare ya karu zuwa kaso 32% daga 26% na karon da ya gabata.
- Daga Ƙarshe Dai Za A Gudanar da Ƙidayar Ƙasa A 2025
- Dikko Radda Ya Bai Wa Gwarazan Hikayata Kyautar Kudi
Har ila yau, yawan kamfanonin da ke cikin manyan kamfanoni 500 da ke kan gaba a duniya, wadanda suke halartar taron ya karu da 42% kan na karon da ya gabata. A cikin dukkan ‘yan kasuwan da suke halartar taron, wadanda suka fito daga Amurka sun yi rinjaye, yayin da yawan kamfanonin Turai da Japan ya karu sosai. To, ko mene ne ya sa wadannan tarin bangarori suke halartar baje kolin?
Da yawa daga kamfanonin waje, suna darajta damammakin yin mu’amala, da hadin gwiwa da taron CISCE yake samarwa. A matsayin taron baje kolin na farko a duniya wanda ya shafi tsarin samar da kaya da gwamnatin wata kasa ta shirya, taron na CISCE ya kasance hajar da kowa zai yi amfani da ita a duniya.
Ban da haka kuma, kamfanonin waje sun amince da karfin kasar Sin na samar da kaya a duniya. A matsayin kasa mafi samar da kaya, da kuma yin cinikin hajoji a duniya, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa a tsarin samar da kaya na duniya. Har ila yau, kasar Sin tana samar wa masu sayayya na kasa da kasa kayayyaki masu inganci da araha, tare da samar da muhimmin tabbaci na tafiyar da harkokin tattalin arziki, yayin da kasar Sin take tafiyar da cikakken tsarin masana’antu, lamarin da ya taimakawa kamfanonin waje su kyautata tafiyar da harkokinsu, da kuma rage kudin kashewa.
Yadda kasar Sin take himmantuwa wajen raya tattalin arzikin duniya mai bude kofa, da kiyaye daidaiton tsarin masana’antu, da samar da kaya a duniya, ya karfafa gwiwar kamfanonin kasar wajen shiga kasuwannin kasar Sin. (Tasallah Yuan)