Cutar Asma, na daya daga cikin manya-manyan cututtukan da ake yawan kamuwa da su a Nijeriya.
Asma cuta ce da ke kama huhun Dan’adam, wanda ya ke amfani da shi yau da kullum don yin numfashi. Har ila yau, Allah ya halicce mu da wannan huhu guda biyu, daya a gefen hagu; dayan kuma a gefen dama.
- Kotun Ƙoli Ta Tabbatar Da Nasarar Zaɓen Gwamna Inuwa A Matsayin Gwamnan Gombe
- Minista Kyari, Gwamna Nasir Sun Kaddamar da Shirin Noma Na KADAGE A Kebbi
Haka zalika, a nan aikin huhunmu shi ne yin numfashi; idan muka yi numfashi, wato muna shakar iska ne ciki; idan kuma muka yi numfashi waje, muna fitar da numfashin da muka riga muka yi amfani da shi ne waje.
Saboda haka, cutar Asma; ciwo ne da ya ke kai hari zuwa hanyar da iska ta ke wucewa. Sannan ka da a manta cewa, akwai abubuwan da Allah ya sanya mana, domin kare mu daga kamuwa da wasu kwayoyin cututtuka.
Na farko shi ne, gashin da ke cikin hancinmu; idan muka yi numfashi ya kasance, iskar nan tana wucewa ta hancin namu; hancin yana dan dumama shi tare da kama kwayoyin cuta, ya makale su; domin ka da su shiga su jawo mana wata matsala.
Haka nan, ita ma majina tana bayar da nata gudunmawar wajen cafko abin da ya shafi kura da sauran makamantansu. Saboda haka, Asma cuta ce wadda ta ke kai wa wadannan abubuwa da suke kokarin tare ko kare shigar ire-iren wadannan cututtuka, daga hanyoyin wucewar iska, sai su tara ruwa su kuma kumbura; majina ta karu, wadancan makaran kuma sai aikinsu ya ragu. Don haka, hakan yana hana iska shigowa da kuma fita, shi ya sa masu ciwon Asma; babu abin da ya fi damun su kamar matsalar numfashi.
Har ila yau, masu dauke da wannan cuta suna yawan haduwa da cututtuka da ke kama huhunsu, misali kamar Nimoniya da sauransu. Kazalika, su kan yi fama da ciwon kirji, tari, sannan idan suna yin numfashi za su rika jin numfashin nasu yana yin kara kamar ana busa usur.